Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 58 of 90
sai da ya daƊe acikin wannsn halin yana kiran sunan Allah sannan ya fara samun karsashi ajikinsa,ya Ƙaraso inda khairat ke Ƙwance cikin Ƙwanciyar hankali,daya duba kan gadon harda Ɗigon maniyyi ajiki,ya rintse idanuwansa yana jin wani irin mugun zafin zuciya,da Ƙarfi ya fara tashinta,yana kallon fuskarta yana ji adadin tsanarta na Ƙara huda zuciyarsa,ya buƊe muryarsa kamar yaro ya Ƙwala wani irin ihu wanda ya yi sabadiyyar tashin khairat a bacci,ta tashi a matuƘar raza ne,tana rarraba idanuwa ta hangosa a gefenta ya kifa kansa yana kuka kamar Ƙaramin yaro.
da sauri ta tashi ta matso inda ya ke ta ce"Hubby lafiya kuwa ka ke irin wannan kukan?waye ya mutu kuma?don Allah ka Ɗago ka faƊamin".ta saka hannayenta da niyyar Ɗago sa Ɗin,da wani irin zafin nama ya wancakalar da ita gefe,na bugi da jikin bango,na fasa Ƙara saboda axabar dana ji,ga hannun da ya yi mugun buguwa,amman duk da haka na Ƙara tashi cikin tashin hankali,tuni idanuwa sun cika da zafin azabar dana ji na buƊe baki na zanyi magana,da sauri ya ce.
"Ke fasiƘa macuciya,Ƴar akuya kada kice har kina da wani bakin yin munafurcin da ki ka saba,ki sani ce wa ayau babu abinda zaki faƊamin ki yi nasara akai na kamar yadda ki ka saba yi,wallahi khairat na tsaneki tsana mafi muni arayuwata,kin cuceni kuma kin cuci kanki,da aure na akanki amman ki ke cin amana ta,ki ke kawo mazan banza har kan gadona na sunnah,ki duba kiga saboda kun gama masha'arku har da maniyyi akan gadonki".?
da sauri na kalli inda ya nuna min,da sauri ba dafe Ƙirji na ganin maniyyin ne da gaske,na waro idanuwa na waje cikin tsoro na ce"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un wallahi yaya ka yarda dani wallahi tallahi ban taÆa cin amanarka abayan idonka ba,ina tsare maka mutuncin ka. . . . . .
cikin Ɗaga murya ya ce"shut up!ke haryanzu bakinki bai mutu ba ko?ke bama ki yadda kinyi ba ko?to ki sani ni Bilal ayau na sakeki saki uku.bazan ƙara zama da fasiƙa maci amana irin ki ba.insha Allah sai Allah ya saka min cutar dani da ki ka yi,khairat ni nasan ban taɓa zina da ƴar wasu ba.amman sai aka yi rashin sa'a matata tana lalata da wasu mazan,kinga kuwa Allah baya haɗa mai imani da mara imani.don haka kije Allah ya isa tsakanina da ke".
sosai naji jiri na ɗiba na,kai na ya dinga juyamin.na kasa gane a inda ma na ke aduniya na ke ko a lahira?.Allsh kuwa alokacin ya kawo min Rashida,wacce bata taɓa zuwa gidan ba sai yau ta sameni acikin wani irin mummunan hali,ta fasa kuka ganin goshina duk jini,bugewar dani ashe har goshina ma ya fashe da kuka sosai tana ce wa"khairat me ya faru da ke haka?wanine ya shigo ya aika ta miki haka?".
Ina bani da bakin magana don alokacin ma ban san inda kai na ya ke ba.na dai ji lokacin da ta shigo ammsn daga nan ban san abinda ke faruwa ba,ta bugawa wayar yaya Bilal amman ta gaza samunsa.ta buga wayar yaya Aliyu yaya na,yana É—agawa ta fashe mishi da kuka wai khairat ta mutu.sosai hankalinsa ya tashi.ya taho daga shi sai jallabiya tunda ranar babu aiki yana zaune gida yana shan iska Rashida ta kirasa.
