Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 43 of 90
Na yi mamakin Ahmad sosai kamar bai san daɗin kuɗi ba?irin wannan zubar da kuɗi haka?nan dai mama ta sakani agaba na shiga banɗaki ta zubamin wani abu mai ƙamshi acikin ruwan,na shiga na yi wanka ƙamshi duk ya baɗe ɗakin,ina fitowa ta bani wata zuma mai kauri tace insha,babu musu na ɗaga kaina nasha,sannan ta bani wasu abubuwan ta koyamin yadda zanyi amfani dasu koda bayan aure idan ina da buƙata.
Yadda ake haÉ—a zumar mata.
*Zuma*
*citta*
*kanunfari*
*minanas*
*RiÉ—i*
*sassaƙen ɓaure*
*sassaƙen gamji*
*ƙwaƙwa*
Ki samu zumarki mai ƙyau,sai ki samu sassaƙen ɓaure amman bayan kin dakashi ya yi luƙui kin tankaɗeshi,sai ki ɗora zumar akan wuta kiɗan ƙara ruwa kaɗan,sai ki zuba garin minanas da kuma garin ɓauren da kika daka,sai gamji shima kamar garin ɓaure,chokali biyu biyu zaji zuba,ya danganta da yawan zumarki don ba'a son ya cika kauri da yawa,sai ki zuba garin citta,da kuma garin kanumfari,sai kiɗan soya ƙwaƙwa daban daman kun riga da kin soyata ƙananu sai ki zuba aciki,riɗinki ma ki zuba bayan kin wankeshi kin busar dashi sosai.sai ki rage wuta kina juyawa kaɗan kaɗan,shi wannan haɗin ba'a son ki cika masa wuta.
Za kiji yana ƙamshi to alamar ya yi kenan,sai ki sauke ki samu ƙwalbarki mai ƙyau ki zuba aciki,ki dinga shan chokali 2 da safe biyu da yamma.
Hmm ni dai bazance komai ba,sai an gwada akan san na ƙwarai.
*****
"Ai Bilal ba sai ka nunamin ce wa baka son yarinyar nan ba?ƙarfe nawa yanzu?ɗaga kanka ka duba agogo?".a hankali ya ɗaga kansa ya duba agogon ƙarfe 10 na dare,ya sauke kansa sannan ya ce"kai Hajiya kaka gaskiya kina takuramin wallahi,yanzu me ki ke son inyi miki?".
sheƙeƙe ta kallesa sannan ta ce"ungo Ruƙayya zaka yi min"?.ta faɗi hakan tana harararshi,ga dai mata nan ka bari agidanku ka ƙi ka kawo motocin da za'a kaita gidanka,mero wacce zata zauna agidannan tun biyar akazo aka ɗauketa,amman kai shine zaka gaya min maganar banza ko"?.
"Haba grany!ba fa ita kaÉ—ai ce matata ba,ga Jidda nan,amman ita babu wanda ya damu,sai ita Æ´ar gwal,kuma ni zanje in É—auko jidda da kaina,ita kuma xan aiko azo a É—auketa,shikkenan?".
Ya faÉ—i hakan yana É—agawa Hajiya kaka gira,ta ce"ai wallahi kuwa baka isa ba Bilal,wato ma har ka ke cemin ita wannan figigiyar matar taka kai za kaje ka É—akkota,ita kuma wannan za'ka aiko a É—auketa ko?to ban yarda ba,sai dai ita ka tura a É—akkota wallahi,kuma ni zan kaita har É—akinta".
Ta faɗi hakan tana shiga ɓangarenta,daman mama ta sakani na canja kayana,wata haɗaɗɗiyar lifaya mai ƙyau,fara ƙal da ratsin kore na yafa ta har kaina na rufe ruf,hajiya kaka ta janyo hannuna mama tana ta rarrashina,muka fito waje.
Yana tsaye inda kaka ta barsa,ya hangota ya juya kai abinsa,azuciyarsa yana ce wa yarinyar da aka haifeta agabana na raineta sannan yanzu acw wai ita ce matata?wannan ma ai janyowa mutum raini ne.ya shiga cikin motar ya tayar da ita abaya muka zauna nida hajiya kaka,sai Æ´ar uwar mamana guda É—aya.
