Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 44 of 86

"Bazar kowa bazar kowa."
"Da bazarka ce nake taka rawa."
"Haƙiƙa ya habibina"
"Ƙaunarka ce ta sa ni zumuɗi."
"Yau sai ka zo mu É—an taka rawa. Yau sai ka zo mu É—an taka rawaaaa!"

Waƙar da na fara rerawa kenan, da abin ya yi mini daɗi na ajiye plate ɗin tuwona na fara tiƙar rawa, gaban shi na zo ina laƙamo wuyansa tare da goga fuskata jikin tashi musamman da na zo ƙarshen baitin ina faɗin "Taka rawaaaa!"
Cire hannuna ya yi daga wuyan shi ya wurgar cikin fushi, tare da nuna ni da hannu yana faÉ—in,
"Sai kin san ni kika wulaƙanta!"

Yana ƙare faɗar haka ya juya zai fice gidan, na bi shi da waƙar,
"Ku yi ta kanku"
"Mu ma mu yi ta kanmu"
"Dariyaa ba fa so ba"
"Ya raye daÉ—in dariyalle"
"Mai hali bai bari ba"

Har ya fita ya dawo buguzum ya shiga ciki kamar ya kifa, na koma na zauna tare da É—aukar plate É—in tuwona ina ci. Lokacin da na ji zai fito na sake É—auko wani sabon baiti na É—ora.
"Bana an gama komai"
"Bori ya kashe boka"
"In dai taro ne in babu ai suna ne"
"Allah ya yi sarkin daka shi ne turmi ahayye"
"Takun ya yi wasu sun saki reshe sun kama ganye."
Babu zato na ji ya shaƙo wuyana, cikin azama saki plate ɗin na rarumi jarumar shi na matse iya ƙarfina. Ya yi hanzarin saki na ya dafe gaban shi hannu biyu yana faɗin,
"Wallahi sai kin gane kuskuren tozarcin da kike ƙoƙarin yi mini a gidan nan."
Daga haka ya fice gidan dafe da gaban shi yana nuna ni da hannu yana ƙwafa.

Na bi ƙofar da harara kafin murmushin mugunta ya suɓuce mini ba tare da na shirya ba. Haka kawai na tsinci kaina cikin nishaɗi, ko babu komai ban bari ya gano dakan luguden da zancen auren shi ya yi mini a zuciya ba.
Saboda ban yi zaton zan ji kishin shi a raina ba, kamar yadda na ji zafin zancen auren da ya yi mini ba a zuciya.
Daren ranar kwana na yi cikin yarana cike da jin daɗi da farinciki, duk da wani gefen zuciyata yana hasko mini kalar matar da Mukhtar zai aura. Tsaki na yi ya fi a ƙirga saboda tunanin kowace ce wataƙila ta fi ni komai, shi ya sa ta yi nasarar kama masa wuya har ya amince zai aure ta.

'To ina ruwanki idan ma ta fi ki? Ke da ba ki son shi kishin me za ki yi na shi?'

Tambayar da zuciyata ta kitsa mini kenan, wadda na kasa bai wa kaina amsa. Saboda ni na sani ba Mukhtar ne ba na so ba, halinsa ne ya janyo ya sire mini na juya wa son shi baya. Kuma ba na ji zai iya yi mini abin da zai ya goge tabon baƙincikin da ya bar wa zuciyata iya rayuwa.

Warr💃🏻

Na yi nan kada Mukhtar ya ci ufana🤣🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

