Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 52 of 90

Na samu wani ta kalmi na high hill me igiyoyi wanda ya ke kalar kayan green da kuma ja,na feshe jikina da turaren Anty Halisa,tuni na fara wani irin ƙamshi mai daɗin daɗaɗawa.

Tun kafin in iso ƙamshina ya iso wajen,ya buɗe idanuwansa manya ya tsuraminsu,tuni naji ina neman gurɗewa saboda takalmin dana saka.

Wow na ce azuciyata shima wanka ya buga da wata ɗanyar shadda ruwan skye blue ta yi masa matuƙar kyau,kamar ka ɗaukesa don gaskiya Yaya Bilal babu laifi ya haɗu.

Bansan ina kallonsa ba sai dana ji ya ce"Yi a hankali dai kada ki faÉ—i?ki wani zuro min ido,da wasu ficicin idanuwanki".hararsa na yo na murguÉ—a mai baki na wuce dining inda na shirya abinci na,na buÉ—e na zuba a plate na fara cin abinci na cikin nutsuwa.

Sosai ya ƙuramin ido har na tsargu na ɗago na kallesa sai kuwa ya ce"ni baza a bani abincin ba"?.

A hankali na fara zuba masa ko kafin in ƙarasa zuba masa ɗin ma har ya iso inda na ke.sosai numfashinmu ya haɗu waje ɗaya,ya tsugunna agaba ya ɗakko plate ɗin abincin ya ɗebo loma ya miƙomin,na kauda kaina gefe ina wani ɓata rai.ya ƙara ɗebowa na kauce.

Ajje abincin ya yi,banyo tsammani ba kawai naji anyi sama dani,sai babba ɗako wato Ɗakin Yaya Bilal,sai wani shure shure na ke amman shi ko ajikinsa shi rashin kunyar khairat ma sha'awa take basa,ai kuwa na ƙulla araina sai rafka masa rashin mutunci.

Ba'azo inda na keso azo ɗin ba,aƙwai dai lokaci,amman yanzu zan nuna masa duk abinda ya baka tsoro wataran shi zai baka dariya.

*Kamar yadda kuka sani na yi muku alƙawarin koya muku abubuwa a wannan book ɗin*

To yanzu zan fara da maganin ƙuraje ko wani iri.

*Sirrinki🌈👂🏻*
1
*Yadda ake maganin ƙurajen fuska.*

Daga ummu maher

Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haɗa arinƙa gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15.

2
ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ƙwanta bacci idan ya tashi ya wanke.

by ummu maher

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:23] Miss Green🍀: *55.. . .56*

. . .har na wuce sai naji muryarsa"ke zo nan"!.ya faƊi hakan cikin haƊe girar sama da ta Ƙasa,wai don kada nace na gansa,haƊe rai na yi sosai kamar ban taƁa dariya ba,na juya shining eyes Ɗina sosai irin yadda Ƴan duniya ke yi,na kallesa irin yadda ya kalleni kallon Ƙasa sannan na yi wuce wata sashe na ba tare da ko waiwayensa na sake yi ba.

sosai abin ya bashi haushi ya wuce fuu kamar kububuwa,ina hangosa ta saman bene,na tun tsire da dariya ina tunanin hali irin na yaya Bilal na wuce ina ce wa hmm zaka shigo hannu sai na gara ka kamar ball,na ÆŠauki wayata muka fara chart da anty halisa,dariya sosai ta yi ta ce"kai haba ashe ma mijin na ki bai da wuyar sha'ani?ai so nake sai ya garu sosai sannan mu gana masa azabar da sai yayi kuka saboda haukan sonki".

"hmm anty ni gani nake kamar ba zai soni ba?Saboda yaya Bilal ya tsaneni sosai".na faƊi hakan cikin damuwa,sai kuwa anty halisa ta yi tsaki ta ce"Hmm gaskiya khairat raguwar zuciyarki ta yi yawa,yo idan banda raguwar zuciya ta yaya zakice bazai soki ba?ke fa macece ba namiji ba?kuma kina da qualities Ɗin daya kamata namiji ya soki,to saboda me kuma zaki ce haka?idan har kina son muyi shiri to dole ne sai kin zama mace jaruma ba raguwa ba,don haka ki tashi ki zama gawurtacciyar mace agidanta,ki karƁo mutuncinki da kuma martabarki waƊanda ki kayi watsi dasu,don haka inw me jan kunnenki akan ki kula sosai,kada ki bada kai da wuri ki wana sa yadda ya kamata".