Karatun qur'anine ke tashi acikin motar,ga ƙamshin freshner ya cika motar mai sanyin daɗi,har mukaje kuka na ke,duk haushi ya cika sa a fili ya ce"wannan ai dole mutum yasha pain reliep".Hajiya kaka na jinsa ta hararesa ta baya.
Abakin kyakkyawan ɓangare na aka saukeni,ɓangare uku ne agidan,ɗaya nawa,ɗaya na jidda ɗaya na me gidan,ɓangare na ya yi kyau sosai,ko sisin mahaifina babu aciki Baba Abdullahi shi ya yi rawa ya yi tsaki,kayan da aka sakamin ko su Rashida dasu ke matsayin ƴaƴansa bai yi musu shi ba.har kayan kitchen bawan Allahn nan shine ya yi,ya bawa ƙannansa su Aisha suka siyo masu matuƙar kyau.
Koda zamu shiga sashen nawa hajiya kaka ta ce"ki yi bismillah kafin ki shiga Allah ya kareki daga sharrin duk wani mai sharri".
Da ƙafar dama na shiga gabana yana dukan uku uku,shikkenan ta faru ta ƙare yau dai Allah ya kawoni gidan da za'a gasa ni kamar yadda na nema,jikina duk ya yi sanyi sosai.
Sai asannan aka dinga kawo mutane aka cika gida ɓam,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,don ta kirasa amman bai gani ba wayarsa na silent,sai sannan ya duba ya gani,tuni jidda tafi awa agidan,don Babanta ya ce akawo ta tunda masu ɗaukarta basu zo ba,a sabuwar motar Jidda ɗin aka kawota,sabuwa dal sai sheƙi take.
Shigowar saƙo wayarsa ne yasa ya duba alokacin yana shirin zuwa ya ɗauko jidda,da sauri ya kalli sashen jidda ɗin sannan ya kalli wajen motocin gidan,sosai abin ya basa mamaki me yasa bata jira yazo da kansa ya ɗauketa ba,wani kishi ya tokare masa ƙirjinsa,yanzu haka wasu mazan duk sun kalle masa matarsa.
Kai tsaye sai da ya fara shiga sashensa ya ajje wasu abubuwan sannan ya shiga wajen jiddarsa,yana shiga ɗakin na ta ya hangota kan gadonta babu ko lulluɓin idanuwanta sun kumbura saboda kuka,ta fara harararsa,ya matso inda take ya kalleta sannan ya ce"haba my jidda ki yi min uzuri don Allah". . .
tun kafin ya ƙarasa ta ce"don Allah kada ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya,idan banda rashin adalci shine ita kaje ka ɗaukota ni kuma ka barni ni kaɗai ko?wannan shine alƙawarin da ka ce za kayi min?".
riƙe hannayenta ya yi wanda suka sha lalle ya ce"jidda kece matar da na keso,ta yaya ki ke tunanin rashin adalci daga wajena?ko kaɗan bazan taɓa haɗaki da wata mace ba,u are my one and only".ya faɗi hakan yana sumbatar goshinta,tuni ta washe bakinta don arayuwarta tana matuƙar son Bilal,amman idan ta tuno da wani abu sai taji duk ranta ya yi masifar ɓaci.
Ina rungume ƙirjin Hajiya kaka sai rarrashina take,Rashida ta ce"hmm wallahi Hajiya kaka duk kinfi son khairat, ni fa har yanzu ko gida na ma bako sani ba".ta faɗi hakan cikin shagwaɓa.
Sai kuwa Hajiya kaka ta ce"Allah sarki dukkanku ina sonku amman a gaskiya ita khairat ina tausayinta ne sosai,sam ita bata ƙwatar kanta kamar yadda ku keyi,haƙurinta ya yi yawa gaskiya,shiyasa na ke tausayinta balle yanzu kuma za ta zauna da wannan miskilin sai yadda hali ya yi.to wallahi daman ina faɗa miki duk abinda ya yi miki ki rama,kada ki zauna kina wani jin kunyarsa yasa miki hawan ruwa ya barki anan."
Hajiya inna wadda zuwanta kenan ta ce"khairat ki ka biyewa Ramatu kaiki za tayi ta baro,don haka ki yiwa mijinki biyayya iya bakin iyawa,yi na yi bari na bari kinji".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.