Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 21 of 90

ta dawo tana haki na ce"ke kuwa hajiya kaka me ya kaiki dukan nadiya ai jikinki sai ya yi ciwo,kinga yadda take fa kamar wata ingausa".kaka ta ce"yo ƴar nema ai ta saba da shaƙe ƴaƴan mutane ai dole ta munmurɗe haka,ni dai Allah ya karemin jikana kada wataran ra murɗeshi shima".dariya kawai na saka awajen don hajiya kaka ba dai abin dariya ba,muna cikin haka wayata ta fara ƙara na ɗaga da sallama ta.

"Maryam ykk y ƙwana biyu"?.ina jiyo dariyarta ta ce"ke khairat bar wannab zancen wai yau sai ga yaya Aliyu a gidanmu?".

*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*miss green ce👉🏼*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚*

📃Littafi na 1

By🪶
*®️Ummu maher(Miss green)🍏*

_*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_

*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------

masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.

*Sirrinmu*

yawan barin jikinmu awaje shine ya ke saka miyagu shiga jikinmu da kuma rashin addu'ah,Allah yasa mu dace baki É—aya.
-------------------

19🟨20

. ..dukkaninsu kallon Hajiya kaka suke ta ce"to me ye kuma akr kallona kamar na faÉ—i ba dai dai ba?shi fa Damas É—innan É—an shege ne ma bashi da uba,asalinsu arnan daji ne tun kakarsa ta wajen uwa,uban dai nasa ne ba'asan inda ya ke ba".ta faÉ—i hakan tana kallonsu.tabbas haka ne mahafiyarsu ta faÉ—i gaskiya sai dai mutuminne yana da hatsari sosai.

Wanene Alhaji Damas?

Adamu shine asalin sunansa nahaifiyarsa kuma Sadiya sunanta,asalin Damas ɗin sunansa ya haɗa dana mahaifiyarsa,ya taso da sonta sosai sai dai baiyi rayuwa da ita mai tsayi ba,aka shigo har cikin gida aka kasheta kisan wulaƙanci,sai dai ba kowane ya janyo mata wannan kisan wulaƙancin ba sai ɗanta Damas faɗa ne ya haɗashi da wasu miyagun mutane kuma ya cucesu akan harkar don haka suka ɗauki wannan mummunan matakin,don mutane ne marasa imani sosai tun daga mutuwar mahaifiyarsa shikkenan wani rashin imani yazo mai,kashe mutum awajensa ba kimai bane,kowa yasan yadda arnan daji ke da asiri,don ma a haka mahaifiyarsa ta musulunta kafin ta mutu shine ma yasa ta dawo cikin gari taje zaune gidan haya,tana ƴar sana'ar mai da ƙuli ƙuli dashi take samu take ciyar da ƴaƴanta,yaranta biyu mace dana miji,Ruƙayya da Adam Ruƙayya ita ce ƙarama sai Adam saɓanin Adam bashi da uba,ita kuma Ruƙayya taba da uba,shi Adam tun a garinsu ta haifesa ita kuma Ruƙayya sai bayan ta shigo birni ne ta yi auren ta haifeta auren ma kuma ya mutu.

Bayan mutuwar mahaifiyarsa ya taso cikin ƙuncin rayuwa shi ya ke zuwa ya samowa ƙanwarsa abinci ta kowacce irin hanya haka ya ke zuwa ya samo ya kawo mata,Ruƙayya ta kasance mai ƙyamar mahaifinta ako da yaushe,don wataranma idan ya kawo mata abincin bata ci don tasan ta hanyar daya samo.

Tun abin na Adam bai yi nisa ba har ya yi nisa,babu irin aikin da ba ya yi,shine safarar miyagun abubuwa daga ƙasar nan zuwa wata ƙasar,shine safarar mata daga waccen jaha zuwa wannan kai har ya zama har ƙasar waje,sai a ɗauki yara dag nan ace za'a fita dasu birni aiki amman kuma daga haka bazaka ƙara ganin ɗanka ba,shikkenan kunyi bye bye.

