Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 85 of 90

Jikin Bilal ya yi sauƙi yanzu,sai dai kowa ya kallesa yasan yana cikin wani hali,ga yaransa wanda yanzu sun koyi wata ƙiwa indai ba shiba basu fiya yadda da kowa ba.hatta abin yanzu yana san ya shafi aikinsa.don daga wajen aikin ma sun aiko masa da saƙo akan yana wasa da aikinsa,uzuri ya bayar akan ce wa bai da lafiya.ai kuwa ba tare da ya watstsake ba ya koma bakin aikinsa.

Sai dai fa ƙwana biyu da komawar tasa jikinsa ya ƙara dawowa,yana daurewa don bai san kowa yasan halin da ya ke ciki,ga ciwo na nuƙurƙusarsa amman yana daurewa.

*********

ayanzu mun gama makaranta wacce muka yi shekara fin biyar muna yi,don kowa yasan aikin Lauya yadda ya ke aƙwai cinye shekaru.ya yi dai dai da kasancewa ta shekara ishirin da huɗu a duniya.abin kuɗi sai gashi shahid ya fara cuku cukun nemomin aiki,Allah ya taimake ni aka ɗaukeni a babbar kotu amman bazan fara aiki ba har sai na haihu.

Tun safe ciwo ke nuƙur ƙusa ta amman naƙi in bar kowa ya gane halin da na ke ciki,har dai Ammi ta gano ai kuwa sai ga ciwo daga kaɗan ya zama babba,muka garzaya asibiti,A ruɗe Shahid ya taho asibitin hankalinsa tashe.

Dai dai wannan lokacinne kuma aka kawo Bilal shima ranga-ranga babu lafiya,kowa hankalinsa atashe sai kuka ake.

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:31] Miss Green🍀: 1001. . . .1002

tashin hankali sai ya zama guda biyu don nima wannan haihuwar har tafi tasu Ƴan huƊu,don har an fara fitar da rai dani,shi kuwa shahid nema ya ke ya fita daga cikin hayyacinsa,ba don ma ammi ba da ba'asan abinda zai faru ba,har an fara haƊa kayan aiki na sunkutu Ƴa ta mace kyakkyawa me tsananin kama da mahaifinta,kyakkyawa ce sosai har tafi mahaifinta ma kyau.

hajiya kaka ma tazo ta yimin barka sai dai fuskarta atamke tsaf,haka ma duk wanda zai zo duba ni sai inga fuskarsa a haÆŠe sosai na rasa gane kan kowa,kai hatta yaya Aliyu dasu mamana kowa sai inga fuskarsa tamau,abin ya dameni sosai,na rasa wanda zan tambaya gashi nima ban gama warwarewa ba don nasha wuya sosai.

Shahid ne ya shigo shima duk jikinsa ya yi sanyi,yana shigowa ya kalleni sannan ya ce"khairat ya jikin"?.sosai maganarsa ta girgizani don bai taƁa kirana da khairat ba sai dai hayatee,na kallesa sosai Na ce"hubby yau kuma sunana ka ke faƊa"?.na faƊi hakan ina me kallonsa kamar ya yimin laifi.

sunkuyar da kansa ya yi ya Ƙaraso inda jaririyar take ya saka hannu ya Ɗauketa ya rungume ta a Ƙirjinsa hawaye masu zafi suka zubo masa a kuncinsa,a zuciyarsa ya ce Allah sarko Ƴata ashe bazan rayu da mahaifiyarki ba?ashe bazanyi rayuwa da ita me tsayi ba?yanzu me na aikata haka?shin nima ina tunanin zan iya wani auren idan na rabu da khairat?shin ya rayuwar Ƴarsa yaya za ta kasance alhali babu me kula da ita sai mahaifiyarsa zai Ɗorawa wahala.

jin kukan da khairat ta fashe dashi ne ya saka ya juyo da sauri ya ce"khairat lafiya ki ke kuka me aka yi miki?".ya faƊi hakan yana matsowa har ya riƘe hannuna wanda na Ɗora aka ina gunxuma ihu kamar wani ya dake ni.

