Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 15 of 90

baiyi niyyar dariya ba amman sao da ya yi ya ce"to ke hajiya idan akaje naushi ÆŠaya za'ayi miku ki baje awajen".

ni dai raƁewa na yi a gefe kamar wata munafuka ya buga min wani banzan kallo sannan ya ce"ke tashi ki fita ni sa'anki ne da zaki zauna kina kallon bakina ina magana,comon dalla tashi ki fita Ƙazama kawai me shegen kallo kamar mayya".

*Miss green ce*

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------

masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.

*Sirrinmu*

Manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da cin naman mutane,ma'ana gulma ka yi gulmar mutamin da baya wajen Allah ya tsaremu amin.
-----------------------

13🟦14

........sosai sukayi mamakin kalamin kakar ta su,wai su za'a mayar ƴan aiki ko kuwa?bata ƙara kallonsu ba ta yi wucewarta,don ta yi alƙawarin sai ta koya musu hankali har kuka sai da ta yi don jin abinda jikokinta suke ai'katawa.

Washe gari a babban farlon gidan aka haɗu na cin abinci ƙaton teburine wanda ake haɗuwa duka family aci abinci don ƙara zumunci,kowa ya yi tsit baka jin ƙarar komai sai ƙarar cokali,wasu suna ci amman kamar suna cin kashi don hankalinsu a tashe ya ke da wannan haɗuwar wasun kuwa ba wasu bane illa su Nadiya,iman,samira,unaisa,khalisat,intisar,raudar,amina.

Duk hankulansu a matuƙar tashe ya ke don sun san har wanda bai san abinda sukayi ba to yau sai ya sani don wannan kakar tasu sai ta faɗa.

"To kunyi zungui zungui kuna kallona kamar baku sanni ba?to daman mun haÉ—une anan don wani gangarumin taro,don haka kowa ya buÉ—e kunnuwansa yaji."

Kowa kallon kaka ya ke saboda sun san aƙwai wata a ƙasa aƙwai wanda ya ke da rabon shan wulaƙanci shiyasa kowa ya kama bakinsa daga su har iyayensu,itama kakar kallonsu take azuciyarta ta ce yau kowa sai ya gane kurensa don wallahi baza'a janyo musu ɓarna har acikin gidansu ba.

Su kuwa Æ´aÆ´anta babu wanda baisan abinda kaka za ta faÉ—a ba,don jiya da daddare sunyi meeting akan hakan,Hajiya kaka ta kalli Baba Abdullahi ba tare da ta ce komai ba,sanin abinda take nufi ne ya yi gyaran murya ya fara jawabi kamar haka.

"Abisa yarjejeniyar da muka yanke tsakaninmu da mahaifiyarmu mun ɗaukar mata alƙawari kuma ayau zamu cika mata shi,ba neman shawarar kowa muke acikinku ba a'ah saboda haƙƙin kune a faɗa muku,mun yanke shawarar haɗa aure ga ƴaƴanmu don ƙara ƙulla zumunci."

gaban jikokin na su ne ya yanke ya faɗi karma ace maka su Nadiya sukayi tsiru suna kallon iyayen na su don jin waɗanda aka haɗa auren,ko har dasu oho?kai har dasu ɗinma tunda dai sune ƴan matan gidan,tuni cikinsu ya bada sauti ƙuuu alamun gudawa.

Baba Abdullahi ya cigaba da ce wa"to mun yanke shawarar gaÉ—a,Aliyu aure da Nadiya".zaro idanuwansu sukayi waje daga Aliyun har Nadiyar.

"Salimat kuma da Abbas,Amina da munir,khalisat da SadiÆ™,intisar da Hafiz,iman da Irfan,unaisa da maher,samira kuma da Arman."

dukkansu tashi sukayi tsaye suna kallon ikon Allah don basu taɓa tunanin wannan abin ba unexpected.babu wanda ya basu damar ce wa komai Baba malik mahaifinsu Khairat ya ce"mun saka ranar aure nan da wata biyu masu zuwa,dukkanku bama neman wani abu daga hannayenku duk abinda ya kama zamuyi sauran abubuwa ku tuntuɓi iyayenku".yana faɗar hakan ya tashi ya ce"to ni zan tafi wajen aiki ina da meeting sai anjima ".ya yiwa ƴan uwansa sallama da mahaifiyarsa sannan ya tafi.

Kallon juna aka shiga yi a babban farlon musamman waɗanda aka haɗa auren,gabansu sai faɗuwa ya ke acikinsu aƙwai waɗanda basu damu ba da haɗin da akayi musu amman fa Nadiya tafi shiga cikin tashin hankali don ita gani take ma kamar baza ta iya zaman auren ba.

