Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 49 of 90

"Yaya Aliyu ka yiwa Yaya Bilal ɗin magana,wallahi ni nayi masa magana amman bai ce komai ba,idan ka yi masa magaba kai zai yadda".na faɗi hakan cikin shaƙewar murya,ya fuskanci tsoron Yaya Bilal ɗin na ke don haka ya ce"ok ba komai insha Allah zan yi masa magana,kada ki damu".yana faɗar hakan ya kashe wayar ya kira yaya Bilal awaya ya faɗa masa.taɓe baki ya yi ya ce"go a head kawai ni ban hana ta zuwa skull ɗinta ba,amman ka shaida mata kada ta kuskura idan taje ta kai dare ko kuma yamma,idan kuma ta taka doka ta to tabbas zan soke makarantar".ya faɗi hakan cikin gadara.

Yaya Aliyu yasan halin Bilal sosai É—an zafin kai ne,bai da tsoron faÉ—ar magana idan ta fito masa,suna gamawa shima yaya Aliyu ya kirani ya faÉ—amin yadda sukayi tsaf,a zuciyata na ce kaji É—an rainin hankali wato ma kada inje indaÉ—e kamar ma ya damu dani.

Tun dare na kira su zuhra da kuma zainab na shaida musu gobe monday,ina skull insha Allah,sosai suka yi murna suka ce a to ai gwara ki dawo ana ta karatu babu ke,harma anyi wasu c/A ɗin baki nan wata ma mune mukeyi miki ita,naji daɗi sosai don sun cika ƙawaye na ƙwarai.

Washe gari da wuri na shirya na fice makaranta,sanye na ke cikin wata doguwar rigar material mai kyau,ta rufe min ruf jikina na samu nayafina babba na yafa da takalmina mai ɗan tsayi,kasan cewa ba doguwa cen ba.banyi wata ƙwalliya cen ba daman ni ba ma'abociyar yin hakan ba na dai gyara ƙwantacciyar gira ta wacce take acike ɓam da ita gata kuma baƙa ƙirin,na kalli madubi,ni dirarriyar macece sosai,baƙina bai hana aga kyau na ba.na ɗakko jakar skull ɗina na saka na fito na ɗan kurɓi ruwan tea kaɗan,na zuba dankalin dana soya acikin ɗan launch box ɗina mai kyau,na kulle sashe na fito,naji duk babu daɗi saboda na saba saka turare yau kuma har zan shafa sai kuma na ajje tunowa ta a matsayin matar aure.

Ganin rashin dacewar tafiyata ba tare dana sanar dashi ba .har na yi hanyar ɓangaren jidda sai kuma na tuno da irin wulaƙancin da ta yimin rannan,kawai sai na yi hanyar waje duk raina babu daɗi.

Nafi kusan minti talatin a bakin titi ban samu abin hawa,na fara tafiya a ƙafa zuwa cen babban titi kafin in samu abin hawa,saboda unguwar mu G.R.A ce babu adaidaita sahu.

Sosai naji ana ta yimin hon amman ban wani juyo ba,saboda nasan idan na juyo wata ƙila irin ƴan iskan nanne,cen dai dana gaji na juyo ina juyowa sau naga Captain,ya washe min baki ya ce"a'ah kaga mata agidan Admiral B.ya akayi kuma kike tafiya aƙafa?".

Fara gaishesa na yi yace"ikon Allah yanzu duk motocin A/D sai arasa wacce zata kai ki unguwa?".sunkuyar da kaina na yi ina wasa da ƴan yatsuna.fuskantar kamar aƙwai matsala ne yasa ya ce"ok shigo in rage miki hanya".

Na shiga amman baya na zauna,wannan É—in ma don nasan aminin yaya Bilal ne shiyasa na shiga,ya waiwayo da kansa ya ce"khairat ina zakije ne?".

"Makaranta zanje Bayero university".murmushi ya yi sannan ya ce"ayya ashe kin koma skull Allah ya bada sa'ah,anjima Halisa zata zo to na kira Bilal sai ya ce wai ita jidda zata je gidansu,to shine na ce ai gaki agidan tazo wajenki.ashe ma kema makaranta zaki".

