Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 39 of 90

Sannan ya ce"ina son ki bani haɗin kai akan abinda na keson inyi,bujeremin dai dai ya ke da mutuwar Bilal da kuma iyayenki,idan ki ka bani haɗin kao zan baki kuɗi mai tsoka wanda har ki gama rayuwarki baki ƙarar dasu ba,yanzu abinda na keso dake ki faɗawa iyayenki ce war zaki fita da Bilal siyayya".

watso masa manyan idanuwanta ta yo tsoro ƙarara ya bayyana a idanuwanta,ji take tamkar za tayi fitsari saboda tsoron mutumin babu yadda ta iya haka ta kira waya ta shaidawa mamanta zasu fita da Bilal".

Kai tsaye babban gidansa na shaƙatawa suka isa,suna zuwa yaransa suka fito suka buɗe masa ƙofa,duk jikin jidda ya yi mugun sanyi ga wani mummunan tsoro da take ji.

Suna shiga ya kalleta sannan ya ce"ki saki jikinki jidda kada ki sake ki nunamin tsoro,don wannan harkar mun fara ta kenan,har sai naga bayan abinda na keson gani".

A takure take dashi wani abu taji an shaƙa mata a hancinta tun daga nan bata ƙara sanin inda kanta ya ke ba,sai tashi tayi ta jita acikin mummunan yanayi,ta yi yunƙurin tashi taji ta kasa tashi ta fasa wani irin mugun kuka mai cin rai,wato daman wannan mutumin ya kawo ta nan ne don ya wulaƙanta mata rayuwa?a satin ɗaurin aurenta?yanzu me zata ce wa Bilal idan hwt ya gane ce wa ita ba budurwa bace?hankalinta ya yi mugun tashi ta saki wani kuka me mugun ƙarfi.

Da kansa ya shigo ya kalleta sosai sannan ya ce"jidda wannan abinda na yi miki nima ba ui sane amtsayin ramuwar gayya akan Bilal,saboda yadda ya keson wulaƙanta ni a idon duniya,shiyasa na nemi wannan hanyar don baƙanta masa,idan ki ka yi gangancin faɗa masa wallahi duk ida kika shiga sai na nemoki,bazan taɓa barinki ba".

ya turo mata wata jakar kuÉ—i sannan ya ce"wannsn kuÉ—in duk na kine,idan kinso ki sakasu a account,idan kinso ki barsu?idan kika haÉ—a kai dani babu abinda bazan miki ba".

yana faÉ—ar hakan ya cillo mata mukullin gida ya ce"wannan mukullin É—aya ne daga cikin gidajs na waÉ—anda na keji dasu,shine na baki shi halak malak,gidane ns haya mai part 50 dai yadda ki ka yi dashi yanzu ya zama naki".

habawa kunsan mutum da kuɗi tuni Jidda ta saki jikinta da Alhaji Damas,tun daga ranar ta zama kamar wata yarinyarsa,kafin ƙwana tara na aurenta,sai ta yi wa iyayenta ƙarya tace sun fita da Bilal alhalin tana wajensa,aƙwai ƙawarta Wata Rabi'atu babu abinda bata sani ba na dangantarka Damas da kuma Jidda.

Saboda kuÉ—i yasa ta yi shiru da bakinta tunda ana É—an gutsira mata,sosai jidda ta kashe kuÉ—i saboda gyaran kanta don tasan ayadda take,naira na gugab naira dubu É—ari biyar haka ta bayar wai duk don ta dawo budurwa.

Sosai iyayenta suke tuhumarta akan kashe kuɗinta,amman da ya ke tana musu ƙarya da Bilal sai suka daina tuhumarta ta cigaba da wandaƘarta da kuƊaƊa,sosai ta ware kuƊi don siyan wasu kayan kitchen da sauran abubuwa.

