Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 25 of 90
*Wattpad user name*
Rabiatu333
*Arewabooks*
rabiattu0444
Ya ku Æ´an uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiÉ—anu.
---------------
25🟩26
. .. . ...Kai tsaye ya wuce gidansu captain,yana isa kai tsaye ya shiga gidan,da kansa yazo ya taresa,Halisa matarsa ta fito suka gaisa harda ɗansa ɗaya wanda sunan Bilal ɗin yaci,Bilal kusan shine hope ɗiin captain ya tsaya masa a komai,shi ne ya nemo masa aiki har yau gashi yana a matsayin captain shiyasa ya ke matuƙar girmama Bilal ɗin,don shi a sahon masu arziƙi masu taimako da gudu zai saka Bilal don mutum ne mai tausayi sosai da kuma son talakawa.
Abinci Halisa ta kawo musu,ruwan shayin dai ya kurɓa wanda yasha coffie sosai don shi arayuwarsa yana bala'in son shayi da coffie suna ɗan taɓa hira captain ya ce"ah mutumina ni fa tunda na ke da kai ban taɓa ganin ranar da naga kana magana kana dariya ba,sai dai inga ka yi murmushi,to meye sirrin A.D? Ko dai ka kamu ne kaga wata ƴar geton namu".?
murmushi ya yi sannan ya kurɓi coffie ɗin sannan ya ce"Captain tabbas ka yi gaskiya,don wallahi na ga wata yarinya wacce ta ƙwantamin sosai a zuciyata".
Dariya sosai captain ya yi sannan ya ce"lallai mutumina wannan wata yarinya ce mai sa'a haka?".
"Hmm captain ni ne dai mai sa'ar don Wallahi yarinyar nan cikin mintina ƙalilan naji ina azabar sonta wanda ban ma san lokacin da ya kamani ba".sosau captain ya ke dariya sannan ya ce"ina ma zan haɗa baki da ita da na ce wallahi kada ta yadda".
dariya sosai Bilal ya yi sannan ya ce"hmm kaga oga maganar ma da na ke maka yanzu ai har na kai maganar wajen mahaifinta,kuma yarinya ta yaba don haka sai ka nemi wata hanyar".
har dukan dining table É—in captain ya yi sannan ya ce"shege mutumina sharp shooter kenan,ka ce har ka kai magana daga haÉ—uwa yau"?.
"To zan tsaya ne abuga min ball?ai kai ma kasan ni winner ne akan komai".dariya dukansu sukayi Halisa na ɗaku tana mamakin jin dariyar Bilal haka,duk tsahon tarayyarsu da mijinta bata taɓa ji ya yi dariya ba koda kuwa awaya ne,don mijinta captain yana da ban dariya sosai.
Suna cikin dariyarsu captain ya ce"yauwa A.D ni kuwa ya maganar case É—inka da Alhaji Damas"?.
ɓata rai sosai Bilal ya yi sannan ya ce"captain mutumin nan ya zarce duk inda ba ka tunani,mutum ne mai mummunan hatsari,yanzu fa wai so ya ke adole gidanmu ya zama mallakinsa,kuma duk akan case ɗinmu dashi ne ya janyo hakan,amman ni nasan ta inda zan ɓullo masa idan ya san wata bai san wata ba".
Yana faɗar hakan ya tashi tsaye ya saka hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya ce"ni zan wuce captain Allah ya ƙara sauƙi".
"Haba mutumina har tafiya?ah to tunda dai ka samu Æ´ar geto ai dole ka koma gida da wuri"?.dariya sosai Admiral B ya yi sannan ya sanya kyakkyawan glass É—insa ba tare da ya ce komai ba ya fita.
Har mota captain ya rakosa sannan ya koma gida.
Har yaje gida tunanin jidda kawai ya ke,yana godewa Allah yau ya samu wacce ya ke so muradin ransa.
Sanda ya sako hancin motarsa muma lokacin muka fito daga cikin gidan,ya wani kallemu ya watsar ya wuce abinsa,na haÉ—iye wani irin yawu mai zafi.da zanyi da tuni na cire son yaya Bilal araina amman na kasa,kallonsa na ke har ya fito ya wuce sashensa.
