Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 80 of 90
Sosai ya ke kallo na da mayun idanuwansa masu mugun tafiya dani,ganin hakan yasa na kallesa kallon cikin ido na hararesa murmushi ya yi min yana huromin iska,ni kuwa na saka hannuwa na biyu na kama iskar na saka dai dai zuciyata.tuni abokansa suka saka dariya ashe duk sunga abinda ke faruwa,kunya duk ta isheni shi kuwa ko ajikinsa.
Anyi mana kyawawan hotuna masu matuƙar kyau ni ina kusa da Shahid ya saƙalo hannunsa ni kuma na riƙe nasa.sai Zainab dasu Amira suna kusa dani,shi kuma abokansa suna kusa dashi,sosai hotunan suka yi kyau,abokan Shahid sai tsiya suke masa wai ya yi musu wayo ya samo baƙar fara me kyau.
Dai dai nan Yaya Bilal suka shigo da goron ɗaurin aure da su Baba usman,ganin hakan yasa Baba Usman ya ce su ƙarasa ayi hotunan dasu.Bilal kamar ya nitse a ƙasa saboda takaici da baƙin ciki,da farko ance ya zama waliyyi ya yarda,kuma yanzu ace wai za'a ɗauki hoto?tuni yaji zuciyara babu daɗi ya goge wata ƙwallar da ta taru a idonsa.hango khairat da Shahid suna ta dariyarsu abinsu,basu da wata damuwa ko kaɗan.
haushi da kuma nadamar dawowarsa nigeria suka kasa hallaka sa.babu yadda ya iya haka ya shiga aka yi hoton dashi,da sauri ya yi hanyar ɓangarensu,sai gasu haidar sun taho sun ƙara cin kwalliyarsu da shadda ruwan ash irinta babansu.
suka riƙe hannunsa irfan ya ce"dady jo muje ayi mana oto da mamanmu".ya faɗi hakan cikin shagwaɓa shi daman bai da magani ko kaɗan iri babanshi,wata irin harara na ɓallawa irfan na yi wuce wata sashenmu tunda su shahid sun tafi.
Yana ganin na wuce sai gashi ya biyo ni ya ce"mamy don Allah kixo a É—aukemu oto da dadynmu".?banza na yi masa kamar ban san me ya ke ce wa ba,sai kuwa ya fara kuka yana ce wa"momy me yasa bakya son dadynmu?nima idan baki sonshi nima bana sonki".
Da sauri na kalli yaron na ce"get out of my room,mara kunyar banza irfan shekararka nawa yanzu just 3 years shine ka ke faÉ—amun haka?to ka daina sona É—in mana".na faÉ—i hakan cikin fushi Duk Rashida najin abinda na ke faÉ—a É—akin kowa ya yi shiru babu bakin magana.
Rashida ta kamo hannunsa ta fito dashi waje,itama duk ranta a ɓace,nima suna fita na taso na koma ɗakin mama na faɗa kan gadonta na saki kuka,kamar ƙaramar yarinya sosai na ke kuka,mama ta shigo ta ce"subhanalillahi Khairat me ya faru kuma?wani abin ne ya faru?."
Duk alokaci ɗaya ta yimin wannan tambayar,babu abinda ba ɓoyewa mama na abinda ya faru tsakanina da ɗana irfan.na ƙara da ce wa"mama wallahi Bilal ke zugamin yara,yanxu meye amfanin abinda yaron nan ya yimin kamar ba mahaifiyarsa ba?yanzu nan gaba yana son yara na suji tausayi na?".na faɗi hakan ina kuka.
Sosai mama ke rarrashi na,ta haɗamin ruwa me ɗan ɗumi a banɗaki na shiga wanka ta ɗakkomin kayan da zan saka ina fitowa na shafe jiki na da mai lotion me ƙamshi da sanyin ƙamshi,banyi wata ƙwalliya ba na shafa hoda da ƙwalli da lipstick na zauna na yi ɗauri na me hawa-hawa,na yi kyau sosai atamfa ce amman super ƴar ubansu,ta ajin ƙarshs na yi kyau sosai,mama ta dinga yimin nasiha sannan na fito na shiga sashen babanmu.
Anty halisa ina zuwa na tarar tazo ta ce"amaryar balarabe tunda nazo na ke ta jiranki amman shiru?ko dai angon ne ya ɓoye mana ke"?.ta faɗi hakan tana murmushi.na ce"wallahi kai na ke yimin ciwo amman yanzu da sauƙi."