Ko da ya iso bai ga Bilal ba,ya shige direct sashen Khairat ɗin ya jiyo ihun Rashida,da gudu ya isa ɗakin a halin da yaga khairat ne yasa shi shima fashewa da matsanancin hali,ya rungumo ƙanwar tasa baki ɗaya suka yi waje suna kuka Rashida na binsu a baya.
Suna fitowa lokacin shima Yaya Bilal ya fito fuskarsa ta yi jawur ya shiga motarsa zai tayar,da sauri Aliyu ya saka khairat amota ya nufi inda Bilal É—in ya ke,ya ce"Yaya Bilal yanzu Rashida ta kirani wai khairat ta mutu,gashi goshinta har fashewa ya yi,me ya faru?".
Sosai yaji gabansa ya faÉ—i da akace khairat ta mutu amman don ya nuna bai damu ba ya ce"ok ta mutu ko?to sai me kuma zan muku?ai gwara da ta mutu É—in taje cen ta yiwa Allah baya nin laifin da tayi masa,idan kuma Allah yasa ta farfaÉ—o ku tambaye ta abinda ya faru".yana faÉ—ar hakan yaja motarsa ya tafi fuuu,yaya Aliyu da ke jikin window É—in motarsa da bai san lokacin da ya yi gefe ba,don yadda Bilal ya tashi motar kamar zai tashi sama.
Aliyu ya ce"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.me kuma ya faru agidan nan?".tuno da ƙanwarsa da ke cikin mota wacce ke ƙwance rai a hannun Allah yasa ya shiga motarsa ya fige ta da mugun gudu.Allah ne ya kaisu asibitin lafiya likitocin suka fito da gudu sukazo don ɗaukarta,Ganin jini a goshinta yasa likitocin suka ce baza su amshe ta ba.
Yaya Aliyu ya ras yadda zaiyi don shi sam ya manta da wani maganar Ƴan sanda,da sauri ya zaro wayarsa tunowa da Ahmad commisioner of pilice,kira na farko ya Ɗaga wayar da murmushinsa,jin abinda Aliyu ke faɗa ne yasa da sauri ya kashe wayar tare da kira ƴan sanda suka shiga mota suka taho asibitin da Aliyu ya gaya musu.
Hannun Ahmad yana kakkarwa ya saka hannu,hankalinsa na kan khairat wacce ke ƙwance kamar gawa,ya share wasu hawaye masu mugun xafi har yanzu maƙalallen son khairat da tausayinta na maƙale azuciyarsa,aka shiga da ita ɗakin don bata taimakon gaggawa,Rashida sau kuka take har haɗiyar zuciya take,kukan tausayin khairat gani take kamar baza ta tashi ba,tabbas idan hakan ta kasance to tasan ita ma baza ta iya rayuwa matuƙar babu khairat ba.
Babu wanda aka sanarwa da rashin lafiyar khairat ɗin,saboda kada hankulansu ya tashi yaya Aliyu ma da ya ke namiji kuka ya ke kamar ƙaramin yaro,shima Ahmad ɗin kuka ya ke,sai duka suka taru suka dinga yi kamar ƙananun yara.
******
. . . . .kai tsaye Bilal gidansu ya nufa,Allah ne kaɗai ya kaishi gidan don yadda ya dinga gudu kamar zai tashi sama,ya fito daga cikin motar yana layi kamar ɗan shaye shaye,ya yi ɓangaren mahaifiyarsa,tana zaune afarlo taji shigowarsa.cikin tashin hankali ta nufo inda ya ke,baki ɗaya ya ƙwanto jikinta ya ɗora mata nauyinsa baki ɗaya,ta zauna a hankali dashi ajikinsa,ta ƙwantar da kansa akan cinyarta taji jikinsa ya yi mugun yin zafi cikin tausayinsa ta ce"Bilal me ya faru?me aka yi maka?ba kada lafiya ne?".
Kasa magana ya yi,Hajiya Ruƙayya cikin tashin hankali ta buɗe fridge ta ɗakko gorar ruwan faro ta ƙaraso ta buɗe bakinsa,ai kuwa ya buɗe bakinsa yasha ruwan sosai,tausayinsa ya cika mata zuciya tsakanin ɗa da uwa sai Allah bayan ya gama shan ruwan ne ta ce"Bilal yanzu faɗamin me ya faru"?.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.