Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 69 of 90

sosai abin ya bawa su Baba dariya,yaya Aliyu ya ce"caƁƁijan ki ce nima in Ƙaro kuƊin da na ke Baki ko?".da sauri ta ce"ai kuwa dai don Ƙanwarka rumbu ce yanzu,shima Bilalu bari yazo sai ya dinga ajjemin kayan abinci buhu buhu".dariya muke ta yi hardani Ɗin amman tana ce wa Bilalu sai naji duk zuciyata ta yi Ƙunci.

Baba ya ce mu shirya zamuje duba Baba Abdullahi daga nan sai a duba lafiya ta,haka kuwa aka yi doguwar riga na saka buba me buƊewa saboda yanzu duk kayana sunyi min kaƊan sosai,ai kuwa ciki na ya Ƙara tsini sosai,hijabi na saka har Ƙasa,ruwan coffie wanda ya haskani sosai,daman gashi na yi mugun fari.

muna fitowa hajiya RuƘayya ma ta fito har da Bilal,ya hangoni naga yana yimi kallon tsaf,murna fal zuciyarsa yadda yaga khairat na tafiya da Ƙer sai abin ya basa tausayi sosai,yana so ya taimaka mata amman kuma yana tsoron abinda zai biyo baya,motar yaya Aliyu muka shiga da ya ke jip ce,kusan mazaunanta 14 ne,hajiya RuƘayya sai wani nan nan take dani,ni dai kallon kowa kawai na ke,nidai hankalina yanzu yana kan cikina in haihu lafiya in basu Ɗansu don ni yanzu hankalina ya koma kan karatuna don ma su zainab na taya ni wasu abubuwan .

jikin Baba Abdullahi ya yi sauƘi sosai don ranar ma yana zaune ana ta hirar yadda abin ya faru,yaya Aliyu ya ce"kai gaskiya Ƙasar nan tamu aƘwai gyara,yanzu fa babu yadda za'ayi ace gwamnati bata san abinda damas ya ke ba,amman anyi shiru an zuba masa ido,yana Ɗibar yaran mutane kamar awakai".wani tunani ne ya faƊomin azuciyata na ce to Allah ya cika min burina,amman tabbas ina son kawo Ƙarshen zaluncin damass.

hajiya kaka na ganin duk an taru ta ce"yauwa Bilalu riƘe jakar khairat ka rakata Ɓangaren masu ciki don a binciki lafiyarta".ai kuwa da sauri ya ce"to. . .to kaka bari in rakata".ya faɗi hakan cikin zumuɗi.

Wata muguwar harara na banka masa.sai kuwa ya kannemin ido ɗaya.jikina ya yi wani irin sanyi da kallon idansa dana yi.na murguɗa baki muka fita.sauri na ke don bana son mu haɗa hanya.amman kawai sai ganinshi na yi kusa dani yana dariya.sosai na yadda na ke tafiya na riƙe bayana da hannuna ɗaya.ga ciki kamar tulu sosai dariyarsa ƙular dani na ce"kaga mlm don Allah ka koma.ko kuma in saka ihu ince ban sanka ba".dariya ya yi yana riƙo hannu na.naji wani mugun shork da sauri na cire hannuna daga nasa na ce"bawan Allah an gaya maka ni ban san addini na bane kome?ka sakeni saki har uku irin sakin jahilci sannan yanzu kace zaka riƙe hannuna".?

Sosai yaji zafin kiransa jahila dana yi,amman bai nuna min ko a fuska ba amman tun daga nan bai ƙara magana ba har mukazo wajen ɓangaren masu ciki, aka yi sa'a babu mutane sosai na shiga na samu wata likita itace ta yimin awo.ta ce congrat lafiyar klau babynki amman yanzu 7month cikin ko?".mamaki sosai abin ya bani na ce"eh".ta ce"ok ki dawo nan da sati biyu".na amsa mata da "to".

