Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 86
Ajiye wayar kawai na yi saboda ban san me zan ce da shi ba a lokacin, domin kwanyata babu komai a cikinta kamar an goge mini komai. Fita É—akin na yi na nufi kitchen, cike da tabbacin ganin abin da zan jefa wa cikina don na san Ummu Salma ta yi mana girki.
Shinkafa da wake na gani, cikin sauri na zuba na dawo falo na zauna ina ci ina tunanin kashedin da matar MD ta yi mini, wanda nake jin sautinta yana amsa-kuwa cikin kunnuwana tamkar a lokacin take magana. Ban san lokacin da na canye abincin ba saboda dogon nazarin da na lula.
A gurguje na gama sallah, saboda kiran da ake ta yi mini wani bayan wani ga wayata da ƙara. Zabura na yi cikin zafin nama na ɗauki wayar a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa. Da hanzari na danna kore saboda ganin sunan MD ɓaro-ɓaro a jikin wayar, kuma zuciyata ta tabbatar mini da shi ne ba matar shi ba.
"Don Allah ki yi haƙuri, kada ki ga na takura ki. Me ya faru ne na ga kiranki..."
"Daman wayar da na gani ce a cikin ledar da ka ba ni. Shi ne na ce ko ka manta ne ka sako ta a ledar..." katse ni ya yi da faÉ—in,
"No! Taki ce ba mantuwa na yi ba. Kuma kada ki ɗauki ce wa na ba ki ita ne da wata manufa. Na ba ki ne a matsayin kyauta saboda ci gaban da kika kawo mana a cikin ma'aikatarmu. Muna alfahari da samun zaƙaƙurar ma'aikaciya irinki, fatan za ki karɓa hannu bibbiyu domin ki ji daɗin ƙara jajircewa a kan aikinki".
Girmansa da mutuncin shi ya sa na ce da shi na gode "Na gode sosai Sir. Allah ya ƙara rufa asiri" Muka yi sallama a mutumce, amma a raina na so ya karɓi wayar shi. Ko ba komai zan yi nesa da rashin mutuncin matar shi, duk da ba na zaton ta san da wayar balle zancenta...
"Da wa kike waya?" Ita ce tambayar da Mukhtar ya jefo mini ba tare da na ji motsin shigowar shi ba. Fuska na haÉ—e alamun babu sassauci ga duk abin da zan furta cikin bakina a lokacin.
"Ina ruwanka da wanda nake waya da shi. Ko kana da ikon duk wani motsin da zan yi sai ka san da zaman shi?" A fusace na yi maganar cikin ɗaga murya. Bai kula ni ba ya nufi wurin wayar da ke kan gado har lokacin, ya fiddo ta a leda yana jujjuya kwalin yana girgiza kai. Ban hana shi ba har ya gama tsugudidin shi ya ajiye tare da rugume a hannu a ƙirji ya ce,
"Wai me kike son mayar da kanki ne? A tunaninki Allah ba zai kama ki a kan cin amanar auren da kike yi ba...?"
"Kafin ya kama ni kai ne mutum na farko da haƙƙi zai rataye maka wuya ka mutu a wulaƙance. Yanzu kai har kana da bakin faɗar ana cin amanar aure? Kai nawa ka yi kafin ni na fara? Ko ka manta bala'in da kake yi na tuna maka yanzun nan? Ka san darajar aure kake shiga hurumin wasu matan auren? To bari ka ji abin da ba ka sani ba, a yau duk abin da na zama wallahi kai ne ka ɗora ni a kan hanyar na miƙe ɗoɗar. Saboda matan auren da ka yi rayuwa da su haƙƙinsu ne ke ƙoƙarin fita a saman kaina..."
Jikina yana rawa nake faɗar maganar saboda tsananin ɓacin ran da maganar shi ta saka ni. Kafin shi ma ya katse ni da faɗar,
"Babu inda aka ce wai don wani ya yi abu kai ma sai ka yi. Ki bar ni da haƙƙinki da kika ce na ɗauka, ke kuma ki sauke wanda yake kanki ki huta. Amma wayar nan ko ki mayar wa ɗan iskan da ya ba ki ita. Ko kuma na sanar wa Umma tun da ni kin raina ni ba kya jin maganata..."
A harzuƙe na ce "Duk inda za ka je ka faɗa ka je ka faɗa, amma wallahi ba zan mayar da wayar nan ba. Idan ka isa kai namiji ne ɗan halak, ka haɗa ni da takardar sakina uku yanzun nan ba sai anjima ba..."
"Allah ya ba ki haƙuri. Tun da ke ba ki da wani zance a rayuwarki sai na saki".
"Aurenka auren tsiya miye amfanin shi? Wallahi da irin wannan auren naka gara zawarcin mace dubu. Don kai ba mijin aure ba ne kuma ba ka kai namiji ba har yanzu..."
"Ya isa! Kada ki nemi faÉ—a mini babu daÉ—i. Waya dai ce ki je ga ki ga ta nan. Idan wadda ta isa da ke ta zo ai sai ku yi maganar tun da ni kin mayar da wani shashasha".
Daga haka ya fice fuu tamkar ya tashi sama, kallon banza na bi shi da shi sannan na yi tsaki. Wayar na mayar a leda sannan na ɓoye ta, don na san tsaf zai iya dawowa ya ɗauke ta ba tare da na sani ba. Zuciyata cike da alwashin ko Ummata ta ce na mayar da ita ba zan mayar ba balle shi.
Ku ci gaba da bi sannu a hankali za mu je inda warwarar ƙullin da ya wargaza zaman lafiyar auren Zaituna da Mukhtar 😅
D. AUTA CE âœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA TA BAKWAI.*
Raina a ɓace na fito falo saboda sautin maganar shi da nake ji a sama, yana bayanin rikicin da muka yi da shi. Wanda nake da tabbacin waya ce yake yi kuma Ummata ce yake faɗa wa. Bakin ƙofar shi na nufa saboda baƙincikin makircin da na ji yana yi a cikin wayar, don bayan abin da ya haɗa mu har da ƙarin gishiri da mai, yana ta ƙoƙarin dole sai ya ɗora mini laifukan da ya saba ya wanke kan shi. Saboda komai na yi a wurin shi laifi ne shi kaɗai ne mai yin daidai.
"Wallahi Umma har yanzu suna tare, a kan shi yau babu abin da ba ta faɗa mini ba. Babban baƙincikina mutane har sun fara yamaɗiɗi da ita a cikin unguwar nan saboda tarayyar da take yi da shi..."
"Hakiƙa duk mai irin halinka a rayuwa ba ƙaramar asara ya yi ba wallahi. Ina takaicin zama wuri ɗaya da kai, ina da-na-sanin auren da na yi maka tsawon shekaru. Haka ma ina tausaya wa yarana da na yi zaɓen tumun dare wurin zaɓar musu uba kamar ka..." Abin da na faɗa kenan a bakin ƙofar ɗakin shi, cikin ɗaga murya bakina yana kumfa, domin ya tabbatar da na ji abin da yake faɗa.
"Ai kin saba faÉ—a ba tun yau ba, don haka yanzu ko kin maimaita ba abin mamaki ba ne..." Na katse shi cikin hanzari ina faÉ—in,
"Tir! Da rayuwarka Mukhtar! Ka ji haushi iya haushi a kan rayuwar azuzancin da kake yi. Idan burinka haÉ—a ni da mahaifiyata ne, to ka je ka ci gaba ga gani idan Allah zai bar ka..."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.