Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 83 of 86

Amsar da zuciyata ta ba ni kenan, babu shiri na yi murmushi. Saboda daman can na yi niyyar fashe ƙwan Mukhtar a gaban kowa domin a san halin da yake ciki. Shi ma ya san matsayinsa a addinance ko da zai tuba kafin ya mutuwa ta ɗauki ransa, cike da fatar ya samu rabauta a nan duniya da gobe ƙiyama.
Bayan kowa da ake buƙatar gani a wurin ya hakarta, aka buɗe taro da addu'a sannan aka fara bayanin abin da ya haɗa mu duka.
Wani mai farar takarda a hannunsa, ya fara gabatar da ƙarar da Umma ta kawo kotun, a kan tana buƙatar Mukhtar ya sake ni. Alƙalin ya kira sunan Mukhtar ya jaddada masa abin da Umma take nema a wurin shi. Mukhtar ya gyara zamansa sannan ya ce,
"Ranka shi daɗe! Ba zan iya sakin matata ba! Don haka ina neman alfarmar a yafe mini mu daidaita kanmu. In Sha Allah zan gyara duk abin da ta ce ina yi mata ba tare da ɓata lokaci ba."

Kallon-kallo muka fara yi da juna tsakanin ni, Umma da Kawu Sale har ma da su Yaya Maimuna. Kawu Sale ya É—aga hannu alamun yana son a ba shi damar yin magana.
Alƙali ya ɗaga masa hannu alamun ya faɗi shaƙƙuwarsa. Kawu Sale ya miƙe yana gyara babbar rigarsa ya ce,

"Ranka ya daÉ—e Mukhtar ya saki Matarsa jiya. Saboda Yayarsa ta ba mu takardar sakin Zaituna da hannunta ta ce shi ya ce a ba ta. Kuma Alhmdulillah mun duba mun gani saki uku ne a cikin takard...!"

"Wallahi! Wallahi! Ni ban saki matata ba!"

Zancen Mukhtar kenan da ya karaɗe ɗakin bayan ya zabura, jikinsa har ɓari yake yi wurin faɗin maganar tun kafin Kawu Sale ya kai ƙarshen maganarsa. Mamaki ya game fuskokin mutanen wurin, amma ni ko gezau ban yi ba. Saboda daman can na san za a rina; wai an saci zanen mahaukaciya.

"Ina Yayar tasa take a nan?"

Tambayar da Alƙalin ya jefo kenan yana wurga idonsa domin ya hango ta ina zai gan ta. Yaya Maimuna ta miƙe ido wuƙi-wuƙi muryarta tana rawa ta ce,
"A lokacin da yake cikin zafin ciwon da ta yi masa rauni a gabansa. Ya ba mu umurnin mu rubuta mata sakinta uku mu kai mata, bayan ya tabbatar mana da ba zai sake zama da ita ba har abada!"

"To ni dai wallahi ban san na sake ta ba, ban taɓa furta saki a bakina ba ko a hayyacina balle ina cikin zafin ciwo. Kuma ni dukan da ta yi mini a jikina bai zautar da ni ba balle na fita hankalina, na yi irin wannan aika-aikar! Don haka ni ba da yawuna aka ba ta takarda ba, kuma ban san lokacin da suka yi ba. Sannan ba su sanar da ni ba sai yanzu da na ji an faɗa!"

Ɗakin ya yi tsit na ɗan lokaci ana nazarin maganganun Mukhtar. Kafin Alƙalin ya yi gyaran murya ya ce,
"To a shari'ance, wani ba ya sakin matar wani. Ko da Mahaifiyarsa ce ko mahaifinsa, addini bai ba su damar sakin matarsa ba balle Yayarsa. Saboda haka takardar sakin da aka ba ta ba ta saku ba! Har yanzu tana nan matsayinta na matarsa. Don ko da a ce shi ne ya furta sakin da bakinsa ba ya cikin hayyacinsa; to akwai aurensu matuƙar ya dawo hankalinsa ya nuna bai san ya aikata ba. Idan ma ya yi ne da gangan ya ce bai san ya yi ba, shi Allah ya sani kuma zunubin da aka ɗauka cikin auren bayan haka duka a kansa zai hau. Domin mu da zahiri muke aiki, sanin gaibu sai Ubangijin da ya halicci ƙirazanmu!"

