Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 47 of 86

'Sai kin tsufa yaranki za su yi miki amfani idan ciwon hawan jini ya kama ki, a lokacin za su dinga zaryar kai ki asibiti ana rubuto miki magunguna wani bayan wani.'

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Ita ce kalmar da ta fito daga bakina ban shirya ba,
'Idan kuwa har haka ƙarshen haƙurin da na yi zai kai ni. To rayuwar da nake yi a yanzu ba ta da wani amfani ko kaɗan, matuƙar ƙarshe na ya zo a ɗawainiyar kai ni asibiti. Domin a yi ta jera mini takardun maganin hawan jini, yarana su sha wahalar kai-da-komo da ni a tsakanin gida da asibiti.'

Amsar da na bai wa kaina kenan a zuciya kamar yadda zuciyar ce ta kitsa mini komai.
''Ya zama dole na yi wata hoɓɓasa, tun kafin wankin hula ya kai ni dare"
"Komai za ka yi yanzu, aikin gama ya gama sai haƙuri. Kuma zama da ni yanzu kika fara, don wallahi babu wata kotu ko alaƙalin da zai sakin ki ba tare da amincewa ta ba. Yadda muka fara rayuwa tare haka za mu ƙare ta, saboda babu ɗan iskan ƙaton da zan bari ya aure ki bayan ya gama bibiyarki da aurena, ba tare da ya yi duba da illar ɗaukar wa kansa kaya a dalilin auren da ke saman kanki ba."
Maganar Mukhtar kenan a kaina yana huci tamkar ya dake ni, da kallon mamaki na bi shi baki a sake. Saboda ƙoƙarin datse mini farincikin rayuwa da yake yi koyaushe. A bahagon tunaninsa wannan barazanar da yake yi ce take hana ni ɗaukar wa kaina matakin gaggawa.
Ajiyar zuciya na sauke sannan na yi dariya a matsayin tura masa haushi na ce,
"Maimakon tsoro ko fargaban da kake ƙoƙarin cusa mini a zuciya, sai maganganunka suka dawo ba ni dariya haiƙan. Wai kai a tunanin da kanka yake ba ka burgarka ce take riƙe da ni a gidanka? To ka yi kuskure kuma ka saɓa lamba. Kamar yadda na sha faɗa yanzu ma zan maimaita; neman gamawa lafiya da rabuwa da mahaifiyata cikin aminci; ya sa ba na zartar da hukuncin da nake yanke wa kuturun aurenka, a kowace daƙiƙa da bugun numfashina. Ka gode wa Allah ko lahira wani yana cin albarkacin wani; kamar yadda kake cin na 'ya'yanka a wurin Ummata yanzu, duk da kai ko kaɗan ba ka san zafinsu ba. Amma idan tani ake bi abin da ka sani ne zan maimata yanzu ka ji, idan ana saki dubu duka sai na katse igiyoyin har ma nemi ƙarin wasu na daddatsa."

A fusace ya yi kaina zai kai mini duka, na yi hanzarin ja baya tare da nuna shi da hannu ina cewa,
"Kul! Kada ka yi gangancin taɓa ni ka janyo na yi maka aika-aika yanzun nan. Na fi so na je gidan kaso da na bari ka dake ni ka hana ni kokawa, domin mari da tsinka jakar da kake yi mini kullum ba don ba na iya ramawa ba ne nake ƙyalewa. Idan ka kai ni bango kuma zan nuna maka na fi ka zama 'yar tarawi."

"Idan ma kin ce za ki rama ai ke ce a wahale, domin aurena ne ba kya so kuma ba zan taɓa sakinki ba."

Yana ƙare faɗar hakan a fusace ya bar wurin zai fice falon, na biyo shi a zafafe ina faɗin, "In dai wannan baƙin auren kake taƙama da shi ka faɗo. Don tuni ya lalace babu komai a cikinsa face kwasar zunubai."

"A hakan kuma za ki zauna ko kina so ko ba kya so!"
Abin da ya faɗa kenan ya fice gidan, tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ƙirjina ya buga sanadin sautin ƙarar ƙofar,

'Garam!!!'

Dawowa na yi na zauna, zuciyata sai hawa da sauka take yi ina fisgar numfashina da ƙarfi. Na ɗauki lokaci a haka sannan na fara jin sallamar wasu mata a bakin ƙofar falon.
Na fito ina amsa sallamar idona a kansu, tunanin inda na san su a raina na yi amma na kasa.

"Dangin amarya ne, mun zo duba É—aki."

"Allah Sarki to ku shigo mana!"