"ayya ba komai idan naje bazan daɗe ba,daman yanzu test muke yi idan naje zan dawo da wuri,ka faɗa mata tazo".murmushi ya yi azuciyarsa yana ce wa oh wannan yarinyar baiwar Allah,gashi yaga alamar wannan ita ce ya kamata ta zamowa Bilal garkuwa agidansa.don ya fara zargin jidda,don duk abinda sukayi da Bilal tamkar a gabanta ne,don matuƙar yaje inda ya ke laɓewa don ɗaukar wasu abubuwa a gidan Damas sai yaga khairat,abin ya tsaya masa sosai kuma ya rasa yadda zaiyi ya faɗawa Bilal hakan,tabbas jidda ta cika butula me mantawa da alkhairi.
*****

Na yi sa'a ina zuwa makaranta na haÉ—u da mutanen nawa musamman ma Zuhra,tana ganina ta rungumeni tana ihu,ga amarya ga amarya ai kuwa Æ´an ajinmu suka zagaye ni suna tsokana ta,nan dai aka shiga hira da bani labarin abubuwanda suka faru da bana nan,kun san Æ´an makaranta da gulma.

Sai dariya na ke kamar ba niba,Zainab na zuwa ta dinga kallona up and down,na kalleta na ce"ke dalla banza me kuma ki ke wani ƙare min kallo?".na faɗi hakan ina dariya dimpils ɗina sai lotsawa suke gwanin sha'awa.

Ta magantu sannan ta ce"haba khairat ba dole in kalleki ba,kinyi aure madadin muga kinyi ƙiba .sai wannan uwar ramar da ki kayi,jibe kifa da ma har kinfi ƙibar?".

Shiru kawai na yi na sunkuyar da kaina don bansan ma me zance musu ba,lamarin aure wuyar sha'ani gare sa,balle kuma na karanta na sani Allah ya tsinewa mai tonawa mijinsa asiri,na wayance na ce"hmm rashin lafiya na yi ne maleria ke damu na,amman yanzu naji sauƙi sosai."

HaÉ—a baki sukayi wajen yimin sannu,nan dai aka cigaba da hira na ke tambayarsu abinda za'ayi yau.Zainab ta ce"hmm mutuminki ne kuma kinsan ya yi tafiya".

"Na ce to ni ina ruwa na da tafiyarsa Allah ya dawo dashi lafiya,daman baƙuwa zanyi ne shiyasa na damu,amman yanzu zan tafi".

Har bakin titi suka rakoni na hau adaidaita sannan suma suka tafi gida,ina zuwa gida na ajje jakata nasha ruwa na jiƙa maƙoshi na,na shiga aikin girki,ina cikin aikin naji ana ɗan buga bell ta ƙofar falona,na goge hannuna na fito,Halisa ce tsaye bakin ƙofar ta sakarmin murmushi ta shigo.

Na gaishe ta tare da kawo mata five alive da kuma ruwa,sai kayan gara ta dubulan da alkaki da kuma cincin,na ce mata zanje kitchen in ƙarasa girki.ta ce"a'ah muje tare in taya ki,ai nima na ɗan wasa jini".muka saka dariya muka shiga kitchen ɗin tare muna girkin muna hirarmu gwanin sha'awa.

Na fuskanci Halisa macece mai hankali da kuma kamun kai,na yarda da hankalinta har naji ina tunanin sanar da ita halin dana ke ciki,ko zata taimakamin.

Muna aikin na kalleta na ce"maman Junior don Allah so nake in faɗa miki wani abu,ina son ki bani shawara akan hakan?".murmushi kawai ta yi sannan ta ce"ayya ba komai ina jinki?ai ke tamkar ƙanwata haka na ɗaukeki".

Babu abinda na ɓoye mata akan zamana da yaya Bilal,har na gama magana ta,kallona kawai take sannan ta ce"kash!gaskiya khairat kinyi sakaci babba tun acen baya,shi fa namiji da ki ke ganinsa ba'a nuna masa so me yawa,matuƙar ki ka nuna masa duk duniya babu kamarsa insha Allah to ke ce baiwarsa,don ko yana sonki to za kiga ya rage sonki,shi namiji haka ya ke yafi son mace me aji sosai,ba wacce zai sameta kai tsaye ba,abu na farko da zan nuna miki shine,kibi duk hanyar da zaki bi mijinki ya dawo hannunki,ba tare da kin nuna masa fuskar kina son ku daidai ta bane,kissa da kisisina ita ce ke jan hankali miji awajenki,ko da bai ra'ayinki don dole yaji babu kamarki,don haka yanzu ki buɗe kunnuwanki kiji ni?dole kayan sakawarki ki ajje duk wata atamfa da leshi agefe,ya zamo kayan sakawarki ƙananun kaya ne,Sannan ya xamana kin iya tafiya ta jan hankali tare da salo salo kala2 ta yadda zaki dinga jan hankalinsa".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.