Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 78 of 90
Tuni aka dinga É—aukar hotunansu ana turawa ta facebook,lefe na ya girgiza Æ´an mata da dama sosai,suka shiga burin ina ma ace suma su samu wannan kaya haka.
Sosai na shiga gyaran jiki na ciki da waje,mama da kanta ta hau gyara ni sosai na yi kyau kamar ba ni ba,Mama ta ɗaukomin me gyaran jiki har gida ai kuwa kafin kace me na yi wani irin mugun kyau kamar ka ɗauke ni,sau ɗaukar ido na ke,na karɓi hutu a skull saboda gyaran da na ke,abin mamaki kawai sai ga Xuhra ta zo wai taji labarin biki na,na yi mamaki sosai harda dariya ta,wato daman tana gaba da nine saboda kada in auri mijinta?babu yadda zanyi don daman ni ban riƙe ta ba,muka cigaba da al'amuranmu tare har yanzu bata haihu ba Allah bai kawo ba.
Shahid ya maƙale murya kamar yaro ya ce"gaskiya Hayatee na gaji ki fito ko kaɗanne in ganki mana?tunda aka fara sha'anin biki bana ganinki,sai ɓoyemin kanki ki ke?".shgwaɓa ya dinga yimin kamar yaro,babu yadda zanyi dole na saka wata arabian gown,me kyau sosai kalar yellow,na yafa velt ɗin akaina na fito,gashi na yasha gyara sosai.
Tun daga nesa ya sakani agaba da kallo kamar zai cinye ni,kunya duk ta ishe ni Iman ta biyo ni da gudu wai zata bini,maimakon tazo inda na ke sai naga ta canja Æ™wana tana ce wa"Baba oyoyo". Da sauri na É—aga kai na ina kallon wanda take kira da baban Bilal na hango yana sanye cikin kayan sojinsa ya haÉ—e rai kamar bai taÉ“a wata dariya ba.. ... .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
[23/09, 16:30] Miss GreenðŸ€: 91. . . . . . .92
. . . . . . .nunawa na yi kamar bansan abinda suke ba,na yi wuce wata gaba zuwa wajsn masoyi na,fuskata Ɗauke da murmushi,wani irin kallo me cike da soyayya ya ke yimin yadda yaga na komar kamar Ƴar shekara goma yarinta na ta Ƙara fitowa sosai,ga wani irin mugun Ƙamshin dana ke fitarwa me gigita namiji,ai kuwa shahid ya gigice Ɗin sosai amman duk da haka hankalinsa na kan Bilal wanda ya Ɗaga iman sama yana yi mata wasa.
Ya ce"hayatee wannan shine baban lovely children ÆŠina"?.sosai gabana ya faÆŠi ahankali na ce"eh shine na manta ban faÆŠa maka ba,yaya ya ke gare ni".sai naga fuskarsa ta haÆŠe nan da nan,na lura shahid shima namijin kishi ne sosai,daman kuma ance larabawa sunfi kowa kishi.
Ya ce"ayya kada ki damu don na tambaye ki ki yi haƘuri,amman wannan yayan na ki wata macece za ta ce bata sonshi?babu abinda Allah bai yi Masa ba,amman na yi mamakin rabuwarku,kuma kema khairat nasan ba zai so rabuwa da ke ba,sai dai Ƙaddara amman duk namijin daya sakeki khairat wallahi ya yi asara gaskiya".
Murmushi kawai Na yi don bani da amsar da zan bashi,don kada yabi inda muke sai ya Ɗauki Ƴarsa suka yi gaba abinsu.Ina jinsa yana tambayarta Ƴan uwanta,sai kuwa iman ta ce"dady mamanmu ta Ƙara yi mana wani dadyn ka ganchi cen ma".ta fara nuno inda Muke.Bilal bai san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka fara zubo masa ba ya yi saurin gogewa ya wuce.
to ranar dai da Ƙer shahid ya barni na wuce gida na lura bai gajiya da kallona,idan na biye masa kuma sai muyi ta tsayuwa awajen,don haka na ce"habibee ni zan tafi gida fa mun daÆŠe".na faÆŠi hakan cikin shagwaÆa,sosai na burgesa ya ce"ah lallai baki so kije gida yanzu,ni wannan shagwaÆar taki tafi komai tafiya dani",yauwa khairat ki yi haƘuri ni dinner bata cikin tsarina sam,duk kuwa kuÆŠin da na ke dashi,amman mu al'adarmu a musulunce shine bayan anyi aure ana walima washe gari,to ni dai hakan yafi Ƙwantamin".
