Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 9 of 90
Jikina a sanyaye na tashi na cire kayana na faɗa banɗaki bayan Rashida ta fito,ko a wajen wankan ma tunani kawai na ke na yadda zan ɓullowa lamarinsu Nadiya don idan wani yaji wannan maganar a gidanmu to tabbas zasu shiga tsaka mai wuya don hatta kashi ma sai ya fisu mahimmanci a gidanmu.
Bacci ma da ƙer ya ɗaukeni saboda tunani,ni mutunce mai saka abu arai musamman wannan abin daya kasa gogewa a zuciya ta,a duk tsahon rayuwata ban taɓa saka wani abu araina irin Yaya Bilal ba sai kuma wannan maganar tasu Nadiya.
Da sassafe muka tashi muna shirin tafiya assembly don yau litinan(monday)uniform ɗinmu kalar baƙi da fari wato black&white riga da hijab duk fari wando baƙi kamar kalar kayan likitoci,munyi ƙyau sosai acikin kayan na mu muka jero mu uku ni da Rashida da Hasiya don daman mu uku ne acikin ɗakin.
Ta ƙofar hostel ɗinsu Nadiya muka biyo abin mamaki su haryanzu basu fito assembly ɗin ba,na kalli Rashida cikin dakiya da nuna kulawa na ce"Rashida don Allah mu shiga wajensu Nadiya mana mu duba su".?kallon tsaf ta yi min sannan ta ce"Hmm gaskiya Khairat kina da matsala wallahi yanzu ko jiya ma fa sai da mukayi maganar nan,bana son ki jefa kanki acikin matsala garin gyara kuma ku ɓallowa kanki matsala,don kin san grp ɗinsu ɗaya da big girl kuma kin san daman tana harinki a skull ɗinnan don ki zama lalatacciya irinsu,to kinga idan kina zuwa wajensu komai zai iya faruwa da ke".ta faɗi hakan tana kallona sosai fuskarta alamun jin tausayina.
Hasiya ta da fa kafaɗa ta ta ce"Khairat bama son abinda zai taɓa rayuwarki ki yi haƙuri don Allah ki taho mu tafi,ki dinga taya su kawai da addu'ah kuma ki yi amfani da shawarar dana baki jiya,ko da kun koma gida kada ki manta wannan shawarar dana baki".
gyaɗa kaina na yi kawai na bisu don hankalina nima bai ƙwanta da zuwan na wa ba,abin mamaki sai da aka kusa gama assembly sannan suka shigo suna wani bubbuɗawa duk idanuwansu sun kumbura alamar basuyi bacci ba,Rashida ta ce"Allah dai ya shirya wallahi sun ƙwana suna lalacewarsu ai dole ido ya kumbura,iyayenmu na cen suna tattalin rayuwarmu da bamu tarbiyya amman su ƴan rashin kamun kai suna nan suna lalacewa."
nima ganinsu da na yi sai da gabana ya faɗi saboda ganinsu a cikin wannan halin don ko da ba'a gaya maka ba kasan abinda ya faru,na ji wata ƙwalla mai zafin gaske ta zubomin na saka hannaye na na sharesu Rashida tana kallona ta ce"iska tana wahalar da mai kayan kara".
rai na duk babu daɗi har aka gama assemly ɗin muka shiga aji,muna fitowa muka koma hostel ɗinmu muka fara girki ƴar ƙaramar wayar Rashida ta fara ƙara ta ɗaga tana ce wa waye?".shiru akayi kafin daga bisani taji ance "abdullahi ne don jakar ubanki".tsalle Rashida ta yi ta ce"Hajiya kaka daman kina duniya"?.da sauri na amshe wayar harda ƴar ƙwallah ta ka fin inyi magana ta ce a bawa ABIN CIKIN ƘWAI,in dai kaji kaka ta faɗi wannan sunan to tabbas dani take.
Rashida ta ce"to ai tun kafin ma in ba ta ta amshe ita me kaka".ina jin kaka tana ce wa"to ke kuma da ba kakar ki ba ce sai ki siyo a kasuwa".riƙe kai Rashida ta yi Hasiya tana ta ɓaɓɓaka dariya don ita dai Allah ya saka mata son tsohuwar aranta.
"Hmm Abin cikin ƙwai ni dai ina ganin baƙin ciki a gidannan wallahi?idan suka isheni wallahi tattara kayana zanyi in koma uman wajen ƴan uwan mahaifina ko kuma in tafi Bauchi".tana faɗar hakan ta tintsire da kuka.
