Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 68 of 86

"Duka kuma!?"

Tambayar da na yi mata kenan tare da samun wurin zama na zauna, saboda labarin da take ba ni mai cike da kayan haushi da takaici.

"Duka tabbas! Ba ki ga yadda muka zagaye gidan da shi ba yana ƙoƙarin kamo ni ina gudu har ya faɗi. Lokacin da ya tashi ne na fice gidan don na san zai iya halaka ni. Babu zato na ji na faɗa jikin mutum ya yi hanzarin riƙe ni Allah ya tsare ban faɗi ba. Sai ga Baba Mukhtar ɗin da gudu, ice a hannunsa yana neman kwaɗa mini na laɓe a bayan mutumin."

"CabÉ—ijam! Ki ce artabu kawai kuka sha ke da shi."

Dariya ta fashe da ita sannan ta ce,
"Ai ba ni kaɗai ba har da Umma, don ita ma ba ki ga abin da ta yi masa ba. Sai da mutanen unguwar suka taru ana ba ta haƙuri. Sannan na ja ta muka shiga gidan muka kwaso kayan, munafukar matarsa sai kallon mu take yi, tana harare-harare. Na so ta tanka na rage haushinta da nake ji, don wallahi sai na darji bakinta babu ruwana da ciwon da ke kanta baƙar makira."
"Gara dai da ba ki taɓa ta ba, ko yanzu ba ki san wane irin mataki zai ɗauka a kanki ba balle kin taɓa masa amarya."

Mere ta yi sannan ta ce, "Hu'ummm! Ai wallahi komai zai yi sai dai ya yi, don ba na tsoron komai tun da gaskiya nake goyon baya ba ƙarya ba. Shi ma watarana zai yi da-na-sanin abin da ya aikata musamman idan figaggiyar matarsa ta koya masa hankali."

"Ki dai bi a sannu! Shi kawunki ne Uwa É—aya uba É—aya da Mahaifiyarki. Za ki rabu da ni amma shi ba za ki iya sauya shi da wani ba."
Umma ta shigo tana 'yar dariya ta ce, "Ke ni fa na fara zargin Mukhtar bai da lafiyar ƙwaƙwalwa. Saboda yadda ya tuɓure yau a kan cewa zai sake ki amma sai an dawo masa da yaransa. Saɓanin jiya da yake kuka a kan a yi haƙuri ki koma ba zai iya rayuwa babu ke a gidan ba."
Ƙirjina ne ya buga dam-dam! Saboda zancen a ba shi yaransa da na ji ya dake ni babu shiri. Gabana yana cigaba da faɗuwa na fara faɗin,
"Ai wallahi ba zan iya ba shi yarana ba, ko babu Barira a gidan balle tana ciki. Saboda jiya kafin a yi rikicin da Maman Taufiƙ ta cire mata kitso, na kama ta da ƙawarta suna aikata harkar banza. Don haka wallahi komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan ba shi yarana ba. Daman ba komai ba ne ya sa ya biyo ta wannan hanyar ba; don kawai ya san ba zan iya rabuwa da su ba. To kada Allah ya sa ya sake ni ɗin ya yi ta riƙon takardar sakin har duniya ta jingine."
Na ƙare maganar jikina yana rawa saboda yadda maganar ta shige ni ba kaɗan ba, kuma ta ƙona mini zuciya.

"Ki bar ni da shi! A wannan karon zai gano kowane gauta ja ne."

Zancen Umma kenan tana ficewa É—akin, Sajida ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Na ji matuƙar haushin da na gano mijin Maman Taufiƙ ne muka yi karo da shi, ya ɓoye ni bayansa ya hana Baba Mukhtar ya sauke mini ƙaton icen da ke hannunsa. Allah ya tsare matarsa ba ta fito ba da na san ko kashe ni za ta iya yi a lokacin."

