Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 86
Yana ƙare faɗar hakan ya shige motar shi ya wuce, ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da Firdausi. "MD yana da kirki wallahi. Kuma ko a offis ba ya shiga shirgin mata, shi ya sa ban ji daɗin abin da Mukhtar ya yi masa ba..."
"Allah dai ya kyauta! Amma zargi ba zai bar Mukhtar zama lafiya da ke ba, matuƙar bai sauya hali ba".
Abin hawa muka samu, bayan mun miƙa tafiya na buɗe ledar da MD ya ba ni da zummar ciro wayata, kawai sai ga sabon kwalin waya na hango. Baki buɗe na yi hanzarin faɗin,
"Na shige su!"
Firdausi ma ta kai kallonta ga kwalin wayar tana faÉ—in "Sabuwa ce!"
Cikin sauri na fito da wayar a kwalinta har wani sheƙi take yi, sai kuma ga asalin wayata ƙasan kwalin na gani. Jikina ya hau rawa cike da tsoron abin da zai je ya dawo, saboda har ga Allah na gaji da tashin hankali. Musamman irin wanda zai janyo rikicin da za a ji tsakanina da Mukhtar, sannan ba na son zargin da yake jifa ta da shi a banza mutane suna zagi na.
"Damuwar mi za ki yi a kan abin da ba ki roƙa ba?" Firdausi ta jefo mini tambayar ganin yanayina ya sauya a lokaci ɗaya.
"Halin Mukhtar na sani, a kan wayar nan zai iya janyo mini zagin mutane da ɓacin ran Umma". Na ƙare maganar kamar wata doluwa.
"To ke faɗa masa za ki yi yadda aka yi kika same ta kenan? To bari ki ji, na rantse da Allah muddin ba ki taimaki kanki da kanki ba babu wanda zai ƙwatar miki 'yancinki wurin Mukhtar. Ban ce kada ki mayar wa MD wayar shi ba idan hankalinki bai kwanta ba, amma ki daina ba da ƙofar da zai dinga ɓata miki suna a banza. Haka kawai don shi laifi yana tudu sai ya dinga tsallake na shi yana hango naki domin ya baza wa a faifai yana rabar wa mutane!?"
Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya cike da jin haushi. Shiru kawai na yi ina nazarin maganganunta, cikin sanyin murya na ce,
"Zan mayar masa da wayar shi gaskiya. Saboda ba na son zargin Mukhtar ya tabbata a kanmu..."
Sannu matar Mukhtar🥲
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA TA SHIDA.*
Shiru kawai Firdausi ta yi mini bà tare da ta ce da ni komai ba, har sai da muka je unguwarmu aka ajiye ni sannan muka yi sallama. Fatan samun sauƙi ta yi mini sannan mai adaidaitan ya juya da ita suka wuce. Da tunanin yadda zan mayar wa MD wayar shi a zuciyata na isa bakin ƙofar gidanmu, dole na yi turus ina kallon ƙofar da kwaɗon da ke jiki. Juyawa na yi cike da gajiya na yi gidan Maman Taufiƙ, saboda tabbacin da nake da shi wurinta yara suka kai mini makulli idan na zo na karɓa.
Da sallama na shiga gidan, tsaitsaye muka gaisa na karɓi makullin na fice. Saboda ba na son tsawaita zance a lokacin saboda burin da nake da shi a cikin raina, wanda nake buƙatar sirri ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba.
Ban tsaya falo ba kai-tsaye ɗakina na wuce na zauna kan gado. Ajiye jakar da ke hannuna na yi sannan na fito da ledar wayar da MD ya ba ni, wayata na fara cirowa cikin sauri na kunna. A gaggauce na nemo wayar MD ina ƙoƙarin danna masa kira wani kiran ya shigo wayata. Ganin sunan mai kiran ya sa na yi hanzarin ɗaga wayar,
"Ke matar nan ina kika shige kwana biyu babu ke babu wayarki?" Murmushi na yi kamar a gabanta sannan na ce, "Kwana biyu ina ta fama da jiki, sai yau na samu sararin buÉ—e wayar..."
"Allah Sarki! Ɗazu na zo gidanki domin na duba ki ba kya nan" Ta ƙare maganar muryarta ɗauke da damuwa.
"Ayya! Na je asibiti ne yanzu na dawo gidan". Na ba ta amsa cike da kulawa saboda tuno wace ce ita da matsayin da ta É—auke ni. "Na so na tarad da ke, saboda akwai maganar da nake so mu yi. Amma dai yaushe za ki dawo wurin aiki?"