Haba ai Rashida dariya harda tsalle tana ce wa"Hajiya kaka yasin kin kusa margayawa ki yadda kawai,amman in banda tsufa ba'ayiwa mutum komai ba sai ya tattara kayansa yabar gida".?
kaka na juyo ta ta ce"shegiya jinin fulani muguwa kawau to babu inda zanje sai inga ta dariya,daman uwarki ce ta ɓata min ran wai akan Sadiq ɗan wajen auwalu ya ce yana son nusaiba shikkenan tsohuwar ƴar bokon nan uwarku ruƙayya ta kafa ta tsare wai ita bata son auren dangi,yanzu don Allah idan banda baƙin hali ita da ubanku ba auren dangi bane?".
Haƙuri na fara bawa Hajiya kaka ta ce"ai wallahi da ce wa na yi tafiya ta zanyi tunda ita dai bata san kara ba".Rashida da ke jinmu tana kallona alamun dai bata ji daɗin zagin da kaka take wa mahaifiyarta ba.
Nima da ba uwata aka zaga ba tabbas banji daɗi ba,in banda abin kaka ai nusaibar nan dai ƴar ta ce ko?amman kuma ta ce bata so saboda nusaiba yarinya ce har ayanzu bata rufa sha 15 ba a s.s.1 take mu kuma muna da 17 aduniya yanzu kuma muna s.s.3 muna shekararmu ta ƙarshe. Nan dai Hajiya kaka ta gama faɗanta daga baya ta kashe wayar,muna gama wayar na kalli Rashida na ce"kai kaka aƙwaita da fi'ili wallahi kamar dole sai ta haɗamu auren dangi haka fa kema da yaya mohd ta da ge sai ya aure ki,don Allah yanzu me ye amfanin auren."?
"Khairat kenan ita fa wannan tsohuwar haka take ni wallahi har Allah Allah na dingayi mu taho saboda yadda tsohuwar nan ta sakani a gaba wai sau na auri yaya mohd,kuma ni wallahi na fi son har inyi jami'a kafin inyi aure."
da fa kafaɗarta na yi sannan na ce"ki yi haƙuri don Allah Rashida akan wannan maganar ki cigaba da addu'a kinga dai yadda kaka ta dage yaya Mohd zaki aura shima kuma ya dage ke ya ke so,to kinga addu'a ita ce mafita don kinga duk su Baba da abinda kaka ta faɗa musu suke amfani don haka kawai sai dai ki yi haƙuri."
"Khairat ni fa wallahi bana sonshi wallahi,ke kin sani idan yaya Mohd yana da ƙyau yana da kuɗi amman ni wallahi matsalar mahaifiyarsa ita ce kawai za ta takuramin ko da bayan anyi auran ne?.
"Tabbas matar Baba tijjani tana da babbar matsala sosai don ko yaya sulaiman babban ɗanta daya auri ƴar gidan Baba Bashir haka ta takura mata zagin yau na gobe daban,don ma kaka tana ta ka mata burki da abin sai ya ɓaci sosai."
"to kin gani khairat to a haka zan auri Yaya Mohd daman kuma duk Æ´aÆ´anta ta fi sonshi sai kawai ace shi zan aura in auri masifa,Allah ni fa bazan aureshi ba gaskiyar magana".tana faÉ—ar hakan ta tashi ta bar wajen.
Na bita da kallo ita sonta ma ake ina ga kuma ni da ba son na wa ake ba shisshigina kawai na ke,yadda yaya Bilal ya tsane ni kamar mutuwarsa,ni kuma na nace sai shi,tabbas idan ban auri yaya Bilal ba to wallahi ni nasan ko da wani ya aure ni to gangar jikina ya aura don bazan taɓa sonsa ba zuciyata da komai na wa yana ga yaya Bilal,ina ma zai soni ko da bai kai yadda na ke sonshi ba,da ranar har azumi sai na yi saboda jin daɗin hakan.
Mun fara exam ɗin second time wacce zamu tafi hutu sannan mu dawo zana jarrabawar waec da neco,muna ta karatu sosai ba mu da lokacin kanmu sam sai na karatu muna dawowa daga class zamu yi bitar haddarmu ayanzu muna izu hamsin da biyar baƙara ce kawai bamuyi ba itama kuma mun iyata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.