Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 5 of 90
Mama da ke ɗakin Abba tana gyara masa shimfiɗa ta jiyo ihuna ta fito da saurin gaske har tana tumtuɓe ta ce"ke Khairat lafiya me ya faru?".
ban iya ba ta amsa ba da sauri na rungumeta ina shesshaƙa kamar zan haɗiye zuciya,ta gane me ya faru don haka bata ce komai ba taja hannuwa na muka koma ɗakinta.
"Da mana ayi magana in zageki tsaf kema don daman akanki na ke son hucewa,da anyi magana sai miji ya ce Zulaiha! zulaiha!wai ita ga ta matar so,ko uban waye ba matar so ba oho".
Anty Zeenatu ita ce ta tsakiyar da ya ke matan babana uku mama na ce Amarya sai kuwa ta ce"Hmm Iklima ai mu da sauƙi tunda asalinmu musulmaine munsha ruwan musulunci ita kuwa fa,tuban muzuru ne fa".
ashe wannan ihun da na yi Hajiya Kaka ta ji alokacin Ƙasim ɗan Baba Auwalu zai kaita unguwa sai kuwa ta ce"kai Ƙasimu ni kukan wa na ke ji ne?".
"gaskiya Kaka ki daina ce min Ƙasimu haka kawai da suna na Aqasim mai daɗi sai kuma a ɓata min,gaskiya a kiyaye?".
"don ubanka ko Auwalu bai isa ya bani doka da order ba,don ba shine ya haifeni ba ni ce na haifesa,don haka ka ki yaye wallahi,ko inci uwarka mai ƙosan siyarwa,ni dai Ƴaƴana sun ɗebowa ruwan dafa kansu daga taimako sai kaga sun auresu ni kuma azo ana gasa ni,akan me ban hana aurensu ba sai kuma ni ace za a takuramin,to wallahi ni babu ruwana gaskiya tana zuwa zan faɗa sai dai mutane suji haushi".
tuni har Ƙasim ya shige mota yana hango Kaka tana ta surutanta don shi bai ma san abinda ta ke ce wa,ya kalli jakar da tasa ka shi riƙewa wai ita daman cen idan zasu fita da mijinta kakansu shine ya ke riƙe mata jaka,duk da kasancewarsa soja baya jin kunya haka ya ke riƙewa,Ƙasim ya yi tsaki yana wani hararar Kaka.
Har ta fara tafiya sai kuma ta ƙara jiyo sautin ihun da ya ke sashenmu ne akusa dana Kaka,don haka duk wasu abubuwan ana iya jiyo su.
Da sauri ta yi sashenmu tana ce wa"wani mai son aci mar mutunci ne ya saka jikata kuka?".tana faɗar hakan tana shigowa farlon da ƙer don ya yi ɗan tsayi tudun farlonmu.
Dukansu shiga taitayinsu sukayi suka haɗe fuska suna gaishe da Kaka amman ko kallonsu ba ta yi ba ta ce"waye ya saka Khairat kuka a cikinku?".sunkui da kai suka fara yi suna ƴan muzurai tare da sosai ƙeya don duk abinsu suna matuƙar jin tsoron Hajiya Kaka don aƙwaita da tonon asiri.
"Ba daku na ke bane ku ke wani sunkui da kai kamar baƙin ɓarayi"?.da ƙer Anty Xeenatu ta ce"da man Hajiya Kaka Khairat ce ta yi wa Hajiya Iklima rashin kunya to shine". . .
"shine me?".
Babu wanda ya ce kanzil duk kawunansu a ƙasa,dai kuwa Kaka ta ƙwala ƙara tana ce wa"Zulai ke Xulai wai kina ina ne kizo ana son kashe miki ƴa".
da sauri muka fito daga ni har Mama fuskata ta kumbura sosai ga marin Yaya Bilal ga kuma na Hajiya Iklima sai abin ya yi min yawa kumatun na wa suka kumbura sosai abin tausayi.
"La ha ila ha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam,Khairat me na ke gani a kuncinki kamar mari rututu haka?,ɓoye fuskar na yi ina muzurai don nasan tunda Kaka ta zo to tabbas ko wa sai ya taru agidan,don Kaka aƙwai son jikoki tun ma ba ni ba.