Alhaji damas ys samu yadda ya keso,don haka yanzu wani kallon tara saura Ƙwata ya kewa Bilal,gani ya ke tamkar fankonsa ya ke ganinsa,tunda wadda ya bawa amanarsa,ya Ɗauketa matsayin mai tarbiyya to fa ta watsar da komai ga Alhaji damas,ta bashi komai ta yadda shi Bilal Ɗin ko alfarmar riƘe hannunta bai samu ba.

sosai wannan abu yake masa daƊi saboda ko ayanzu ya gama da Bilal, gamawar har ya mutu bazai taƁa mantata ba.
****

koda aka tashi yin dinner babu yadda Rashida bata yi dani ba,akan inje dinner Ɗin naƘi zuwa tunda dai ni ba sona ake ba,to kuma me zanje inyi?Don yaya Bilak bazai ji kunyar wulaƘanta ni awajen mutane ba.

Da Rashida tarasa yadda za tayi dani sai taje ta sanu yaya Aliyu ta gaya masa komai,yazo ya yi min faƊa akan inje,kuma su yaya salim ma duk zasuyi idan har banje ba baza suji daƊi ba,haka dai na haƘura amman can cikin zuciyata tsoro fal.

Ana cikin maganar hajiya kaka ta fito daga kinta baya sun gama faɗa da mero.sai kuwa ta ce"kai Aliyu rabu da ƴar banza,ina cewa nan naji kina gayyatar ƙawayenki fatin?sai yanzu za'a wani zo ana wani rarrashinki akan kije?to yasin kada kije ni daman haka zanso sai in hakimce akan kujerarki ince ni ce uwargida.

Duk wanda ke wajen sai da ya yi dariya sosai,ni kuwa kallonsu kawai na ke,ɗaurin aurena da za'ayi da Yaya Bilal shine kawai ya tsayamin aƙoƙon zuciyata,ko wani irin zama zanyi dashi oho?.

Ƙwalliya aka yimin sosai wacce ni da kaina sai da na yaba kaina,wani farin les ne wanda ya gaji da haɗuwa gashi yaji ruwan stones sai walƙiya ya ke,kamar ka ɗaukeni,ƴar pos ɗina da kuma takalmi na duk ash ne suma sunji ruwan stone,diri na sosai ya fito da ya ke ni dirarriyar macece,sai na haska na yi wani irin bajajjan ƙyau wanda ya amsa sunansa aƙyau,head ɗina ma arsh ne sai net golden shima sai walƙiya ya ke,aka yafamin shi akaina.

"Wow gaskiya amaryarmu kinyi ƙyau sosai,gaskiya yaya na zaiyi santin kyaun nan".cewar Rashida wacce ke ta faman ɗauka ta a hoto kamar babu gobe.

Bansan lokacin da naji wani hawaye yana zubomin ba,da gudu na tafi naje na rungume mahaifiyata tsam kamar wani zai ƙwacemin ita,i'tama ɗin rungume ni ta yi tana ɗan buga bayana tana rarrashina,har cikin zuciyarta take jin babu daɗi arabuwa da tilon ƴarta mace da zata yi.

Su mero ana gefe ansha ƙwalliya sai ka rantse ba meron hajiya kaka bace,ganin khairat na kuka dai yasa duk jikinta itama ya yi sanyi sosai,ta koma gefe ta rakuɓe tana kallon uwarta hansai wacce ke ta shirinta cikin haɗaɗɗiyar atamfarta super wacce Hajiya kaka ta bata.

Itama da gudu taje ta rungume hansai tana ta kuka,Hajiya kaka ta ce"kai ku ganemin wani shashanci,don kunga iyayenku na wajen suna ƙefta muka idanuwa ku taso kuyi kuka shine zaku faramin kuka kamar gidan mutuwa?to wallahi ba dani ba,duk shegiyar da ta ƙaramin kuka yasin sai na saka jikana fasa aurenta".

dukkanmu juyowa mukayi muna kallon hajiya kaka,wacce ta yi mirsisi kamar ba ita ce ta yi maganar ba,ta ɓantari guntun goronta ta saka abakinta tana tauna,ganin duk muna kallonta sai kuwa ta ce"meye ne kuma kuke kallona?To wallahi kuruwa ta kurr akanku,ina ƙwanannan aka samu wata shegiyar ta yi min asiri cikin matan ƴaƴana?duk da ban yarda da hakanba,don ni dai naci dubu sai ceto,mai dambu kafin ta mutu ta barmin tsari ajikina.kunga kuwa kuma sai dai kuci kanku".ta faɗi hakan tana zare fici-ficin idanuwanta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.