Rashida ta dungureni ta ce"to ya wuce sai ki taho mu tafi?".ta faÉ—i hakan tana hararata,kunya ta kamani muka wuce gaba.
Muna dawowa daga islamiyya kai tsaye na wuce sashen hajiya kaka,ina shiga na tarar da mutane sosai,muna cikin gaisawa sai kuwa hajiya kaka ta ce"inno kin gane wannan kuwa?".
"A'ah gaskiya ban gane taba?kinsan rabona da birni na daɗe tun su khairat suna ƙanana".sai kuwa kaka ta ce"ahaf ai wannan i'ta ce khairat ɗin?".gwalalo idanuwa inno ta yi sannan ta ce"ikon Allah girman ɗan mutum babu wahala yau shekara 17 kenan rabona da garin nan tun sunansu,amman kinga yara sunyi wayo".
ɗan murmushi na yi kawai sai kuwa kaka ta ce"khairat sunzo saukarku ne fa?ga mairo cen don Allah ta zauna a sashenku,tunda ita dai ta dawo nan da zama yanzu,kunga idan tana cikunku za ta ƙara gogewa".kallon wadda aka kira da mero na yi sai kuwa ta ce"hannunki dafatan kina lafiya".nima murmushin na maida mata muka cigaba da hirarmu,na fuskanci mairo aƙwai ƙauyanci sosai akanta.ga ƙiriniya sosai ni kuwa dariya kawai na ke azuciyata don tun yanzu har sun fara faɗa da Hajiya kaka.
****
Su Rashida suna zaune a farlonsu harda mahaifiyarsu sai ga yaya Bilal nan ya shigo,da sauri Su Rashida suka tashi don sunsan karon nasu bai musu ƙyau dashi.
Suna fita hajiya Ruƙayya ta kallesa ta ce lafiya kuwa Bilal".?
Babu abinda ya ɓoye na dangantakarsa da Jidda,har unguwarsu babu abinda ya ɓoye mata.sosai ta yi murna da jin hakan sannan ta ce"to insha Allah kuwa xan gayawa Babanku idan ya dawo,sai ayi bincike sosai don daga jin labarinta mutuniyar kirki ce sai dai yana da ƙyau binciken.
*****
"wallahi khairat atsorace na ke sosai,don gaskiya ni tsoron rikici ne dani ko yaya ya ke?,ni fa har yanzu ban amsawa yaya Aliyu ina sonsa ba?".
kallonta na yi sosai sannan na ce"ke dai kawai ki fito kice min bakya son yaya Aliyu?amman ina ruwanki da anty khadija wanine ya ce kada ta riƙe mijinta da ƙyau".?
Murmushi maryam ta yi sannan ta ce"hmm khairat ko dai ma yaya ne?ai macece Æ´ar uwata nima kuma bazan so hakan ya faru dani ba".ta faÉ—i hakan kamar za ta yi kuka.
"Maryam ni dai don Allah ki taimakeni kiso yaya Aliyu,don wallahi ina jin tausayinsa wannan auren da zaiyu shine zai kawo solution ga dukkanin matsalolin da suke faruwa tsakanin yaya Aliyu da anty khadija".
"Khairat bari in fito miki a mutum sosai kinga nan na daɗe inason yaya Aliyu amman ban taɓa nunawa kowa ba,sai dai in shiga ɗaki inyi kuka idan abin ya dameni,amman duk da haka ina jin tsoron abinda zai faru khairat?kin san ku ƴan uwane ni kuma bare ce acikinku to kinga aure na da yaya Aliyu zai iya kawo matsala tsakanina dashi."
"Babu wata matsala da zai kawo?".da sauri muka ɗaga idanuwanmu Rashida ce tsaye akanmu tana murmushi ta samu waje ta zauna ta ce"Maryam haƙiƙa na jima ina jiran wannan ranar tazo da wani ɗan gidanmu zai aure ki maryam,kina da tarbiyya sosai da kuma nasaba mai ƙyau babu namijin da zaiso ya auri macen da take da hali irin na anty khadija.tunda har ya buɗe bakinsa ya ce yana sonki don Allah kada ki bawa maraɗa kunya ki yadda musha biki".ta faɗi hakan tana dariya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.