Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 86

"Ina zan kai ki?"

Ita ce tambayar da ya jefo mini wadda ta zamo magana ta farko da ta shiga tsakanina da shi. Ban ce da shi komai ba ina ci gaba shesshekar kukana har sai da ya sake tambayar, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,

"Tasha"

"Ba zan je tasha a yanzu ba, domin ko na je ba lalle ne a samu abin hawa ba."
Maganar da ya yi kenan cikin matsanancin fushin da ya kausasa muryar shi.
"Ba ni da kowa a garin nan.. Birnin Keb...bi zan..je." Na ƙare maganar da ƙyar saboda kukan da ya ci ƙarfina. Daga haka bai sake cewa da ni komai ba har muka je wata unguwa, a lokacin da ya isa bakin wani ƙofar gida ya fara horn Maigadi ya wangale masa babbar ƙofa.
Nan take ƙirjina ya buga, cikina ya katsa saboda tunanin da ya ɗarsu raina. A kan zancen da zuciyata take sanar da ni gidan shi ne ya kawo ni, hakan ya saka ni faɗuwar gaba tare da wani sabon tashin hankali. Saboda tuno masifar matar shi da irin kashedin da ta yi mini a kan shi.

"Fito mu je!"

Zancen da ya yi kenan sannan ya yi gaba, ni kam motsin kirki kasa yi na yi balle na samu kuzarin fita daga motar, na bi shi kamar yadda ya umurta. Tsawon minti biyar ina cikin motar ban motsa ba, cikin tashin hankalin da ya saukar mini da gumin da ya jiƙa mini fuska nan take.

"Ki fito na ce!"

Maganar shi kenan da na sake ji a cikin kunnuwana cikin tsawa tare da saukar abu a jikina, hannu na saka na É—auki abin da ya jefo mini a jiki na shiga warware shi. Fahimtar hijabi ne ya jefo mini na saka, ya sa na yi hanzarin sakawa kafin na fito daga motar.
Bayan shi na bi tamkar raƙumi da akala har muka shiga cikin gidan muka haye sama, mun wuce wasu ɗakuna sannan muka isa wani ɗakin ƙarshe ya tura ƙofar muka shiga.
Ƙamshin da ya daki hancina da raɓar da ɗakin ya kwasa nan take jikina ya yi sanyi ƙalau. Kujera ya nuna mini na zauna sannan ya fice mintuna goma tsakani ya dawo ɗauke da plate ɗin abinci.
Gabana ya ajiye sannan ya nufi firij ya É—auko gorar ruwa da Hollandia ya sake ajiyewa a gabana. Zama ya yi nesa da ni yana haÉ—e fuska ya ce,
"Ki ci abincin."
Kai na fara girgizawa domin ba zan iya magana ba.

"Ki ci na ce!"

Tsawar da ya katsa mini ce ta sa na yi hanzarin jawo plate ɗin na buɗe, Indomie shaƙe a cikin plate ɗin sai dafaffen ƙwai guda biyu har an ɓare.
Cokali mai yatsun da na gani a ciki na shiga É—ebo abincin ina kai wa bakina hawaye yana zarya a kan fuskata. Sai da na kusa cinyewa sannan na ajiye cokalin na sha ruwa, bai matsa mini a kan na sha madarar Hollandia ba. Illa kafe ni da idon da ya yi fuskarsa a haÉ—e wanda idon shi yake nuna mini tamkar ya rufe ni da duka.

"Me ya fito da ke a cikin tsohon daren nan?"
Tambayar shi kenan zuwa gare ni, ina zuƙar majinar kuka na ce, "Tafiya zan yi."
"Zuwa ina?"
"Kebbi."
Shiru ya ratsa tsakani bayan na sanar da shi inda zan je, duk da ba haka ne gaskiyar abin da ke raina ba. Domin babban burina a lokacin na yi nesa da duk inda aka san ni, balle na je inda za a dawo da ni gidan Mukhtar domin na ci gaba da zaman 'ya'yan da nake yi.

"Me ya haÉ—a ki da mutanen da na ga sun biyo ki?"
Ya sake jefo mini wata tambayar, kai-tsaye na sanar da shi duk abin da ya faru. Sai dai ban sanar da shi Ummita ta taɓa ƙirjina ba, saboda na tsani duk abin da zai zubar mini da ƙima a rayuwata.