D.AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*ASHIRIN DA BAKWAI.*

Da safe ban fita aiki ba har sai da na gyara zaman kujeruna, kasancewar falon babba ne na yi gefen É—akina da su duka. Sannan na sa aka kafa mini plasma TV ta a bango, daidai tsakiyar kujeruna. Saboda ba na son a zo yi wa amarya jere a nemi kawo mini rainin hankali, ko kuma shi ya faÉ—a mini abin da ba zan ji daÉ—i ba a samu matsala.
Ranar sai ƙarfe sha ɗaya na je ma'aikatarmu, na duƙufa aiki sosai ba tare da na biye surutun Amina ba. Lokacin da aka tashi ma ban yi jinkirin komai ba na nufo gida, saboda tunanin yaran da ke raina. Domin fargabar da nake ciki a kan kada ya hana su yin girki kamar yadda ya yi jiya, cikin sa'a na taradda Ummu Salma kitchen tana aikin abincin.
Sannu da zuwan da suke yi mini kawai na amsa, sannan na yi wanka a gurguje na fito. Iman na ce ta zo ta raka ni mu je gidan Maman TaufiÆ™. Haidar ya fara rigimar sai ya bi ni na ce da su kowa ya yi zamansa na fasa ba zan je ba.
Abincin Ummu Salma ta kawo mana muka baje a tsakiyar kujerun muka fara ci muna hira. Mukhtar ya shigo da manyan ledodi a hannunsa ya yi ɗakin shi yana muƙu-muƙu, sai da ya fito sannan ya fara faɗin ina abincin shi.
Kallo ma bai ishe ni ba balle na tanka masa, Ummu Salma ce ta miƙe ta ɗauko masa kular abincin ta miƙa masa. Karɓa kawai ya yi ya nufi ɗakinsa, na bi bayansa da harara saboda haushin auren da ya jajiibo wa kansa nake ji.

***
Abu kamar wasa, cikin kwana biyu Mukhtar ya shiga fafutukar auren shi gadan-gadan. Domin kuwa na ji labarin ya kai wa amaryarsa lefe daidai gwargwadon ƙarfinsa. Mafarin na sani ma, yara ya shigo wa da lemuna ya bai wa kowa gora ɗaya, sannan ya ba su biskuit guda huɗu ya ce a kawo mini.
Muna falo ni da su muna kallo Sajida ta kira ni a waya, cikin muryar damuwa ta ce da ni, "Aunty ke ya ba ki kayan?"
"WaÉ—anni irin kaya Sajida?"
Tambayar da na mayar mata kenan don ban gane inda zancenta ya dosa ba, "Kayan faÉ—ar kishiya mana, saboda na ga ya yi wa amaryar lefe ma sha Allah tamkar wata budurwa."
Ƙirjina na ji ya buga dam-dam! Sai da na dafe saitin zuciyata saboda luguden da take yi mini, sannan na yi murmushin ƙarfin hali na ce da ita,
"Ma sha Allah! Ki ce da ke aka kai lefen? To Allah ya tabbatar da alherin da ke ciki."
"Amin Aunty! E, da ni aka je. Amma ke kala nawa ya ba ki? Don na ga ita kala goma sha biyu ne bayan tarkacen da ke ciki."
"Allah ya sa ta kashe lafiya. Sai dai ni bai ba ni komai ba Sajida, amma kuma hakan ba zai hana ni saka sabuwar sutura a ranar bikin ba."
Ajiyar zuciya ta fara saukewa sannan ta ce, "Allah dai ya kyauta Aunty. Wallahi idan kika ga matar sai haushi ya nemi kashe ki. Ni na rasa me ya gani a jikinta yake wannan rawar jikin auren. Ki yi haƙuri Aunty in Sha Allah babu inda auren nan zai je, don kina zaune za ki ga haƙƙinki ya fita a kan duk wanda ya zalunce ki."
"Kada ki damu Sajida, Allah yana tare da ni koyaushe. Na gode sosai da ƙaunar da kike nuna mini a kowane lokaci."

Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar, shiru na yi ina nazarin maganganunta.
'Waton dai tukuicin kai lefen ne ya ba mu muka laƙume ba tare da na sani ba.'
Haka kawai na tsinci kaina cikin damuwar da ta janyo mini zubar ruwan hawaye, waÉ—anda ban shirya wa zuwan su ba.

'Ashe ma Bazawara ce!'

Zancen da na yi kenan a zuciyata ina kuma maimatawa a cikin raina.
Murmushin takaici na yi tare da jin haushin Ummata, wadda ta janyo mini ganin irin wannan ranar baƙincikin a gidan Mukhtar. Don da a ce ta bar ni na yi abin da nake so, da tuni ba wannan zancen ake yi ba. Da rayuwata ta yi farin da zan hango haskenta gaba da bayana.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.