"Ranar Laraba in Sha Allah zan shigo. Amma idan babu damuwa ki faɗa mini yanzu mana". Na ba ta amsa cikin ƙosawa da son jin abin da za ta faɗa mini, duk da jikina ya ba ni tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Domin ni da ita kusan duk kanwar ja ce sai dai matsalarta ta fi tawa sauƙi linkin.
"Hmmmmm! Na gaji da matsalar Mama, kuma ba na so na yi abin da zai janyo mini wata rigima..."
"Ki yi haƙuri kamar yadda kika saba.Saboda mai haƙuri yana tare da Allah komai daɗewar lokaci, zai kawo miki waraka ta gano gaskiya gaskiya ce da yardar Allah..."
"Mama ta yi nisan da ba ta jin kira, yanzu haka dawowar da na yi na iske ana damun fura a tsakar gidan nan. Amma har aka sha aka shanye daga ni har Yusuf babu wanda aka bai wa. A ganina ko ba mu da haƙƙi za a ba mu ladar ganin ido, sannan abin da kowa ya sani ne ina son fura amma ba su ji kunyar hana muna ita ba, daga ita Mamar har Sadiyar duka. Sannan ko ya dawo na faɗa masa haƙuri kawai zai ba ni. Ƙarshe ma ya bi ni da dogon sharhin ƙarya domin ya kare Mama kada a ga laifinta..." Cikin muryar kuka take magana, kafin na sauke ajiyar zuciya na ce,
"Ki yi haƙuri Amina ki bar su da girman haƙƙin da ke kansu, idan kina buƙatar furar ki saya ki sha ai ba faɗuwa ba ce".
Sautin sharar kukan da take yi a cikin wayar ya kashe mini jiki matuƙa, da lallami na kwantar mata da hankali har ta fahimta, kuma ta sauko daga dokin fushin da ta hau. Sannan muka yi sallama na kashe wayar bayan na tabbatar mata da zan fito aiki ranar Laraba.
Shiru na yi na ɗan lokaci sannan na furzar da iska a bakina, na ƙara lalubo wayar MD na danna masa kira. Sai dai har ta tsinke ba a ɗaga ba, ban gaji ba na sake danna wani kiran, ringing ɗaya biyu aka ɗauka.
"Assalamu alaikum" ita ce sallamar da na yi cikin karyayyar murya.
"Wace ce ke?" Tambayar da aka jefo mini kenan a fusace cikin ɗaga murya, ƙirjina ya buga babu shiri cikin sauri na katse kiran. Saboda muryar macen da na ji hakan ya tabbatar mini da matar shi ta ɗauki wayar. Jikina ya hau rawa musamman kiran da na ga ya shigo wayata ɗauke da sunan MD. Kamar kada na ɗauka, sai dai na yi jarumtar ɗagawa cikin ɗar-ɗar saboda tsoron abin da za ta faɗa mini.
"Me ya haɗa ki da mijina har kike kiran shi a waya?" Shiru na yi saboda ban san me zan ce da ita ba. "Wannan kiran ya zamo na ƙarshe tsakaninki da shi matuƙar kina da sauran son kanki. Domin a kan mijina wallahi babu abin da ba zan yi wa duk 'yar iskar da ta raɓe shi ba. Idan kuma kina ganin faɗa ce kawai nake yi, to ki sake kula shi ki ga yadda zan sa a nemo mini ke a duk inda kike cikin faɗin duniyar nan.." ƙitt ta datse kiran ta bar ni riƙe da waya a hannu na kasa motsin kirki tamkar wadda aka zare wa laka.
Cikin sanyin jiki da na gaɓɓai, na sauke wayar daga kunnena tare da sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. 'Gaba kura baya siyaƙi' zancen da na faɗa kenan cikin raina. Saran da na ji kaina ya yi ya sa na miƙe da nufin ɓoye wayar na ci abinci. Saboda masifaffiyar yunwar da nake ji, na yunƙura kenan saƙo ya shigo wayata. Da sauri na duba saƙon ƙirjina yana bugawa saboda fargaban kada a ce matar MD ce, sai dai na kasa ɗauke idona daga kan allon wayar saboda saƙon da nake ta maimaicin karatun shi a zuciyata.
'Ki yi haƙuri Zaituna. Na shiga wanka ne ban san kin kira ba. Me ke faruwa ne?'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.