murmushi na yi sannan na ce"kada Ka damu nima duk wannan bidi'ar bata gabana albarkar auren shi na keso".sosai na burgesa amman fa muna cikin zancen naji alert Ɗin kuƊi awayata na ce"habibee naga ka turomin kuƊi me zanyi dasu haka"?.murmushi ya yi sannan ya ce"ki yi wani abin dasu,amarya ta me sirrin kyau".ya faƊi hakan yana murmushi,bai bani damar Ƙara magana ba ya yi shigewarsa cikin mota ya yi gaba.
Sosai na keson shahid,ba don kuÆŠinsa ko kyau ba,a'ah sai don tsare mutuncinsa,sam bai taÆa koda taÆa hannuna da sunan wasa ba,balle kuma wata maganar banza,muna mutunta kanmu mu duka,anan na ke jan hankalin Ƴan mata da zawarawa adinga riƘe mutunci da kyau,saboda ke mace duk abinda ki ka yi bai Æoyuwa namiji kuwa ko zai yi sau ÆŠari ba'a Ganewa,kuma a musulunce ma hakan sam ba shida kyau kuma ma ba tarbiyya bace.kuma matuƘar ki ka sadaukar da mutuncinki ga wani to fa wannan mijin koda tare ku ka yi lalatar bazai taÆa ganin darajarki ba,balle kuma akaiga zancen mutuntawa,don shi aure anfison ayisa da ganin mutuncin juna.
da kai na na ware kuƊi masu yawa aka sakewa hajiya kaka sabbin kayan Ɗaki aka yi mata sabon fenti,mama na itama aka sake yi mata furnitures duk da basu daƊe ba,sannan mama ta faƊawa babana duk kuƊin da shahid ya ke bani,baiyi mamaki ba ko kaƊan don yaron yasan tarihinsa tun farko har zuwa yanzu,mahaifiyarsa da mahaifinsa suna da kuƊi sosai kuƊi kuma masu mugun yawa,shi da kansa shahid a iya nigeria ma yana da company's sunfi ashirin,ga kuma na Ƙasashen waje,uwa uba kuma likita ne me zaman kansa me kuma lasisin kowacce Ƙasa,likitan zuciya ne shi,mahaifiyarshi kuma unguwar xoma ce.kuma ba Ƙaramin kuƊi suke samu ba.
ranar daya rage saura Ƙwana biyu gidanmu ya cika Æam kamar auren budurwa,son hatta ankon biki,sai da shahid ya turomin kuÆŠi wai abawa kowa,wai su haka suke yi naƘi amsa sai gashi ya lallaÆa yaje wajen hajiya kaka,itama da farko taƘi amsa amman da taga ransa ya Æaci sai ta amsa,ai kuwa kowa sai daya samu ankon biki,ranar Ne kuma amminsa tazo gidanmu mata mai mutunci da sanin darajar mutane,ta ÆŠakko wata mata wai za ta yimin gyaran jiki na larabawa.
daga ganin matar ma balarabiya ce wataƘil ÆŠakkota aka yi,,harda Ƙanwarta tazo ita ammin,duk suna da mutunci sosai naƘi fitowa wai ina jin kunyarsu ta ce"a'ah khairat mufa bama jin wannan kunyar gwarama tun yanzu ki saba don shahid ba shida kunya wallahi".murmushi kawai na yi ai kuwa aranar aka fara yimin gyaran jikin,wowo hmm wai ko tsagar gida ma hanani fita matar ta yi sai dai ina ÆŠaki ina shan a/c,Mutanen gidanmu suka dinga zuwa ganin ammin shahid,shima tun daga ranar ammin ta hanashi xuwa saboda gudun saÆawa Allah don taga yadda Ƙirar khairat ÆŠin take,ba kowani namiji ne xai iya kallonta ya kyale ba,duk da ta yarda da ÆŠanta mutum ne me kana kansa sosai,da tsantsae tsoron Allah,,shiyasa a kullum take godewa Allah da kyautar da ya yi mata na samun ÆŠa kamar shahid,daman kuma ba yawan yara akeso ba albarkarsu ake nema.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.