Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 2 of 90

Ranar ɗaurin aure da wuri muka shirya mu ƴan matan gidan duk anƙwan shadda fara mukayi,iyayenmu kuma skye blue,samari kuma arsh sukayi.
Wajen Kaka na shiga ina zuwa naga ta yi baƙi ɗakinta cike da mutane amman maza ma sunfi yawa wasu pan gidanmu wasu ba ƴan gidanmu ba.
Na gaishesu na kama hanya zan fita sai naji kaka na ce wa"ƙwaji shasha Salisu ba yanzu ka gama yimin ƙwatancenta ba?ka ce inya maka iso kana sonta kuma tazo kabarta ta fita,to wallahi ni babu ruwana gwara ma ku sasanta tun yanzu don wallahi na gaji da kallon ƴan matan gidannan yara sunkai talatin duk ƴan mata,wannan ma idan kana da hawan ruwa ai sai ya tashi".

ni dai ranar kunya ta isheni azuciyata na ce kaka kenan É—azu ta gama faÉ—ar munyi kaÉ—an yanzu kuma ta ce wai munyi yawa,kaka kenan babu mai iya mata sai ita.
Shima wanda ta kira da Salisu É—in kunya sosai ce ta kama sa,ya kama rufe fuska,ni kuwa É—an satar kallonsa na yi sam wallahi baiyi min ba ni wallahi ko da ma ace ya yi min ni yaya Bilal na ke so.
Da sauri na yi hanyar sashensu Rashida sai ga Salisu ya biyo ni a baya yana yimin magana,ban iya wulaƙanta ɗan adam arayuwata don haka na juyo muna cikin gaisawa sai ga Yaya Bilal ya fito daga cikin sashensu ya yi bala'in yin ƙyau cikin shaddarsa ruwan arsh,ta zauna sosai a murɗaɗɗan jikinsa mai ƙyau da tsari,kaf gidanmu babu wanda ya yi fari da kuma ƙyau irin na Yaya Bilal shine ya yo asalin kakanmu,kuma Yaya Bilal yana kama da babanmu wato alhaji abdulmalik.
Ayanzu yaya Bilal soja ne yana a matsayin Admiral ana ce masa Admiral Bilal Mohd.in kiyarsa Admiral B.
Gaba ki ɗaya hankalina da nutsuwata duk yana kan Yaya Bilal,Salisu yana ta zuba surutunsa dai daga baya ya gane ce wa hankali na yana wani wajen ba wajensa,mamaki sosai ya ke ganin wanda na ke kalla tabbas idan baiyi ƙarya ba yasan wannan yaya na ne kuma yasan ɗa ne ga yayan mahaifina amman ya aka yi haka na ke ta kallonsa lallai aƙwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin,don ruwa baya tsami banza sosai Salisu yaji haushin wannan lamarin ya juya ya tafi don shi tunda ya ke bai taɓa buɗe bakinsa bama ya ce,yana son wata ƴa mace ba sai akan Khairat amman ta wulaƙanta sa haka.
Anyi bidiri sosai aka saki kiɗa amman iya mata ne kawai ƴan uwan Mama suma sunyi na su al'adun na inyamurai,ashe abin ya zaunawa Kaka a ƙoƙon zuciya ta shige ɗaki ta fara kuka wiwi,ashe lokacin Kishiyar mama na ta ganta wato Hajiya Iklima ta biyo kaka don salon gulma tana tambayar kaka abinda ya faru,haba daman kaka na jiran ƙiris ta ƙara volume ɗin kukanta tana tirje tirje kamar ƴar yarinya ƙarama,ta ce wa mama iklima ta je ta kirawo mata malik da sauran ƳaƳanta.
Duka iyayenmu maza suna babban farlon gidan ana hira ta zumunci,sosai hankalinsu ya tashi maxa goma ɗinnan duk suka taho daman biyu ne mata ƴaƴan kaka goma maza,nan fa kaka ta shiga gaya musu wai tana ji lokacinda aka ce a ƙara volume tunda masifaffiya ta iso.

*Miss green ce*
[23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
---------------

*Arewa book user*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
--------------------

*Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiÉ—a yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala'iku za ta tabbata akanki. --------------------------------

3🟪4

.. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa "umma lafiya me ya faru?".kukan ta ƙara fasawa tana ce wa"yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa".

dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce"Umma ki faÉ—a mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi".

"To matarka ce inya mura ita ce ta ɓata min rai,wai ga masifaffiya nan ta iso,don ubanta gidan inyamurai ne nan da za ta tara mana ƴan bariki suna muskuta ɗuwaiwaka kamar gidan maguxawa?to wallahi ni nagaji xan barmuku gidanku".sai ta fashe da kuka sosai har da majina,Hajiya Iklima ta ce"kaka don Allah ki yi haƙuri ki daina kuka"sai kuwa kaka ta Juyo a fusace ta ce"indai na kuka ko?tunda ba uwarki ce taka kukan ba ai dole ki ce haka?ni tashi ma shi ki barni in yi magana da ƴaƴana bana son bare awajen.

wani malulun baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya iklima ta Kalli fuskar hajiya kaka ta harareta,ita ta rasa wacce irin mata ce ba ta ɗaukar zuga ko kaɗan,amman ta yi alƙawarin muddin tana raye sai ta haɗa Hajiya kaka da dukkanin surukanta ta zama ita ce ta gaban goshi.

Tashi ta yi ta fita tana mai ƙara jin haushin cin fuskar da Hajiya kaka ta yi mata,sai kuwa kaka ta ce"to as dai a fita don bana son ina shawara da ƴaƴa na a zo asakamin idanu irin na fulanin daji".

wannan magana da kaka ta faɗa ba ƙaramin mugun haushi ya bawa Hajiya iklima ba,don tasan sarai da ita take don asalinta fulanin daji ce,don itama kafin ta bari a aurota ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba.

"Umma insha Allsh daga yau Zulaihat ba xa ta ƙara yi miki wani abu da zai ɓata miki rai ba,yanzu ma ba sai anjima ba za ta baki haƙuri",yana faɗar hakan ya yi saurin fita.

Usman autan Hajiya kaka ya ce"gaskiya umma ki daina yi wa wannan baiwar Allahm haka,gaskiya ba a ƙyauta mata wallahi saboda ita ba yaranmu ba ce sai kuma ace za abi a tsaneta".

"ah lallai ƙanin Zulai ka ce kaima an jiƙa an baka,kamar yadda sukayi wa ɗan uwanka a da cen baya,yanzu kuwa Allah ya dawo min da hankalin ɗana jikinsa,yanzu muna nan da kai za kaga caccakar da zai yi musu shegu masu cin arziƙi,tunda suka zo ina kula dasu babu abinda suke sai dafa nama daga an sauke wancen a ɗora wannan,ɗana yana ta kawowa suna cinyewa".

dukkansu shiru sukayi har Alhaji Aliyu wato babban ɗan ta don shima ba'a bar matarsa ba,don haka haƙuri kawai ya iya bawa Hajiya kaka yaja bakinsa ya yi shiru.

A ɗakinsa ta samesa yana kaiwa yana kawowa hannayensa ya rungumesu a baya,sallama ta yi ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa sai ta ji ya ce cikin zafi"Yanzu Xulaihat abinda ki ka yi wa mahaifiyata ya yi miki daɗi kenan? ki tara ƴan uwanki suna zagar min mahaifiya ta to wallahi ba zan lamunta ba,kowa ya haɗa kayansa ya barmin gidana don ba zan lamunci cin fuskar kowaccenku akan mahaifiyata ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.