Sannu ta yimin anan take tsokanata wai na yi mugun kyau kamar wata acikin zarah.murmushi kawai na yi na zauna duk jikina ya yi sanyi saboda abinda irfan ya faÉ—a min.
Sosai na ƙaru da nasihar da anty halisa ta yimin.tare da bani wasu sirrika na musamman,sannan ta bani dubu ɗari wai inji captain Ahmad,ita kuma ta kawomin wasu manyan followers masu shegen kyau.wanda kuɗinsu ya haura dubu hamsin ma da kuma wani flask ne gudu baƙwai me mugun kyau.abin dai gwanin sha'awa su Rashida dasu maryam ma kowanne ya kawomin gudun mawarsa dai dai gwargwado.
Daman shahid yace su al'adarsu ba'a yi wa mace kayan É—aki miji ke yi wa mace komai.babu yadda baba na baiyi ba akan akawo min kaya amman ya ce a'a su abin kunya ne ayiwa mace kayan É—aki daga gidansu.don haka shi za yi ba komai.
Amman nasai kayan kitchen masu natuƙar yawa.da kuma tsada abin dai sai wanda ya gani.
Shahid da kansa yazo da yamma ɗaukar amaryarsa khairat.kamar su haidar sun sani suka maƙal ƙale ni.amman abinda ya bani mamaki kuma ya ƙonamin rai shine bai wuce yadda irfan ya yi banza dani ba.ƙarshe ma ya koma wajen mahaifinsa.na lura yaron yana masifar son mahaifinsa fiye dani.su kuwa sauran sunfi sona don duk inda na ke zaka gansu.
Hajiya kaka ta shigo sashenmu da kanta tana sababi wai tun ɗazu ƴan kai amarya har sun fara ɗaukar mutane amman ni ban fito ba?samu na ta yi ina ta kuka kamar za'a kai ni gidan maƙiyi na.
*Sirrinki***
9)-KARIN GIRMAN NONO
wasu matan wanda daga sunyi haifuwa daya zakaga nononsu ya zuba wannan yana saka me gida yayi miki kishiya Ki samu ,h/sauda,hulba,alkama,gyada,ridi, danyar shinkafa da busassen karas duk ki dakasu waje daya kina sha da madara peak Awa 2 kafin barci da kuma Awa 2 bayan barci…
10)-KAMMALA JININ HAILA KIDAWO DAI DAI
Kisamu zuma da garin tagargade da almuskibayan kin gama wanakan tsarki saiki debo garin tagargajen ki dama acikin ruwa ki wanke gabanki dashi saiki dangwalo zuma ki rinka sakawa acikin farjinki sai ki bari idan dare yayi saiki dauko farin almuski ki kara shafawa acikin farjinki sannan ki jira dare yayi zakiga yanda mai gida zaiyi…SMILINGÂ
11)-BAKYA IYA GAMSARDA MIJINKI
Kisamu furen tunfafiya da yayan zogale da gero ki dakasu lukui sannan kirinka sha dafresh madara daga ranar zaki fara gamsarda mijinki har sai ya gaji da kansa.
12-MATSI DA SANTSI
Idan kinaso mijinki yarinka jinki cikakkiyar mace kisamu Lalle mai kyau ki kwabashi ki hada da zuma ki saka farjinki sai ki samuman zaitun da Baby oil ki dauko auduga ki rinka dangwalowa kina sakawa a farjinki wannan shine asalin matsi mai saka mai gida kyauta bayan haka sai kisamu kankana ki markadata ki hada da madara peak wannan shine zaki zama mai dadin jima i..
13)-RAGE GIRMAN mama
Samu Ganyen Lemon zaqi, Buhuru sudanyiya.Ki hada ki dakasu ki dinga shafawa a nonon zai Ragu amma ki rage shan madara Ki dinga soya hanta da kitsen akuya
kina ci zasu ragu.
14)-SAURIN KAWOWA MANIYI
Maza da dama suna bukatar jimawa awajen jima'i, amma hakan baya samuwa saboda daga sunfara jima'i, zasuyi relax to ka gwada wannan kasamu garin h/sauda cokali daya
Sai kasamu kwai guda uku sannan ka hadasu ka soya kada ka bari ya soyu sosai insha allah za adace..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.