da sauri na yar da hannunsa gefe na ce"haba na gaji wallahi,yaya kuke so inyi ne?kO cikakkiyar awa ÆŠaya banyi da haihuwa ba,amman kowa ya shigo sai inga duk hankalinsa atashe kuma ya ÆŠauremin fuska?Haba wannan wani irin rashin tausayi ne?ku faÆŠamin mana idan wani abune ya faru?"

da sauri ya koma gefe ya ce"khairat babu komai fa haka dai ke ki ka gani,amman babu komai bari inje wajen Ammi sai mu taho tare taje duba wanine ba shida lafiya".yana faƊar hakan ya fita da mugun saurinsa,tuni naji zuciyata ta tsinke na shiga wani irin kuka wanda na kasa gane kansa,na kalli Ƴata wacce kebta shan hannu alamar tana neman abincinta,da ta gaji da shan hannun sai ta fara kuka sosai,nima uwarta ta kuka nake sosai kamar wacce aka aiko mata iyayenta sun mutu duka.

ana cikin wannan halin ne anty hakisa tazo,da sauri ta Ƙaraso cikin Ɗakin tana ce wa"subhanalillahi khairat me ya faru haka?ga yarinya na ta kuka alamar tana neman mama kuka kinƘi bata?".ta saka hannunta cikin gadon babyn ta Ɗakko ta tana Ɗan girgiza ta,ta zauna ta ajjemin ita akan cinya ta tace"khairat yi haƙuri ku bata tasha kinji?koma menene ya faru bai kamata ki yiwa Ƴarki ta cikinki haka ba,ki bata tasha sannan sai muyi magana".

Sai shashsheƘar kuka ba ke harda majina ta kalleni kawai,tana jin tausayina har cikin ranta,a hankali na ke shayar da ita jaririyar ta riƘe babban Ɗan yatsana tana kuma kallon cikin idona sosai,ina kallon yarinyar sai naji zuciyata ta fara sanyi tabbas ƳaƳa rahama ne arayuwa,Allah ubangiji ya bawa duk wanda basu haihu ba,ya basu masu albarka wanda za'ayi alfahari dasu aduniya da lahira.

sai da tasha ta Ƙoshi sosai sannan anty halisa ta amsheta ta sakata a kafaƊarta har ta yi gyatsa,sannan ta kalleni sosai ta fara yimin nasiha sannan ta ce"khairat yanzu fa daga dubo baban Ƴan huƊu na ke".da sauri na kalleta sannan na ce"me ya same shi kuma?daman ba shida lafiya ne?".

Na faƊi hakan zuciyata na bugawa sosai,ganin na shiga wani hali ne yasa ta gane ce wa ban san ba shida lafiya ba ta ce"khairat come down,kinga yanzu kin haihu fa kina buƘatar ki samu kulawa sosai don haka kada ki Ɗaga hankalinki don Allah ciwon fa yanzu da sauƘi".

da sauri na miƘe na ce"haba anty halisa ni fa ba yarinya bace kamar da,kowa fa ya shigo fuskarsa babu daƊi,ni nasan aƘwai abinda ake Ɓoyemin."Na faƊi hakan cikin kuka na tashi tsaye ina jin wani irin jiri yana Ɗiba ta,ga uwar yunwa da na keji wacce ta gama cika min ciki na ce"anty halisa don Allah zo muje ki nunamin Ɗakin da aka Ƙwantar dashi"?.

da sauri ta ce"a'ah fa khairat bazan iya rakaki ba gaskiya,kinga ba kida lafiya kuma bayan haka mijinki ma fa yana cen yanzu na baro sa acen,kinga ai babu daƊi ki dai bari ki samu lafiya sai kije".da sauri na Ƙarasa kusa da ita ina kuka na ce"don Allah anty halisa ki rakani in duba sa,zuciyata ji na ke tamkar zata fito don Allah".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.