cikin dakiyar zuciya na ce"insha'Allah anty zan zama jajirtacciya kamar yadda ki keso kuma bazan taƁa baki kunya ba".sosai anty halisa ta yi farin ciki muka cigaba da hirarmu.
*****

sosai abinda khairat ta yi masa ya tsaya masa,khairat Ɗin daya sani Ƴar Ƙauye?me nuna masa tsantsar so?yau kuma kallon wani hadarin kaji yaga tana yi mai,kamar an zabure sa haka ya tashi wato allurar soja ta miƘe,indai kuwa baiyi maganin khairat ba yau bai cika soja ba.

ina gama chart Ɗin na kashe wayata baki Ɗaya na tashi na cire after dress Ɗin jikina wacce itama tabi lafiyayyiyar baƘar fatata,na fito farlo na wuce kitchen na Ɗakko indomie Ɗin dana dafa,kawai sai ganin mutum na yi a gabana,wani mugun buguwar zuciya naji,amman kuma sai na daure gudun kada in bada kai na,sai na yi mai kallon Ƙasa yadda na yi masa Ɗazu.

"khairat ni ki kewa wannan kallon ko?".

Na tsinkayo muryarsa Ƙara yimai kallon na yi ya matso inda na ke sosai yana neman taƁa ni,da sauri naja baya kamar naga abin Ƙenkyami na waro ido waje na ce"dont touch me,Kada ka yadda ka taƁani wallahi,ni ba,muharamar ka bace".na faƊi hakan ina turo bakin shawaƁa ta,wanda ya ke yimin mugun kyau Ɗan baki na kamar cunkun fure.
"Khairat ni ki ke cewa ba muharraminki ba?ni ba mijinki bane?".da sauri na zaro ido na ce"Allah ya tsare ni wallahi ni bani da wani aure zaman kai na nake,kuma idan ka Ƙara shigomin sashe wallahi ihun Ɓarawo zan maka.

waro manyan idanuwansa ya yi yana ganin kamar ba khairat ba,khairat me shiru shiru yarinyar da babu ruwanta?to ko dai ba ita bace wani aljanin ne ya shiga jikinta?ga wani mugun turare wanda duk ya tada masa da feeling Ɗinsa,musamman ma akan khairat Ɗin,daman haka take da kayan ado da alatu?sam bai taƁa tunanin hakan daga gare ta ba,don ko agida ma bata fiya fitowa ba tare da hijab ba.

Ganin yaƘi fita ne yasa na ce"mlm don Allah mlm fitarmin a sashe ni na gaji da wannan tsayuwar da ka yi min aka kamar wani sunduƘi".

sosai abin ya bawa Bilal mamaki,sam bai jurar rashin kunya don haka yanxu zai yi maganinta.ban yi tsammani ba kawai sai naji ya janyo ni ya matse min baki na sosai naji zafi na gallara mai cizo,amman ko gezau bai yi ba,na Ƙara gallara mai wani cizon.abinda ban sani ba shine hankalinsa sam baya kan cizon dana yi masa,rigar dana saka irin mai wajen wuya Ɗin nance da sauri na tashi na ture sa gefe,cikin fushi na ce"haba bawan Allah me ye kuma zaka zo kana kallo na".na faƊi hakan cikin shagwaƁa,anan take ya tuno da abinda ya aika ta,da sauri ya fita waje yana gyara zaman bottle Ɗin rigarsa wanda duk a buƊe ya ke.
Yana fita baki ÆŠaya na zauna akan babbar kujera wato tree seater,na lumshe idanuwa na fuskar yaya Bilal na yimin gizo sosai,wani irin farin ciki naji azuciyata na danne saitin zuciyata ina jin bugawarta sosai,har hawayen farin ciki sai da na yi saboda tsananin murna da wankewar zuciya,wai yau ne nice ga ni ga yaya Bilal?mutumin da ko inuwa ta bai son gani.kullum sai hantara da kuma zagi?amman yau har shine ya ke kallona kallon cikin ido.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.