"Me ya sa ba ki bari da safe ki yi tafiyar ba? Yanzu da ace wani abu ya same ki a hannun waɗannan azzaluman wa gari ya waya? Ga shi kin zubar da jakunkunanki, wataƙila ma akwai abubuwa masu muhimmanci a ciki."
Maganganun da ya faɗa kenan cikin faɗa tare da ɗaga murya, cikin tsoro na dinga kallon ƙofar ɗakin saboda tunanin yadda zan kare kaina idan matar shi ta iske ni tare da shi a ɗakin.

"Daidai ina kika jefar da jakunkunan?"

Sai da na haÉ—iye yawun tsoro sannan na yi masa bayani, tare da tsoron kada ya ce zai koma É—auko su wani abu ya same shi saboda ni. Bayan haka kuma ba na so ya bar ni gidan matar shi ta nemi salwantar mini da rayuwa, don na san muddin ta yi ido biyu da ni sai buzuna.

"Me da me ne a cikin jakar?"
"Credentials É—ina ne da wasu 'yan kayana, sai wayata da ATM tare da sauran wasu tarkace."
Na ba shi amsa jikina yana rawa, kai-tsaye ya nufi hanyar fita É—akin tare da faÉ—in,
"Jira ni yanzu zan dawo."
Zumbur na miƙe tare da rawar jiki da ta murya ina haɗiyar yawun tsoro masu wucewa muƙut a wahalce. Kuka na dawo yi masa ina faɗin, "Don Allah ka bar kayan nan kada ka koma ba sai an ɗauko ba, idan ma za ka je mu je tare dukanmu daga can ka ajiye ni wani wuri na jira asuba."
"Babu inda zan je da ke! Ki jira ni a nan yanzu zan dawo."
Yana ƙare faɗar hakan ya fice tare da rufe ni ta baya, dole na durƙushe jikin ƙofar ina wani irin kuka mai kama da na mutuwa. Saboda abubuwa sun cakuɗe mini a kwanya na rasa me zan kama na ji sanyi.

Na daÉ—e a cikin halin kafin na fara jiyo sautin kukan yaro wanda ya sa hantata kaÉ—awa, domin hakan ya tabbatar mini da dole ne matar shi ta farka duk nauyin baccin da take yi. Kuma faruwar hakan tamkar fallasa asirin rufin É—akin da aka yi da ni ne, wanda alamu ya nuna mini kafin ya dawo ta yi watanda da naman a cikin gidan.

Safa da marwa na fara yi da a tsakiyar falon, hannuna a ka ina tsiyayar ruwan hawaye mara sauti. Kukan yaron na ji ya yi yawa, da muryar shi gwanin tausayi. Na nufi ƙofar ɗakin na kara kaina jikin ƙofar domin na ji ko akwai wani motsi bayan na shi.
Amma har ya ci kukan ya bari don kan shi ban ji muryar kowa ba balle wani motsi. Ƙarfe biyu da rabi na dare da mininti shidda, na ji alamun takun tafiya yana kusanto ɗakin da nake, gabana ya ƙire ya faɗi dum-dum! A lokacin da na ji ana murɗa ƙofar ɗakin da nake ciki.

Shin wane ne? MD ne ko matar shi?😹

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*LAMBA SHA BIYAR.*

Ƙoƙarin buɗe ɗakin da na ji ana yi, hakan ya ƙara ƙarfin dakan luguden uku-uku da zuciyata ke yi. A ɗari na bazama da gudu na faɗa wata ƙofar da na gani, babu jinkiri na saka key tare da shan jinin jikina na lafe a jikin bango. Addu'a na dinga yi a zuciyata bayan na toshe bakina da nake gudun ya tona mini asiri.
Takun tafiya na ji ana nufo bakin ƙofar toilet ɗin da na ɓuya, hankalina bai ƙara tashi ba har sai da na ji an sake taɓa handle ɗin ƙofar an murɗa. Babu shiri na darje daga tsayen da nake, saboda sulɓin tyles ɗin da ya ja ni zuwa ƙasa na yi zaman 'yan bori.
Ƙuguna na dafe ina yarfa hannu saboda sosai na ji zafin faɗuwar. Shiru ban san sake jin motsin komai ba bayan takun tafiyar da na ji kamar an bar bakin ƙofar. Mintuna a tsakani na fara jin kukan yaron a cikin ɗakin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.