Ganin haka yasa ƙanwarsa Ruƙayya guduwa garin mahaifinta tunda tasan garin,Adam ya yi baƙin cikin barin ƙanwarsa gida don yana sonta sosai,kai tsaye shima yabar unguwar don daman saboda ƙanwarsa ya zauna agidan,don ya yi da ita ta koma gidansa daya ƙera taƙi yadda dole ya ƙyaleta ya cigaba da miyagun aikinsa,aka daina jin ɗuriyarsa a unguwar don daman suma ya fara isarsu,ko da idan ya yi wani kaifin ka kaishi wajen ɗan sanda to fa washe gari za'a sakosa don ya samu masu goya masa baya cikin manyan masu kuɗi na ƙasa baki ɗaya.Ga shi da mugun asiri don ko biyosa akayi ba'a samunsa saboda ɓacewa ya ke.

Wannan shine taƙaitaccen tarihin Alhaji damas.
****

daga zuwa na gidan Anty Khadija gidan ya koma gidan amarya sak saboda tsafta ina tashi da safe babu abinda na ke farawa da na yi sallah na yi azkhar da karatun alqur'ani to ajjewa na ke in fita in gyara gidan tsaf ɗakinta kuma sai bayan ta tashi na ke gyarawa,sannan inyi girki inyi wanka sai dai matar gidan ta fito taci ta koma tana yimin sannu,ni kuwa har mamakinta na ke,wata shegiyar rigar bacci tun ranar da nazo gidan na sameta da ita kusan sati biyu har yanzu bata wanketa ba,kuma me wanke yana zuwa wai sai ta ce mai ya tagi bata da wanki,kuma ga kuɗin me wankin anbata amman tana baƙin cikin fitar da kuɗin,ko da daman yaya Aliyu yasan halinta sai da ya siyo komai na kayan da ake buƙata komai da komai har nama sai da ya saka a fridge don shegen son kuɗine da ita.

Ko da nazo gidan har nan yaya mk ya ke biyoni yazo ya tafi ya barni da tunanin waninsa yaya Bilal don nifa babu namijin da ke cikin ƙwaƙwalwarnan tawa idan ba shi ba,ko da na yi tunanin ciresa araina bai taɓa ciruwa.sam ko kaɗan bana son yaya mk har tausayi ya ke bani yadda duk ya matu akaina,bana son nuna masa bana sonsa ne saboda halinda zai shiga ina dai lallaɓasa ne dai mu rabu lafiya.

Babu yadda baiyi dani ba da in amshi wayar daya kawomin naƙi amsa saboda Baba ya ce baza a bamu waya yanzu ba,haka ya koma da abarsa sai dai tun a fuska naga bai ji daɗi ba don fuskarsa ta canja,na lallaɓashi na bashi haƙuri.muna rabuwa na dawo cikin gidan na sameta tana cin abinci,daman aikin kensn taci abinci ta ƙoshi shine aikinta babu abinda take sai bacci,sai kuwa ta juyo ta ce"wai ni Khairat in tambayeki?"da sauri na ce"ina jin ki anty khadija".

Gyara zamanta ta yi sannan ta ce"wai da gaske yaya mk sonki ya ke"?.ta jeho mun wannan tambayar alokacin da ban shirya ba na ce"eh sona ya ke".na bata amsa nima sai kuwa ta ce"kai Æ´an gidan mu ma sai abarsu Bara'atu fa baki ga yadda take sonshi ba,kuma wallahi har soyayya suke amman shine ya komo wajenki?amman ya cika mayaudari".ta faÉ—i hakan tana kallona.
ɗan murmushi na yi sannan na ce"to ni yanzu Anty khadija meye na wa a ciki?ina shi ya ce yana sona ko?kinga ba ni na ce ina sonsa ba kinga ai ta ƙwana gidan sauƙi ko?soyayyarsu kuma da suke yi da Bara'atu su cigaba da yin soyayyarsu ko kada su cigaba wallahi ba damuna zaiyi ba".ina faɗar hakan na tashi na shige kitchen dan ɗora girki don ni ko san hirar yaya mk ɗinma bana son ayi,ni dai ba ni na ce ina sonsa ba?hasalima ni bana sonsa wallahi ni da zai auri Bara'atu wallahi daɗi xanji don sam bana son in koma gida ya cigaba da zuwa wajena a matsayin saurayi sam bana son hakan,wata dabara ce ta faɗomin na fito na samu Anty khadija har ta fara chat ita da yaya Aliyu sai shagwaɓe mai take wai ya dawo,ni dariya ma abin ya bani da kuma kunya bayan sun gama ne na ce"yauwa Anty khadija don Allah magana na ke son muyi".kallona ta yi sannan ta ce"to ina jinki ya aka yi"?.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.