Dukkansu tashi sukayi tsaye suna bawa Kaka haƙuri don sun san ko da basu ma tashi ba to yanzu zasu tashin don sai ta tara musu mutane.
Ko kallonsu ba ta yi ba,tana ta faman girgixa ƙafafu alamar yau aƙwai masifa a gidan.
Ko da Ƙasim ya gaji da jiran Hajiya Kaka sai ga shi ya biyota sashenmu ya tarar ana dirama,gurin zama kawai ya nema ya zauna don yasan wannan tsayuwar da kakar ta sa ta yi sai akai dare ana abu ɗaya,don kaka bata san ta yi abu ɗaya ta yi shiru ba.
Tun ana abun tsakanin ɓangarenmu har ƴan sauran ɓangaren sashen suka fara tururuwar shugowa har ana ƴan rige rige.
Umma ce kawai bata shigoba mahaifiyar Bilal don dawowarta daga makaranta kenan,don ita ce headmaster a makarantar Æ´an matan da take.
Kowa ya baza idanu ya ji abinda zai faru,masu dariya na yi masu jin haushi suma ba a barsu a baya ba.
"Wallahi yau bazan yarda ba,bari Malik ɗin yaxo idanma shine ya ɗaure muku gindin dukan jikata yau zanji,wannan wani irin rashin imanine kamar an samu ƙato,duk cikinku wa ubanta ya taɓa duka?ku gaya min tambayarku na ke"?.
babu mai bawa Hajiya Kaka amsa,don idan kaka na abinta kowa shiru ya ke idan ba haka ba sai a dawo kansa.
Ƙasim kaka ta kalla ta ce"kai uban son gulma kirawo min ɗana Malik,yanzu duk abinda ya ke ya dawo gida don bazan yarda ba wallahi sai an karɓarwa jikata ƴanci don har hukuma yau sai munje wallahi".
ai suna jin maganar hukuma suka tsugunna har ƙasa suna ba ta haƙuri amman fir Kaka ta ce bata san zance ba".
yana ɗauka kaka ta warce wayar ta ce"kai Malik uwarka ce ke magana duk abinda ka ke ka yi hanzarin dawowa gida,don wallahi yau sai dai ka zaɓa ko ni ko ƴan iskan matanka Iklima da Xeenatu".
yana jin hakan ya ce"ganinan zuwa Umma".ƙit ta kashe wayar ta jehowa Ƙasim,ya yi saurin cafkewa don sauran ƙiris wayar tasha ƙasa.
Mintina kaɗan sai ga shi don daman ba nisa ya yi ba,suna meeting ne a gidan gomnati,tunda ya sauka a mota ya hango ɓangaren na su a cike an ɗaga labule yasan Hajiya Kaka ce da wannan aikin don in dai za ta yi faɗanta ɗaga labule take.
Yana zuwa kowa ya fita don suna matuƙar jin tsoronsa don sam bashi da wasa ko kaɗan balle wargi soja sak a haka ma idan ya juya sai ka ɗauka Bilal ne don suna matuƙar kama da Bilal ɗin.
A hankali ya zauna sannan ya gaida kaka amman ko amsawa bata yi ba ta ce"yo ta ina zan amsa maka ana neman kashe min jikata,janyo ni ta yi ta gurfanar gaban Abba gabana sai faɗuwa ya ke don muna matuƙar jin tsoronsa,duk da wataran yana sakar mana fuska.
Abba ya kalleni sosai ya kalli kuncina ya kalli kaka da mutanen wajen ya ce"waye ya yi mata wannan bin cikinku"?.
Dukkansu har Mamana sai da hankalinta ya tashi don cikin kakkausar murya ya yi maganar,idanuwansa sun kaÉ—a sunyi jawur jin babu wanda ya basa amsa sai ya ce"babu wanda zaiyi magana acikinku?tunda duk kun rainani ko?".
"yo ta yaya za'ayi suyi magana munafukan banza da wofi kawai,to idan baza ku faɗa ba ni bari in faɗa ka ga wannan ƴar me tallan ƙosan da waccen almurar ƴar fillon dajin suka haɗu suka mari Khairat a fuska ka ga yanzu sun janyo maka asara don ko babu komai ka kashe kuɗi a asibiti."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.