Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 46 of 90

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:22] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*

📃LITTAFI NA 2

UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

*Matso kiji👂🏻*
Ki dinga tsarki da kanimfari musamman ma idan bayan kin gama al'ada yana cuko da gaban mace sosai sannan ya matseki ciki da kuma wajenki.

49. . . .50

. .. ."Yaya Salim kaine?".Na faÉ—i hakan ina matsa masa,na gaishesa ya ce"ai ba ni kaÉ—ai bane ma dasu mama ne harda Hajiya kaka".buÉ—e idanuwa na yi murna ta isheni Æ´ar damuwata naji ta kau.

Na rungume Hajiya kaka ina ce wa"i miss u so much my Hajiya kaka".itama rungumeni ta yi tana tsokana ta,wai tunda na yi aure ko kiranta awaya banyi ba.

Sosai mukasha hira ananne ma ake hirar zancen rashin lafiyar Rashida,na ce"Hajiya kaka inason zuwa in duba ta".
"A'ah ƴar nan ba'a haka daga aure sai kuma ki fara fita?yanzu ma daga gidan mero muke,itama ta saka min kuka wai sai ta biyoni munzo nan,to shine fa naja mata kunne akan baza ta bini ba,sokon mijinta gashinan gabanki Salim ko kallon ƙurar zancenmu baiyi ba,daga baya ma ya fito waje shine na biyosa na ce sai ya kawoni gidanki,amman gidan Rashida muka fara zuwa tunda yafi kusa da gida."

dariya na yi na ce"Allah sarki Mero ai ita ga ta ga gida ma babu nisa tunda bayan gidanmu ne,Amman hajiya kaka ya ki ka jikin Rashidan?".

"Ah wallahi jikinta da sauƙi sosai,ai da ya ke ma an sallamota da wuri,ita kuma haka Allah ya tsara mata to ubangiji Allah ya bada na aike".dukkanmu da amin muka amsa aka cigaba da hira,Hajiya kakanta leƙa taga garar da aka kawomin ta ce"ah gara wallahi ta yi,wannan dai idan ba rabawa biyu zaki yi ki bawa waccen figigiyar ba ai har sai ayi shekara ma".ta faɗi haka tana dariya.

Har ƙofar sashena na rakosu mama ta ce"to khairat muyi banƙwana gobe insha Allah zan wuce gida,Allah ya bada zaman lafiya".na amsa da amin hawaye na fitowa daga cikin idaniya ta.

"Au yay naji ɗan jakar uba,au yanzu don Allah Bilalu kana cikin gidannan?Amman har muka gama zaman daɓaro baka shigo ba?saboda kana wajen wannan ƙwailar matar taka?a to ahir ɗinka idan aka shiga haƙƙin jikata,don ina jiye maka tashi da ƙonannan jiki".

Ta faɗi hakan tana harar jidda wacce ko kunyar idon hajiya kaka bai hanata ɗafewa jikin Yaya Bilal ba,shine ma yaji kunya ya ture ta gefe ɗaya ya durƙusa har ƙasa yana gaidasu mama,Hajiya kaka ta ce"ah to ni dai na faɗa maka,ka biyewa mace ka faɗa wuta tsundum wallahi,kuma duk ihunka Ruƙayya da Abdu baza su fito da kai ba".Ta daɗi hakan tana yin gaba abinta.
Bayansu Hajiya kaka sun tafi da daddare na yi wanka na mai kyau da sabulun da mama ta haÉ—omin na gyaran fata,na É—akko qur'ani ina karantawa sai naji zuciyata kamar an wanke min ita fes.

Na É—akko wayata na buga wayar Rashida naci sa'a ta É—aga,da sauri ta ce"ah lallai amaryar yayana kin manta dani ko?da tuni yanzu ina barzahu,amman ko kizo ki dubani ko?".

Duk alokaci ɗaya ta sakomin waɗannan tambayoyin na ce"ayya Rashida kinfi ƙarfin haka awaje na,nima shekaran jiya da maryam tazo shine take faɗamin abinda ya faru har kuka sai da na yi wallahi".

