Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 56 of 86

"Lafiya kike kuwa?"

Na faɗi maganar cike da jin haushin banzancin da take ƙoƙarin yi wa kanta. Kallo ta bi ni da shi sannan ta yi hanzarin miƙewa tana gyara zaman rigar barcin da ke jikinta. Soshe-soshen kai ta fara yi tana mayar da hularta bisa kai, ta nufi hanyar ɗakinta ranta a haɗe cikin maƙoshi ta ce da ni,

"Lafiya lau!"

Bayanta na bi da kallo har ta shige ɗakinta ta rufe, murmushi na yi tare da girgiza kaina ina maimata sunan Romiyon a raina, wanda ta raɗa wa Mukhtar ba tare da ta san bai cancanta da sunan ba. Domin bai san komai a kan soyayya ba balle abin da ta ƙumsa, saboda iya sanin da na yi a rayuwar zamana da shi; ko kiss irin na haɗuwar leɓe da leɓe bai taɓa haɗa ni da shi ba.
Kitchen na koma ina ta hada-hadar ɗora mana abin kari. Zuciyata cike da tunanin rashin kawaici irin na Barira, da rashin sanin darajar Mukhtar balle ya sauke haƙƙoƙan da ke kansa.
Kasancewar muna da sauran kayan tea na soya mana Irish da ƙwai. Ina ƙoƙarin fitowa daga Kitchen ɗin hannuna ɗauke da cups da flack's, na ji sautin muryar Barira a sama tana masifa.
"Na rantse da Allah sai ka san ni ka wulaƙanta. Babu wata magana da za ka faɗa mini yanzu na yarda, saboda ni ma ba ka ji kalolin kiran da na yi maka ba amma ka ƙi buɗe mini ƙofa."
Abin da na ji kenan bayan na fito daga Kitchen ɗin, saman carpet ɗin tsakiyar kujeruna na ajiye kayan sannan na ƙwala wa su Ummu Salma kira. Duk da ina jin sautin Mukhtar ƙasa-ƙasa yana magana amma ban ji me yake cewa ba.
Fitowar su Ummu Salma ta yi daidai da fitowar Barira a fusace ta nufi kitchen. Mukhtar ya bi ta yana kiran sunanta cikin ƙaramar murya kafin ya rufe ƙofar.

Baki a sake yaran suke bin ƙofar kitchen da kallo, karantar da na yi wa fuskokinsu na gano mamakin da suke yi. Murmushi na yi mai sauti na miƙe daga durƙushen da nake ina faɗin,

"Ku bari na kawo muku madarar"

Kitchen ɗin na nufa na tura ƙofar, cikin sa'a bai rufe da makulli ba. Kai-tsaye na nufi kular da na saka soyayyen Irish ɗin, duk da na tarar da kular a buɗe Barira tsaye tana ci a cikin plate ɗin da ta shaƙe taf! Ba tare da ta jira na ba ta ba, ko kuma ta tuna da cewa akwai wasu masu haƙƙi da shi a cikin gidan bayan ita.
Sai girgiza ƙafafuwa take yi tana cin abinta shi kuma yana faman yi mata magiya. Na so na yi magana, sai na ga duk abin da zan faɗa a lokacin zai janyo wani sabon tashin hankali a tsakanina da ita.
Kular kawai na ɗauke sannan na ja biredi, wanda shi ma ta fasa ledar ta bar shi a buɗe, na fice ba tare da na ce da su komai. Raina a ɓace na dire kular na koma na ɗauko tire na kasa musu kowa ya ɗauki na shi.
Zuciyata a ƙuntace saboda mummunan ganin da na yi musu a kitchen ɗin. Sai da yaran suka cinye sannan na ce da su,
"Oya ku tashi ku je islamiyya kada ku yi latti"
Suka É—auko jakunkunansu suka wuce, na bi su da addu'ar a dowa lafiya sannan na karya. Na kasa tashi daga wurin na baje saman 3seater tare da rufe idona kamar mai barci, sai hotonsu nake gani a lokacin da suke shagalinsu.