"Ki cire wa zuciyarki tsoronta, kawai dai ki yi iya bakin ƙoƙarin ki wurin hana wa kanki shi ko don zaman lafiya."
Abin da na faɗa mata kenan zuciyata ɗauke da damuwa, saboda gabaɗaya na rasa farincikina. Balle walwalar zuciya a kan zancen Mukhtar da na ji na karɓar yara. Don na san zai yi hakan ne kawai domin ya ƙona mini rai, ba don ya damu da su ba. Ni kuma ba zan taɓa bari tarbiyar yarana ta lalace a kan banzan shirmensa da tunanin kansa maras inganci ba.

Haka muka yi ta bitar abin a tsakaninmu, ni, Umma, Sajida da kuma Inna Kulu. Ban samu zuwa aiki ba, haka ma yaran ba su je makaranta, saboda lokaci ya ƙure sun yi latti sosai. Sajida tana gidan har aka yi sallar Zuhur muna tsaka da cin abinci aka kira ta a waya. Fuskarta a haɗe ta ɗaga kiran ba tare da ta yi magana ba. Babu shiri ta miƙe tsaye dafe da ƙirji tana zaro ido waje ta ce,

"Aure!!!?"

Ban san me aka ce mata a cikin wayar ba ta jefar da wayar ta dunƙule tana kuka. Cikin tashin hankali na miƙe na yi kanta a ruɗe ina tambayar lafiya. Su Umma ma suka shigo ɗakin muka rufu kanta da tambayoyi, amma ba ta fasa kukan da take yi ba har da majina.
Da ƙyar muka samu ta sassauta kukan sannan ta ce,
"Rayuwata ta zo ƙarshe! Tun da aka ɗaura mini aure da Aminu mijin Maman Taufiƙ! Wallahi na fi so na mutu da dai na yi wannan aure."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Ita ce kalmar da na faÉ—a a bakina hannuna a kai ina zarya tsakiyar É—akin."

Umma ta fara faɗin, "Haƙuri za ku yi dukanku, saboda ba ku isa ku hana Allah aiwatar da abin da ya tsara ba. Daman can an ƙaddara akwai aure a tsakaninsu shi ya sa hakan ta kasance. Don haka ku daina jayayya da ikon Allah! Ku rungumi haƙuri dukanku ba ku san abin da Ubangiji ya kulluɓe a cikin auren ba."

"Wallahi Umma sai dai na bi duniya ba zan zauna gidan mutumin nan ba!"

"Subhanallah! Ki daina faɗar ire-iren waɗannan maganganun ba su da daɗin sauraro. Ki rungumi ƙaddararki wataƙila hakan alheri ne ba ki sani ba."
Inna Kulu ta faɗa tana ƙoƙarin rarrashin ta da hannu.
"Babu wani alheri a cikin irin wannan auren! Tun da ban son shi, kuma ba da amincewata aka yi ba. Don haka wall..."

Kiran wayarta da aka sake yi dukanmu muka mayar da hankalinmu a kanta. Amma ko kallon wayar ba ta yi balle ta ɗauka tana ta kuka har kiran ya tsinke. Sai da aka ƙara wani kiran sannan na yi jarumtar nufar inda wayar take na ɗauka. Ganin sunan mai kiran ya sa na gano Yaya Maimuna ce take kiran ta.
Cike da tsabar jin haushinta na É—aga kiran ba tare da na ce da ita komai ba.
"Wallahi duk inda kike ki dawo gida yanzun nan ko na tsine miki albarka. Aure kuma ko kina so ba ki so an ɗaura ke kawai ake jira ki dawo a kai ki gidan mijinki. Sai ki je ki yi auren ke ma ki daina shiga rikicin auren wasu, kina ƙoƙarin ci wa ƙanena zarafi a kan Shegiyar matarsa marar tsoron Allah! To wallahi ko ki dawo gida yanzun nan kamar yadda na faɗa ko na tsine miki albarka, sai ki bi duniya ki lalace gabaɗaya kowa ma ya huta da shegen halinki."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.