Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 86

Abu kamar wasa wunin ranar zungur MD yana maƙale a zuciyata, domin ko na so kawar da tunanin shi sai ya dawo mini sabo. Ta kai minti ɗaya biyu sai na buɗe data domin kawai na yi katarin hango shi online, sai dai abin haushi tun daga saukar da ya yi bai sake hawa ba sai dare. A galabaice na ga daren saboda matsuwar ganin shi da na yi.
Cikin sa'a bayan Isha ina hawa na hango shi, farincikin da ya lulluɓe ni ya sa na kasa ɗauke idanuwana daga kan lambar shi. Sannan tunatarwar da ake ta yi mini ta MD online ta ƙara rura wutar murna ta. Haka kawai na tsinci kaina da shiga Gallery na ɗauko hotona da nake ji da shi na ɗora a status, duk da hakan ba halina ba ne ɗora hoto a status. Amma zuciyata ta ƙawatu da saka shi cikin ɗoki da zumuɗi, mintuna a tsakani da ɗora shi na shiga duba saƙunan da ke ta shigo mini har lokacin tsakanin groups da private.
"Ma Sha Allah!"
Ita ce kalmar da ya yi mini comment da ita a jikin hoton. Murmushi na yi a raina ina faÉ—in 'Dama ta samu' Sannan na yi reply da "Na gode Sir"

Shiru bai sake cewa da ni komai ba bayan ya duba saƙon, kawai sai na ji ina sha'awar gaishe shi.
"Ina wuni?" Ita ce tambayar da na yi masa ƙirjina yana bugawa, saboda har raina ina jin kaina tamkar wata mara gaskiya.

"Lafiya lau ya ƙarfin jikin?"
"Alhmdulillah!"

Daga haka kamar ba zai sake ce mini komai ba, sai na hango ya sake cewa, "Gobe sai offis ko?"
Cike da jin daÉ—i na amsa da, "In Sha Allah!"

"Your welcome!"

Yana gama faɗar hakan ya sauka, na yi reply da "Thanks!" Amma har sha biyun dare ta wuce bai dawo online ba balle ya ga godiyar da na yi masa, na ji matuƙar haushin hakan, a raina na ce,
'Wai shi bai san babu kyau ana tsaka da magana a sauka ba a sanar ba?'
Tsaki kawai na yi saboda ya ɓata mini rai ba kaɗan ba, sai da na nutsa cikin tunani na hango rashin yi wa kai adalcin da nake ƙoƙarin yi. Sai kuma na dawo faɗin, "To ma ni ina ruwana da shi wai? Ummh!" Shiru na yi kawai ina ta bai wa kaina laifi, a kan damuwa da wanda bai dace na damu da shi ba, har bacci ya yi awon gaba da ni. A cikin baccin ma na yi ta ganin fuskar shi yana mini murmushi.

Safiyar Laraba na tashi cikin kuzari da ƙarfin jiki, saboda magungunan da na sha sun taimaka mini wurin rage mini ciwon da nake yi. Sannan a gefe ɗaya kewar ofishina da ɗokin ganin MD ya saka ni gaba, saboda ina ji a raina tamkar wannan ne karo na farko da zan fara zuwa wurin aiki.
Kwalliya na yi sosai cikin shiga mai fisgar zuciya, sannan na feshe jikina da turaruka masu ƙamshin daɗi. Jakata na saƙala a kafaɗa, sannan na saka yarana gaba muka fito gidan suna ta yaba kyawun da na yi musu a ido. Inda Haidar yake wasar baki ya ce,
"Kin yi kyau sosai Mama. Ko wurin biki za ki je idan kika dawo aiki?"
Murmushi kawai na yi masa sannan na ce, "Kai na yi wa kwalliyar nan duka domin ka ji daÉ—i Yarona" Haidar ya yi tsalle yana faÉ—in "Gobe ki yi wata Mama, zan siyo miki yalo da kuÉ—in tarata".

Ummu Salma ta maka masa harara tana faɗin, "Daina murna yaro ba don kai kaɗai aka yi ba har da mu". Yana yi mata yelum muka shiga adaidaita sahu, Iman ta riƙo hannuna tana murmushi ta ce "Kin yi kyau Mama" Cike da jin daɗi a zuciyata na rungume su duka ina faɗin,

"Na gode yarana! Ubangiji ya yi wa rayuwarku albarka, kuma ya ƙara shirya mini ku..." Nan take muryata ta fara rawa saboda ƙwallar da ta cika idanuwana.