"Ina nawa breakfast?"

Zancen Mukhtar da na ji kenan cikin tsakiyar kwanyata, ban motsa ba kamar yadda ban yi niyyar amsa masa ba.

"Da ke fa nake magana!"

Ya sake maimaitawa a fusace cikin ɗaga murya, gyara kwanciyata na yi ba tare da na ce ƙanzil ba.
"Ni za ki wulaƙanta ina yi miki magana kina sharewa?"

"Wane breakfast zan ba ka bayan wanda ka yi a kitchen?"

"Haƙƙina ne aka ba ni a can, wannan kuma shi kike da haƙƙin bayarwa"

Wani ɓacin rai ya taso mini, nan take ya yi mini lulluɓin da ya rufe mini idon gani, domin ban san lokacin da na diro daga kan kujerar ba ina faɗin,
"An canye haƙƙin ko kana da abin da za ka yi ne idan an hana ka!?"
"Kwantas Hajiya! Ai kuma yanzu babu kare bin damo! Ki yi yadda kike so ni ma na yi nawa."
Yana ƙare faɗar hakan Barira ta fito daga kitchen ɗin sum-sum tamkar munafuka ta shige ɗakinta. Harara na wurga masa saboda kallon da ya bi ta da shi yana 'yar dariya. Na danna masa wani kafurin tsaki har sai da na dantse naman ƙasan leɓena. Sannan na bar wurin ina ƙoƙarin shigewa ɗakina ya ce,

"Sai haƙuri kuma, ni kam na samu inda aka san muhimmancina."

Baya na dawo saboda ganin idan na yi masa banza bai san kawaici ba,
"Bari na faÉ—a maka zancen da ba ya tashi! Wallahi daga wannan karin safiyar; ba zan sake yi mata girki ba. Tun da ta san muhimmancinka ta girka ta ba ka ka ci kai da yaranka."

"Hahahahahh!"

Sautin dariyar da ya yi kenan har da buga ƙafa ƙasa, sannan ya yage baki yana ƙwala mata kira cikin ɗaga murya.

"Barcy!!!"

"Na'am Romiyo!"

Barira ta fito daga ɗakinta cikin sauri ta iso wurinsa da gudu, towel ɗaure a faƙon ƙirjinta da babu tudun komai face na fatar da ke jikinta.

"Ki shirya yi mana girkin rana ni da yarana. Zan aiko miki da kayan cefane idan an dafa a zuba wa Uwargida nata."

Tana fari da ido ta ce, "Haba Aunty! Me ya yi zafi ne haka tsakaninki da Romiyo?"

Baki a sake na dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, maimakon na ji raina ya ci gaba da suya; sai na ji wata dariya ta suɓuce mini ban shirya ba. Sannan na gyara tsayuwata na ce da ita,

"To ke Barcy ina ke ina sanin sirrin mata da mijinta? Yana da kyau ki tsaya inda kike da iko da inda ya ajiye ki, ki daina ƙoƙarin shiga hurumin da ba naki ba har sai an kasa da ke. Girki dai ne ya ce ki shirya yi mana saboda yana so na huta da aikin da na sha haka nan, domin tun da aka fara shagalin bikin aurenku ban zauna ba, kullum ina tsaye tamkar haƙori. Don haka idan kin gama ki zuba mana namu a kula ni da yaransa, kamar yadda ya faɗa miki."

Ina ƙare maganar na juya ba tare da na damu da kallon tuhumar da take aika masa ba. Na je ƙofar ɗakina na ja na tsaya rungume da hannuwa a ƙirji ina musmushin mugunta.

"Wallahi ba haka muka yi da ita ba Allah ma ya sani."

Maganar da ya yi kenan yana ɗaga manunansa duka biyu a ƙoƙarin son ta yarda da zancen shi.
"Daina rantsuwa zan yi girkin kamar yadda ka saka ni, amma wallahi sai ka biya duk wata wahalar da na sha yau."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.