Nan dai muka cigaba da hirarmu ta aminai,ta ce"kin buga number maryam kuwa".?
Na bata amsa"eh na buga ita ma akashe shiyasa duk naji kamar na rabu da wani abu mai muhimmanci arayuwata,me ya faru da wayar na ta"?.

"Hmm kinsan fa washe garin ranar da aka kaita sukayi faɗa da Khadija shine ta fasa mata wayar,bata tsaya anan ba ta shiga ɓangarenta duk ta rugurguza kayan wuta masu amfani da kayan kitchen ɗinta,Hmm kedai bari khairat jiya dai Khadija agida ta wuni,don yaya Aliyu ce wa yayi ta koma ta gyara tarbiyyarta sannan ta dawo,ina faɗa miki da ya ke yaya Aliyu ɗan duniya ne,kayan daya canjawa khadija na kayan wuta da kuma kayan kitchen su ya ɗiba ya bawa maryam".tana kaiwa nan ta rintsire da dariya.

Nima dariyar na ke na ce"hmm Rashida kema fa ki danki da makamanciyar irin wannan matsalar,ki daina dariya".

"Hmm a fahimtarki hakanne,amman a fahim tana ba haka bane,da zaki yi ƙwana ɗaya agidana da sai kinci dariya har cikinki ya ƙulle,abinda baki sani ba shine Yaya Aliyu dai da ki ka sani mijina,agaban Nadiya yana nuna kamar yana sonta ne ko kuma tsoronta,amman wallahi ko ɗaya babu haka,ahi dai yana yi ne saboda fita hakkinta,kuma wallahi son da Nadiya ke yimai ya fi nasa yawa nesa ba kusa ba,don haka ki daina zaton ko aƙwai wani abu,in ma asiri zasuyi to ni na fisu har awajen Allah,don ni zuciyata awanke take fes,babu wani abu acikinta kinga kuwa ƙarshe kansu zai koma".

GyaÉ—a kai na yi kawai don ni a fahimtar tawa ko wani abin suka yiwa Rashida,don tsaf nasan Mama iklima cikinta da wajenta,basu da tsoron Allah ko É—aya,su dai kansu kawai suka sani da kuma Æ´aÆ´ansu.
****

Wayar dana ajje ce ta fara ruri,na ɗauka na saka a kunne ba tare dana duba ba,saboda wanke salad ɗin dana ke a kitchen,muryar Zuhra ce ta karaɗe min kunnuwa,ƙawata ce a Bayero university muka haɗu,wajen zamanmu ɗaya da kuma wata Zainab,ganin suma duk masu hankaline yasa na yi ƙawance dasu.

"Ah lallai ya yi amarya agidanta,kina more amarci wallahi,kai muma dai Allah ya nuna mana ranar aurenmu,amman kash nasan Dadyna bazai taɓa aurar dani yanzu ba,kin san burinsa akaina wai har sai na cika lauya sannan zai aurar dani,wallahi abin nan yana damuna,gashi kuma ni ina son auren".

Ɗan murmushi kawai na yi,tausayin Zuhra duk ya cika ni,Allah sarki ita tana ganin kamar duk wata mace idan ta yi aure shikkenan ba tada wata damuwa?ko kuma kawai morewarta take?ita dai gata nan kamar wata sunduƙi agida,yau sati ɗaya cif amman babu ita babu miji,naji wani abu kamar mashi ya daki ƙirjina,saboda jin tashin motar Yaya Bilal,na ɗan zuge labulen kitchen ɗin ina hangosa,shi da ƴar ganan goshin sane wato Jidda.

"Kina jina kuwa amarsu"?.

Da sauri na dawo cikin hayyaci na sannan na ce"zuhra abinda ba keso dake,ki ƙara haƙuri komai lokaci ne,haka zali ka shima aure lokaci ne dashi,don haka ki cigaba da addu'ar Allah dai ya baki miji nagari,ba auren ba samun miji nagari ayanzu shine ya yi ƙaranci acikin al'umma."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.