"Amin" suka ce, sannan suka dinga yi mini surutu kala-kala, tare da ba ni labarin bulalar da za a yi wa 'yan latti a makantarsu, har muka je bakin gate ɗinsu aka ajiye su. Kuɗi na ƙara musu domin su dawo gida saman abin hawa, kada su biyo sayyada kamar yadda suke yi kullum. Godiya suka yi mini dukansu suna mini bye-bye har suka shige, sannan mai adaidaitan ya juya da ni zuwa ma'aikatarmu. Inda nake ji a raina tamkar wannan ne zuwan farko da na fara yi a wurin aikin nawa. Saboda sauyin da na samu tsakanin wancan zuwan da nake yi da wanda zan yi a yanzu.

Shin me zai faru a gaba a kan wannan canjin na Zaituna?🥲 Ni dai ba za a ji mutuwar Sarki bakina ba🏃🏻‍♀️

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*LAMBA TA TAKWAS.*

Har cikin harabar ma'aikatar ya shigar da ni, bayan ya É—an tsaya na gaisa da maigadin wurin. Saboda zaman shi dattijo kuma yarena waton Hausa Fulani, hakan ya sa a duk lokacin da ya gan ni yake ba ni girma sosai ni ma ina ganin mutuncin shi a idona.
Mai adaidaita na biya kuɗin shi sannan na rataya jakata a kafaɗa, taku na fara yi cikin taƙama irin wanda nake jin sauyin tafiyar a jikina.
Gaisawa na fara yi da mutane kamar yadda na saba cikin sakin fuska da babu yabo balle fallasa. Kai-tsaye ofishina na nufa ina baza ƙamshin da ya janyo mini kallo a wurin mutane. Domin ina hankalce da ɗaiɗaikun da suke bi na da kallo ta gefen idona. Murmushi na yi mai bayyana jerarrun haƙorana farare tas da ke cikin ɗan ƙaramin bakina, saboda tsintar kaina da na yi a cikin mayalwacin farinciki.

'Da alamu kwalliya za ta biya kuÉ—in sabulu'.

Zancen da na yi a zucina kenan, bayan na buɗe ofishina na shiga. Zama na yi a kan kujera bakina ya ƙi rufuwa saboda ina ji a jikina zan yi bankwana da damuwar Mukhtar, matuƙar haƙa ta ta cim ma ruwa.
Zamana ba da jimawa ba wani É—aya daga cikin ma'aikatanmu ya shigo yana faÉ—in. Akwai waÉ—anda suke jiran zuwan ki tun É—azu, amma Oga ya ce ki je yana son ganin ki yanzun nan kafin ki fara ganin su.
"Ok" Kawai na faÉ—a cikin tsare gida ya fice, saboda abu ne wanda kowa ya sani ba na sakin jiki da kowa cikin ma'aikatar idan aka cire Amina. Ita ma sai da na gama tantance halinta sannan na fara sabawa da ita a farkon zuwana.
Turare na fito da shi na ɗan goga a hannu sannan na shafe a jikina, nan take ƙamshin ya ƙara kama ni na nufi offis ɗin MD kai-tsaye. Zuciyata a sake kuma cike da zumuɗin yin ido biyu da shi, duk da ina ji a raina babu kyautuwa a cikin abin da nake ƙoƙarin yi. Amma na kasa hana wa zuciyata muradinta.

Ƙofar na tura a hankali bakina ɗauke da siririyar sallamar da harshena ya karye a lokaci ɗaya yayin furzo ta. Kan shi a duƙe yana ta rubuce-rubuce a cikin wasu files, ya ɗago babu shiri tare da jefa idanuwan shi a kan fuskata. Kallo ya fara bi na da shi amma ban san me ya tuna ba ya ɗauke kan shi daga kaina cikin sauri, mayar da idanuwan shi ya yi a kan files ɗin yana ci gaba da rubutun shi.
Shiru ya ɗan ratsa tsakani ina tsaye cikin sanyi jiki, sannan na yi ƙarfin halin furta masa, "Barka da safiya". Daga duƙen ya amsa mini da,
"Barka dai! Ya ƙarfin jikin?"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.