Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 12 of 90

Ina cikin wannan tunanin na shiga sashenmu kai tsaye na wuce sashen baccinmu daman kowa da ɗakin baccinsa amman yau ina shiga naga Nadiya a ɗakin baccina ta fito daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki tana jan ƙafarta da ƙer wata uwar harara ta bugamin sannan ta fita daga ɗakin ban kula taba na shige ɗakina na ƙwanta a hankali duk jikina yana yimin wani irin mugun ciwo wasu zafafan hawaye suka zubomin tuno da abinda ya faru dani.
Ina cikin wannan halin mama ta shigo ɗakin ta ce"a'ah khairat daman kina nan?ina ta tunanin shiga ɗakin kaka ashe kin shigo?tashi muje yayanki Bilal ya kirawo dr xai duba lafiyarki."har zuciyata na ji wani irin sanyi mai daɗi wai yaya Bilal ya kirawo likita?to ko dai shima ya fara sonane ban sani ba?ina cikin tunanin mama ta ƙarayimin magana na tashi na fita Yaya Bilak na hango ya wani kame a kujera ya yi ƙyau a cikin jallabiyarsa ƴar asalin larabawa,wata irin kunya ce ta baibaye ko ina na jikina a hankali na isa wajen na gaishesu amman Yaya Bilal ko kallo na baiyi ba.naji babu ɗadi a raina amman ban nuna hakan ko a fuska ba.

Allura ya ce zaiyi min ta kashe zafin ciwo,rau rau na yi da idanuwa kamar zanyi kuka naƙi in tsaya ayimin wata uwar tsawa yaya Bilal ya yi min jikina yana kakkarwa na tsaya akayimin ina kuka.tsaki naji yaja sannan ya yi ficewarsa tare da ce wa"dr maher ka sameni a waje".da to ya amsa likitan ya kalleni sosai ya ce"sannu crazy girl".ban amsa masa ba na cigaba da matsar ƙwalla ta,ya ajjemin magungunan da kuma allurar da ba'a gama min ba.mama ta yi masa godiya ya tafi.

Mama ta ruƙo hannuwa a hankali muka fara tafiya sai ga Hajiya kishiyar mama ta fito daga kitchen ta ce"hmm ayi dai duk a gama wai ke uwarki ta koya miki munafunci ko?to duk kuyi a sannu in dai munafurci ne na iya shi har na dameku ba dai ƴaƴanmu kika ɓatawa suna ba?hmm kijira na ki ɓatancin don kare ma bazai shinshina ba,shegiya ƴar inyamurai kawa".tana faɗar hakan ta yi shigewarta ta barmu anan tsaye tunani ya cika zuciyoyinmu,muka haɗa idanu da mama na bata ce komai ba ta kaini har ɗakina sannan ta bani magani ta tafi.

"Ƴar halak yanzu na je tunaninki?".dariya Rashida ta yi sannan ta ce"Allah sarki Khairat ya jikin na ki?".ɗan murmushi na yi wanda yafi kuka ciwo na ce"da sauƙi Rashida".

"Hmm gaskiya Khairat idan da zaki yarda da kin koma ɓangarenmu sai mu dinga ƙwana tare don ban yarda da zamanki a ɗaki ke kaɗai ba,ni fa waɗannan munafukan har yanzu ban yadda dasu ba,don wallahi zasu iya aikin tumasancinsu a gidannan don haka ni zanje in samu mama in faɗa mata komai".

Ruƙo hannunta na yi na ce"kada kije Rashida kin san halin mama da gudun zuciya ba za ta taɓa yadda ba,don haka ki barta kawai Allah zai kareni daga sharrinsu".taɓe baki Rashida ta yi ta ce"to ni yanzu me zance Allah dai ya tsareki daga sharrinsu".nan muka cigaba da hirarmu.
****

Washe gari da safe har É—aki mama ta kawomin abin kari bakina ya kumbura sosai ta ce"Khairat kafin kici abincin nan sai na gasa miki bakinnan don ya kumbura sosai".mama da kanta ta gasa min bakin muna cikin wannan halin naji muryar hajiya kaka tana ta tujara a babban farlonmu,na kalli mama itama ta kalleni sannan ta ce"kaka ce ki fita ku gaisa".ina shirin tashi sai ga tabta shigo ta ce"wayyo Allah na me zan gani Khairat?kai amman waÉ—annan yara sun cika marasa mutunci,shiyasa yanzu ina shigowa waccen munafukar ta taho wai za ta gaisheni ko kallon iskarta ma banyi ba na yi tahowa ta,shegiya sadakar yalla".

tana ta sababinta bance mata ƙala ba mama ma bata komai ba sai kuwa kaka ta ce"hmm ai ke Khairat sallamammiyar uwa kika samu tunda duk abinda za'ayi miki sai dai ta yi shiru ta yi zugudum kamar buhun lalle".ta harai mama da sauri mama ta fita don zamanta awajen ba alkhairi zai janyo ba don haka ta fita don tsahon shekarun da ta yi da kaka tasan halinta tsaf.

"Ke ba fa zaki zauna a wannan sallamamman sashen na ku ba,ɓangarena zaki koma don na ga aƙwai masu halin awakai a gidanku,don haka ki tashi yanzu yanzu ba sai anjima ba mu tafi don bazan lamunci halin masu laluben mata ƴan uwansu ba,kada Allah ya turo mala'ikunsa su rushe mana gidan duka tunda saɓon Allah ake a gidan".

kallon kaka na yi rau rau da idanu na ce"a'ah ni dai kaka babu inda zanje wannan sashen na ki mutum yaje ki yi ta yimai masifa abu kaÉ—an ki zageni".galala Hajiya kaka ta yi tana kallon Khairat ta ce"eh lalla ai barewa ba tayi gudu É—anta ya yi rarrafe ba eh halin Malik ki ka yi tsaf na taurin kai to wallahi ko zaki yi kashin jini yasin sai kin bini sallamammiya kawai".tana faÉ—ar hakan ta fito.

A farlo suka haÉ—u da Nadiya da iman suna kallo a tv da sauri kaka ta murza idanuwanta ta ce"yo ikon Allah khairatu zo ki ganemin waÉ—annan masu halin mutanen annabi luÉ—i sunyi rashe rashe suna kallo,ko uban waye ya basu damar zama suna kallo?su da sukayi wannan mummunan laifi".

Da sauri su Nadiya suka kalli kaka sukayi wuƙi wuƙi da idanuwansu,don sun san kakarsu aƙwai tonon asiri suka haɗa baki wajen ce wa"hajiya kaka ina wuni".zaro idanu kaka ta yi sannan ta ce"oh ni ina ganin rashin hankali a gidannan ke Nadiya don ubanki sadakar yalla ce ta raɗamin wannan sunan Hajiya?ke kuma imani fulanin daji ce ta raɗamin ko kuwa?".da sauri suka haɗa idanu don mamakin zagin da kaka ta yi musu,ganin mamakin zagin da ta yi musu suke ta ce"to wannan kallon da kuke min munafukai nima ƙwaƙwuleni zakuyi?kamar yadda kuka yi wa ƴar uwarku khairat?to wallahi ahir ɗinku don ni na fi ƙarfin maitarku,kuma bari Malik ɗin ya dawo duk sai an kori masu aikin gidannan ku koma masu yi mana aiki,tunda rashin aikin yi ne yasa kuke saƙule ƴaƴan mutane".

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.