Na ƙare maganar cikin sakin fuska da murmushin yaƙe na yi gaba, suka bi ni a baya na ja na tsaya a bakin ƙofar ɗakin. Da fara'ata a kan fuska na ce da su,
"Ku jira na karɓo muku makullin ɗakin a wurinsa."
"Ai shi ya ce mu shigo, ga makullin a nan ya ba mu."
"FaÉ—uwa ta zo daidai da zama, yanzu yake sanar da ni zai ba ni na ajiye muku kafin ya fita."
Maganar da na yi kenan ina 'yar dariya, a ƙoƙarin kore damuwar da ke kan fuskata.
"An hutar da ke ai tun da ya ba mu!"

Wata matashiya daga cikinsu ta faɗa cikin haɗe rai tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, ɗakina na nufa zuciyata tana tafasa saboda duka biyun da yake ƙoƙarin hawa kaina. Tsakanin rashin mutuncin da Mukhtar ya yi mini da rainin hankalin da dangin amaryarsa suke ƙoƙarin kawo mini.
Wanka na faÉ—a shaf-shaf na dirje jikina, cike da jin haushin bai sanar da ni zuwansu ba. Da ban bari suka same ni a yadda nake ban cancanÉ—a kwalliya ba.
Ƙwafa na yi kawai tare da cije leɓen ƙasa a lokacin da na gama shafa hoda sama-sama. Wata doguwar rigar atamfata na saka fited gawn, kuma mai fitting ɗina sosai a duk lokacin da na saka. Turaruka nake fesawa ina jiyo sautin muryoyinsu suna yaba tsarin falon.
A daidai lokacin da suka shiga kitchen na fito na kunna tv sannan na zauna kan kujera ina kallo. Duk da ba na gane komai amma ban É—auke idona daga kan tv'n ba jefi-jefi na latsa wayata.
Sun É—auki minti sha biyar a kitchen É—in, suna ta maganganun da ba na tantance abin da suke faÉ—a. Sannan suka fito daga Kitchen É—in suna faÉ—in,
"Ma sha Allah wuri ya yi kyau! Sai fatan Allah ya ba da zaman lafiya da ƙazantar ɗaki."

Kaina na É—ago daga latsar wayar da nake yi na ce da su, "Amin, har kun gama?"
Wasu biyu suka wuce suna faÉ—in
"E, mu za mu tafi."
Yayin da wasu masu hankalin cikinsu uku suka ce, "Mun kammala, gobe idan Allah ya kai mu za mu zo a yi jere. Allah ya ba ku zaman lafiya da haƙuri da juna."

Da murmushi a kan fuskata na ce da su, "Amin-amin." Suka nufi hanyar fita na rako su ina yi musu godiya da Allah ya tsare.
Sai da suka fice gidan sannan na rufo ƙofar na juyo zuciyata a cunkushe da takaicin Mukhtar. Don da ya faɗa mini za su zo, dole ne a tanadar musu wani abu, saboda babu daɗi su tafi hannu rabbana ba a ba su komai ba.
Ko zama ban yi ba Maman TaufiÆ™ ta shigo na tarbe ta da fara'a muka zauna. Kallon tsarin falon ta shiga yi da kujeruna da muke kai, fuskarta a sake ta ce da ni,
"Kujerun nan sun yi mini kyau Maman Haidar!"
"Na gode" Na faÉ—a cike da murmushin da ya kasa barin fuskata. Zamanta ta gyara tana faÉ—in,
"Wasu mata na gani sun fito daga gidan nan suna ta yabonki. Kuma jikina ya ba ni kamar dangin amaryarsu ne?"
"E, su ne. Sun zo duba É—akin amarya da tsarin gidan."
"CabÉ—ijam! Lalle kin fara aika musu makaman nuclear. Domin kuwa da kunnena na ji wata yarinya daga cikinsu tana faÉ—in"
'Ni fa haushi ya hana ni tsayawa na fito gidan. Don wannan haÉ—aÉ—É—iyar mata ko ni aka haÉ—a kishi da ita an cuce ni balle Barira. CabÉ—i! Na tausaya wa mata gaskiya, don ta kawo kanta inda za a ga kasawarta'
'Idan ban da ma hali irin na maza da ba a iya musu; mai irin wannan zankaÉ—eÉ—iyar macen ne zai auri Barira?'
'Shi aure ai nufi ne na Allah! Ita ce matarsa shi ya sa ya nemo ta. Don haka ku zo mu je mu bi su da addu'ar zaman lafiya, saboda alamu ya nuna a fili ta yi sa'ar kishiyar da babu ruwanta'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.