Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 57 of 90

******

"Jidda gaskiya kada ki yiwa wannan yarinyar wannan abin,saboda ita bata taƁa binki da sharri ba,tana zaune da ke lafiya,infact ma awannan lokacin da muke ciki ba kowace kishiya bace za taga kina yawo ta yi shiru da bakinta ba,jidda wallahi yarinyar ba tada matsala kada ki cuce ta."

"Dalla Rabi'a ki rufemin baki,wa'azi na ce ki yimin?ko Kuma shawara na ce kiban?na dai tambaye kine ko a unguwarku za'a samu wani talakan ya yi mana wannan aikin?tunda unguwarku duk talakawa ne,amman shine zaki nemi yimin wa'axi?ina son kafin in buƊe ido na ki fita daga gidan nan,idan muka wallahi naji labarin kin gayawa wani wannan maganar,zan Ɓatar da ke ne aduniyar nan,don kinsan ina da kuƊin da zan iya yi miki hakan."

"Babu komai jidda ni dai nasan kema kafin ki zama komai kema talakance,harma na fiki rufin asiri,kinga kuwa ashe duka muna ÆŠaya ne,kuma zan bar miki gidanki,amman ki sani shi sharri ÆŠan aike ne".

wani banzan kallo tabi Rabi'a dashi sannan ta ce"as as bana nemanki anan,ki fita tun kafin in saka ayimin waje da ke,banza faƘiriya kawai,talakan banza talakan wofi,insha Allah a haka zaki Ƙare a talauce tunda aure ya gagara,an gama iskanci da Ƴan iskan unguwa.

Kuka sosai Rabi'ah ta yi na wulaƘancin da aminiyar ta jidda ta yi mata,ko a mafarki bata taƁa tunanin jidda za ta iya koda makamancin haka ba,ta goge hawayenta ta fita daga gidan,tana tuna ranar da jidda za ta yi nadama,don tabbas tasan aƘwai ranar nadama.

***

Ina kallon tv naga wai wani ya Ƙwaci yara daga hannun mugu Alhaji damas,suka rubuta sunansa Admiral b.wanda akafu sani da Bilal,sosai na waro ido ina kallon hubbyna tsamo tsamo acikin Ƴan jarida yaran su kusan Ɗari,duk ƳaƳan talakawa ne,sosai naji daƊin ganin mijina ya,kasance me taimako na hura masa kiss ta tv Ɗin,sannan na ce"Allah ubangiji ya karemin kai yaya na".

Na koma Ɗaki na na fara trying Ɗin number Ɗinsa,amman akashe na Ƙwanta tunaninsa ya cika zuciyata fal,daga wannan baccin na xarce,barcin daya zomin da Ƙalubale na rayuwa Ƙaddara ta,barcin daya kasance dana sani acikin rayuwata,wanda na yi kuka kamar zan mutu,barcin daya rabani da yaya Bilal,tsanar da ya yimin ta Ƙara ninkuwa sosai.

tun ina bacci naji kamar ana ÆŠauka ta a hoto,amman sai na ÆŠauka ko mafarki na keyi,na cigaba da bacci na sai dai baccin babu daÆŠi don dai babu yadda zanyi ne,a yanzu na zama kamar kasa wajen bacci,sai in yini ina bacci idan babu skull.

yaya Bilal ya kalli captain ya ce"kai nifa ka cikani da surutu banni in koma gida,saboda in koma wajen farin cikina khairat in ganta ko naji daƊi,wataƘil ma tasan na dawo,don waƊan nan Ƴan jaridan ba barin mutum za suyi ba,sai sun watsa duniya."Murmushi captain ya yi sannan ya ce"To nima dai ba tsayawa zanyi ba,don kasa ina da mata nima kuma ina sonta kamar yadda ka keson matanka,kai har dama nuna banbanci tunda ka sauka ka ke ta faman kiran khairat a bakinka,ita jidda ko oho ko?a dai ji tsoron Allah".ya faƊi hakan cikin xolaya don shi mutum ne mai raha sosai.

Bilal bai tanka masa ba ya wuce motarsa yana dariya,sai dai tun akan hanya yaji gabansa na faÆŠuwa sosai,ya dai fara addu'ah acikin zuciyarsa,yana parcking y hango jidda ta fito daga sashensa,ta rungumesa har da kukanta ya ce"banji ÆŠuriyar khairat ba lafiya dai ko?".

"hmm to ni me zance Love tunda fa ka yi tafiya yarinyar nan take yawo, da kawo mutunen da ban yadda dasu ba."

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

Instagram links👇

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

MISS
GREEN CE
[23/09, 16:29] Miss Green🍀: 71. . . . . .72

. . . .cikin fushi Bilal ya juyo ya kalli jidda ya ce"ki rufemin baki ke yanzu ko kunya bakya ji?ki ke jifan khairat da wannan mummunar maganar,to me ki ke nufi da hakan?yawon banza take kenan?ko kuwa me ki ke so ki faÆŠamin".?

rau-rau jidda ta yi da ido alamar kuman munafurci sannan ta ce"to ai shikkenan na yi shiru tunda ita Ƴar uwarka ce babu dama a faƊi laifinta sai kace an faƊa,insha Allah ni bazan Ƙara magana akan shiga harkar ta,nidai nasan aƘwai ranar Ƙin dillanci,kuma ma ai bani kaƊai na ke ganinta ba,har da masu gadin gidan nan,ai sai ka tambayesu ko?".bai sake kulata ba ya shiga Ɓangarensa ya ajje kayansa sannan cikin zumuƊi ya yi Ɓangaren khairat.

wata muguwar dariya jidda ta saka don tuno da abinda xai faru matuƘar Bilal ya gani da kansa,ta sauke labulan Ɗakinta,ta fito daga sashen nata zuwa waje ta yi Ɓangaren sojojin masu gadin,tana zuwa ta kallesu Ɗaya bayan Ɗaya sannan ta ce"ku taimaki kanku a wannan harkar,matuƘar kuka yimin abinda na keso to tabbas zan ruƁanya muku kuƊin dana yi muku alƘawari,wanda kuma na baku na shan ruwa ne wannan,don haka ku taimaki kanku,tonamin asiri kuwa shima yana Ɗaya daga cikin abinda zai sa na ruguza rayuwar mutum kamar yadda na ruguxa rayuwar wannan shaiƊaniyar kishiyar tawa,don haka ku ki yaye".

Da sauri suka ce "ok ma insha Allah baza mu baki kunya ba,zamuyi yadda ki ka ce harda Ƙari ma akan naki".murmushi ta yi da sauri ta wuce Ɓsngarenta ta haye saman bene,ta kulle Ɗakin na ta,ta Ɗakko wayarta ta kira Alhaji damas,suka cigaba da shaiƊancinsu awaya,abin dai sam babu daƊin faƊa.

"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un".ya faƊi hakan yana dafe hannunsa jikin bangon Ɗakin,tuni yaji wata muguwar zufa na tsatstsafo masa a dukkanin gaɓɓan jikinsa,ya kasa Ƙarasawa yana jin yadda kansa ke mugun sara masa,da gudu Ƙaton mutumin me kama da aljanu ya tashi daga kusa da khairat,da gudu ya fece daga shi sai gajeren wando rigarsa a hannu.Sam Bilal ba shida Ƙarfin da zai tsayar dashi saboda yadda yaji jikinsa baki Ɗaya kamar an cire masa lakar jikin nasa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.