"Alhmdulillah!" Ita ce kalmar da Mukhtar ya furta a bayyane cikin É—aga murya, har da É—aga hannu sama ya shafa a fuskarsa alamun ya yi nasara.
Umma ta ɗaga hannu aka ba ta damar magana ta miƙe,
"Ranka ya daɗe ni mahaifiyar Zaituna ce! Kuma ina buƙatar a raba aurenta da shi, tun kafin baƙincikinsa ya sa zuciyarta bugawa. Saboda tun da ta aure shi take fuskantar baƙinciki da ƙuncin zuciya har yanzu da muke wannan maganar. Ƙazafi, sharri, cin amana, yaudara, ƙarya, munafurci babu kalar wanda bai ƙulla mata ba. Tun tana ɓoyo ba ta bari na sani har ta fara sanar da ni ina tausar ta. Da abin ya kai maƙura ta fara neman hanyar barin gidansa ina danne ta, saboda ba na so ta fita gidan uban 'ya'yanta ta bar yaranta a gantale. Amma yanzu ni da kaina na tsani zamanta da shi, saboda an yi zama babu adadi ana yi musu sulhu. Sai an gyara kwana biyu ya dawo ma halinsa, to mun gaji daga ni har ita, har masu zaman sulhun. Ya sallame ta ko kuma ku ku sallame ta idan ya ƙi bi ta hanyar lalama!"

Shiru ya ratsa tsakanin maganganun Umma kafin Alƙalin ya yi gyaran murya ya ce,

"Ina Zaituna!"

Na miƙe jikina yana rawa saboda idanuwan da aka zuba kaina.
"Mijinki yana ba ki ci da sha da sutura?"

"Ba ya ba ni ranka ya daÉ—e! Saboda lalurorina duka da na yarana a kaina nake É—aukar su, tun lokacin da na fara aiki!"

"Subhanallah!"

Ita ce maganar da na ji wani ya faÉ—a wanda ban san lokacin da ya shigo É—akin ba. Sannan muryar Mukhtar da na tsinkayo yana faÉ—in,

"Wallahi ranka ya daɗe ƙarya take yi!"

Alƙalin ya dakatar da shi da hannunsa sannan ya gyara zamansa ya sake jefo mini wata tambayar,
"Ɓangaren shimfiɗa fa! Yana sauke nauyin da Allah ya ɗora masa kanki?"

"Ba ya saukewa! a
Asali ma rabon da mu'amalar aure ta haÉ—a ni da shi shekara huÉ—u kenan!"

"Harka ta lalace!"

Zancen Baba Ali kenan, kafin Alƙalin ya yi magana, Mukhtar ya riga shi da cewa,
"Wallahi ranka ya daɗe ko ranar na faɗa maka ba ta yarda da ni, ko na zo ta ba ni haƙƙina sai ta ƙi amincewa da ni. Dalilin haka ma na yi wani aure saboda kullum faɗin take yi; ita ba matata ba ce! Babu aurenmu!"

"To ke saboda me kike hana shi haƙƙinsa? Kuma me ya sa kike faɗar ke ba matarsa ba ce babu aurenku?"

Jikina yana rawa, cikin É—aga murya na ce,
"Ranka ya daɗe tun da na aure shi shekara sha uku bai taɓa gamsar da ni ba. Sannan hannunsa yake aure ba farjina ba!"

Idona a rufe na faɗi maganar, saboda zuciyata ta gama rufewa da takaicin ƙaryata nin da yake yi, bayan ya san gaskiya. Ɗakin ya yi tsit ana sauraron maganar Alƙalin bayan wadda na faɗa.
"Idan na fahimce ki da kyau, tun da yake saduwar aure da ke, ba ki taɓa gamsuwa da alƙalaminsa ba. Haka ne?"
Na É—aga masa kai duk da nauyin maganarsa da na ji a cikin kunnuwana.

"To zancen hannunsa yake aure ba farjinki ba! Me kike nufi da hakan?"

Sai da na goge gumin fuskata, sannan na daidaita natsuwata saboda nauyin faÉ—ar maganar da nake ji a bakina.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.