Ina fitowa naga yaya Bilal riƙe da jaka ta abin tausayi.ban kulasa ba na fara tafiya abina sai kuwa ya ce"uwar biyu me suka ce miki"?.wata muguwar harara na watsa mishi kuma naƙi yin magana.ta kaddar daya gani a hannuna ita ya warce ya fara karantawa.wata ƙwallace ta fara zubo masa ya ce"Allah sarki Baby na ka kusa zuwa duniya.Allah ya bawa mamanka haƙuri ta dawo gareni mu cigaba da zaman aurenmu cikin so da ƙaunar juna.

Wani kallo na yi masa sannan na ce"hmm Allah ya kiya ye".ina faɗar haka na yi gaba abina.har na koma wajensu kaka banga ya dawo ba cen sai gashi ya dawo da wata ƙatuwar leda guda biyu.ya miƙomin guda ɗaya ya ce"wannan maganinki ne aciki kisha akan lokaci".ganin da mutane awajen yasa na amsa har da godiyata amman araina ce wa na yi to wa yasa ka?.

*********

Sosai su jidda suke shan wahala don an gano ita yarinyar Alhaji Damas ce.ta yi wani iri da ita kamar tsohuwa duk ta yanƙwane abin tausayi.babu wanka babu wanki Jidda ƴar gayu amman yanzu babu gayu,don axabar da take sha ma addu'ah take Allah ya karɓi ranta ta huta.

Tunda wannan abin ya faru Alhaji Damass yabar Nigeria zuwa ƙasar Germany.don ya tsorata da abubuwa da yawa musamman ma da ƴan jarida suka fara cika masa gida,gashi kuma an gano shine ya ke ɗauke yara,gashi yaji labarin an kama Jidda.

Yana son dawowa nigeria,saboda yana son ya aiwatar da wani aiki.don gani ya ke kamar idan yabar jidda araye aƙwau babbar matsala arayuwarsa.gudun kada ta tona masa asiri.

*********

*Bayan wata2*

To kwanaki na ta tafiya watanni na ta shuɗewa,kullum Yaya Bilal yana gidanmu musamman ma ɓangaren Hajiya kaka.naci da son in kulasa sai ya yi ta hillata ta,amman ko ɓangarensa ban kalla duk wasu abuwan more rayuwa na samu don kullum da kalar abinda zai kawo min,kayan haihuwa kuwa ɗaki guda ya ware na kusa da hajiya kaka ya ke ta zuba kaya.

Ayanzu ya yi tafiya baya nan,ranar da zaiyi tafiya ya daɗe sashen Hajiya kaka don in kulasa.hajiya kaka sai biye masa take kamar ba ita ce ta yimin alƙawarin taya ni ƙwatar ƴan cina ba.sai biye masa take musamman ma idan ta ganshi da ƴan kuɗi.

Ranar dana ga zai takuramin sashen maman Arman naje,ai kuwa sai hira muke itama ta haihu sati ɗaya kenan da suna.haka kuwa ya haƙura ya tafi amman shi kaɗai yasn yadda ya kejin zuciyarsa,don gani ya ke kamar da bason khairat ya ke ba.yanzu ne ya ke sonta.gani ya ke kamar yanzu khairat ta tsanesa.indai ya tuno da wannan sai yaji duk zuciyarsa ta yi masa zafi.

Ina dawowa na iske ya tafi na ajje mayafina zuciyata fess.na hangi abincin da aka kawomin Hajiya Ruƙayya ce ta kawomin,haka yanzu bata gajiya kullum tana hidima ta kullum hankalinta na kaina.nima ina zuwa ɓangarensu musamman da yanzu Aisha ke gida ƙanwar Bilal ɗin yayar Rashida wacce ta haihu amman c.s ne saboda haihuwar tazo da matsala ƴaƴanta 4 yanzu.

Da ƙer na samu na zauna saboda yadda cikin ya yi mugun girma ga nauyi.na samu na zauna Hajiya kaka ta ce"lafiya dai ko?don ni tsoro ki ke bani tunda cikin ki ya tsufa.ni tunda na ke ban taɓa ganin ciki me girma irin naki ba tubarkalla".banza na yi mata saboda yadda cikina ke ya mutsamin.marata zuwa bayana duk sun ƙage saboda azaba.na fara yarfe hannu ina addu'ah.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.