Bayan taro ya tashi ko wa da abinda ya ke saƙawa acikin zuciyarsa,Rashid ta kalli Khairat cikin tsokana ta ce"to ikon Allah yanzu fa agidannan mune muka zana gwauraye don kowa da mijinsa".nima ƴar dariyar na yi sannan na ce"gaskiya wannan haɗin ya yi min sosai wallahi kinga ni daman su Nadiya na ke tunanin amman kinga yanzu rayuwarsu za ta inganta kuma yaya Aliyu mutunne mai mutunci da karramawa."Rashida ta yi min sannan ta ce"wai kina nufin daman Nadiya da Aliyu aka haɗa?".saurin ɗaga mata kai na yi alamar eh.hawaye naga yana fitowa a idanuwan Rashida na ce"a'ah me ya faru kuma"?.

ruƙo hannuwa na ta yi duka biyu muka shiga ɗan lungu da ke manne dana kaka,a hankali cikin siririyar murya ta ce"Khairat muna soyayya da yaya Aliyu fa?".da sauri naja ɗan baya na zaro idanuwa na waje alamar tsoro.
tausayi ta bani sosai a zuciyata kuma ina tuna girman zurfin cikin ita Rashidan da ko ni ban taɓa sani ba,a hankali na ce"haba Rashida gaskiya kinyi kuskure ba kaɗan ba wallahi,ko ni baki taɓa gayawa ba?ballan tana ma in taimaka miki ta wani ɓangaren,kin san yanzu kan iyayenmu a haɗe ya ke kada azo ayi abinda kansu zai rabe,kin san kawu Auwalu matarsa ta fi ƙarfinsa sai yadda ta yi dashi gashi kuma basa shiri da Mamanku kinga hakan kamar zai janyo wata matsala fa"?.

"Na sani Khairat amman wallahi mundaɗe muna soyayyarmu daman munƙi bayyanawa ne sai har mun gama makaranta.

Kasa ce wa komai na yi cen dai na ruƙo hannuwanta duka biyu na ce"Rashida aduk halin da zaki shiga bazan taɓa gudunki ba ina nan tare da ke,tun daga kan wasan ƙasa har zuwa yanzu munanan tare babu wani mahaluƙin da ya taɓa shiga tsakaninmu don haka kinga yanzuma dole in tsaya kaida ƙafa inga wannan al'amarin ya dai daita".

Kamar daga sama mukaji ana ce wa"ya dai dai ta ma ai".muryar kaka mukaji ta nufo inda muke ta ce"munafukar yarinya au ke yanzu daman kina son gadanga ƙusar yaƙi kika ƙi magana sai yanzu".?ƙada da kai Rashida ta yi tana zubarda hawaye tausayinta ya ɗarsu a zuciyar Hajiya kaka ta ruƙo hannun Rashida suka nufo ɗakin kaka Yaya Aliyu yana zaune akan kujerar kaka wadda aka zuba mata ƙwanannan kansa a ƙasa idanuwansa sunyi jawur kamar harda kayan aikinsa ma ajikinsa ba tare daya ciresu ba,kayan aikin likita yaya Aliyu likita ne na ganycology ma'ana likitan mata.
Yana ganin Rashida ta shigo ya tashi da sauri yana kallonta jikinsa duj babu ƙwari ya zauna yana ce wa"Rashida kinga yanzu abinda shirin mu ya ja mana,kin fiya zurfin ciki Rashida kin hanani gayawa kowa saboda sai kin gama makaranta za'a sani how comes hakan ya faru."ya faɗi hakan yana kallon Rashida.mu dai duk muna tsaye mun kasa zama sai da kaka ta ce"to aadarawan sarki ku zauna kun wani tsayamin akai".zama mukayi a kan capet ɗin ɗakinta ba ta ce komai ba ta janyo wayarta ta ce"ke Abin cikin ƙwai kirawo min abdullahi dai malik dai auwalu duk ki kirawomin su alokaci ɗaya."
Gabana yana faɗuwa na fara kiran Babana faɗa masa,sannan na kirawo su suma duk akayi sa'a suna cikin gidan dawowarsu kenan,su dukansu ta tarasu sannan ta ce"kun gane min waɗan cen ja'iran yaran".ta nuna su Rashida da Aliyu dukansu sunkuyar da kansu sukayi don kunya sannan kaka ta ɗora da cewa to kada ku ɗoramin laifi don nima ban sani ba?sai yanzu".duk iyayen nasu su suke kallo sun kasa gane inda maganar mahaifiyartasu ya dosa.Baba Auwalu ya ce"to umma me kuma ya ƙara faruwa kin sakamu acikin duhu?".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.