Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 59 of 86

***
Daren ranar ban yi bacci mai daɗi ba, hakan ya sa safiyar Litinin ta waye mini babu kuzari, na ji kamar kada na fita wurin aiki. Ƙarfafa kaina na yi dole na shirya tare da su Ummu Salma, da ke nasu shirin zuwa makaranta.
Sai dai inda gizon ke saƙar babu komai na kalacin safiya a kitchen, domin alamu ya nuna Barira ba ta fito ba ma balle ta girka mana. Haushi ya sa na yi mana boiling ruwa na jefa Indomie ta jiƙa, a gurguje na saka mana mai da yaji.
Nan take muka lamushe saboda mun daÉ—e ba mu ci ta a hakan ba ta yi mana daÉ—i sosai. Kiran da Najib ya mini a waya ya sa muka fito tare da su duka za mu fice.
"Ai wallahi ba zan girka komai ba a gidan nan don ba boyar kowa nake ba."

Maganar da Barira ta yi kenan tana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinta Mukhtar yana bayanta. Turus ta yi a lokacin da ta gan mu ni da yaran za mu fice,
"Aunty ina za ku je ba ku karya ba?"

Kallo ma ba ta ishe ni ba daga ni har yaran muka fice ba tare da mun tanka su ba dukansu. Muna ƙoƙarin shiga adaidaitar Mukhtar ya iso wurin yana faɗin,
"Yanzu abin naki har ya kai ki hana yarana su gaishe ni?"

"Ina kwana?"

Ita ce gaisuwar da Najib mai adaidaita ya yi wa Mukhtar yana sosa ƙeya, ni kam kallo ma bai ishe ni ba illa umurnin da na bai wa Najib,

"Mu tafi ka ji!?"

Ya buga adaidaitarsa ya tafi muka bar Mukhtar a nan tsaye yana kallon mu.

'Dole na canza tsari'

Zancen zucin da na yi kenan saboda ganin tsarin da na É—auka a kan girki, ba zai haifa mini É—a mai ido ba. Domin ni da 'ya'yana ne za mu tagayyara, ita da shi ko a jikinsu mu ne a wahala. Na tsayu a kan ci gaba da girkina daga ni sai yarana, tun da ba wani amfani yake yi mini ba ba zan jira ta yi girkin kwanakinta na yi nawa ba.

'Zan fita sabgarsu duka, kuma zan dinga abincina daga ni sai 'ya'yana.'

Tunanin da na yi kenan a cikin zancen zuci, na sauke ajiyar zuciya sannan na ce da Ummu Salma. Idan suka dawo ta yi mana abinci kamar yadda take yi kafin zuwan Barira, kuma kada su yi abin da zai janyo rikici a dake su a banza.

Bayan an ajiye ni na fara taku a hankali zuciyata cike da tunanin abin da zai faru, idan sun dawo ba na gidan. Gaisawa na yi da mutane suna yi mini ya jiki ina amswa har na isa offis É—ina.
Key na saka na buɗe sannan na shiga da sallama a maƙoshina. Kujerun na kakkaɓe sannan na share Ofishin tas na goge, saboda ƙurar da ya yi tsawon kwanakin da ban zo ba. Ga shi makullin yana hannuna na mance ban bai wa Amina ba a lokacin bikin.
Zama na yi ina sauke numfashi sai ga ɗaya daga cikin masu shararmu ta ƙwanƙwasa mini ƙofa. Umurni kawai na bayar a kan a shigo ta fara gaishe ni na amsa mata a mutunce.

"Hajiya shara za a yi!"

"Ki je kawai Inna har na share!"
"Allah ya saka miki da alheri ya ƙara duba gabanki da bayanki."

"Amin." Na faÉ—a zuciyata a sake saboda na ji daÉ—in addu'ar sosai. Fitar ta ke da wuya wani masinja ya zo yana faÉ—in,
"Ranki shi daÉ—e Oga yana kiran ki."

"Ok!" Ita ce iya maganar da na yi ya fice na miƙe ina kakkaɓe ƙurar da ta ƙi sakin jikina, sannan na nufi ofishin fuskata a haɗe ƙirjina yana bugawa.

Sallama na yi cikin siririyar murya ya amsa mini a gadarance tamkar ba ya so. Takardu na gani a gansa tsibi guda da hannu ya yi mini nuni da su a kan na É—auka. Harara na wurga wa kwantaccen gashin kansa da ya sha gyara, saboda haushin izzar da yake ji da ita a lokacin.

ÆŠauka na yi kawai ba tare da na ce da shi komai ba na nufi hanyar fita.
"Ya hidimar bikin? Fatan Allah ya ba da zaman lafiya."

"Amin" Kawai na faɗa na fice, tunanin ƙara yi masa godiya ya faɗo mini a rai na koma. Bakin ƙofar na tsaya ina faɗin,
"Na gode sosai a kan kyautar da ka yi mini. Allah ya ƙara rufa asiri."

Bai ce da ni komai ba, har sai da na juya na ji ya ce, "Amin" can cikin maƙoshinsa. Raina a haɗe na fito ina gungunin da ban san me nake ta faɗa ba.
Saboda sauyin da ya yi mini sosai yake taɓa mini zuciya, saɓanin baya da yake faram-faram da ni, duk da ba ya sakewa sosai ina yabon kirkinsa da Amina. Amma tun daga kan abin da Mukhtar ya yi masa ya daina sake mini fuska, musamman lokacin rikici na da su Ummita har tsawa yake daka mini tamkar ya dake ni.

Ban ɓata lokaci ba na fara aikina gadan-gadan, Amina ta shigo muna hira ina aikin har lokacin tashi ya yi. Tare muka miƙa wa MD takardun muka fito tana cewa,
"Wai ina amarya? Na manta ban tambaye ki ba."
"Amarya tana gidan mijinta. Sauri nake yi ma na koma saboda ba na so yaran su yi mata ba daidai ba. Don na fahimci ita ma rawar kanta ya fi ta yawa."

Dariya Amina ta yi sannan ta ce, "Ganin take yi karanta ya kai tsaiko. Tun da ta haÉ—a kishi da mace mai halin kirki da nagarta irin taki. Don wallahi ba don ke ta samu ba; da sai ta gane barno gabas take a yadda na gan ta wata jagwal tamkar sandar makafi."
Ajiyar zuciya na yi ina tare wata adaidaita na ce, "Ki bari kawai! Nan da kike ganin ta ba ba ƙaramar 'yar hannu ba ce."
"A hakan?"

"Tabbas! Ke dai kin ga mutum!"

Da haka na tafi muna ɗaga wa juna hannu. Zuciyata cike da tunanin su Ummu Salma har aka ajiye ni ƙofar gidan. Tun da na jefa ƙafafuwana cikin gidan na fara jin sautin kukan Ummu Salma. Da sassarfa na shiga falon idona a kan Ummu Salmar da ke rakuɓe jikin gini tana cisgar kuka har da shessheka.

'Me nake shirin gani?'

Wata sabuwa🤔 wa ya taɓa mana Ummu Salma ne haka?😢

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*TALATIN DA BIYAR .*

"Lafiya!? Me ya same ki!?"
Abin da na fara faÉ—a kenan a hargitse tun kafin na isa inda take. Tana gani na da ta tarye ni da gudu ta faÉ—a jikina, tare da rushewa da wani sabon kukan ya sa jikina kyarma.
Domin ko ni rabon da na saka hannu na dake ta har na manta, saboda tana ƙoƙarin barin abin da duk ta san ba na so, balle ta yin abin da zan dake ta a kansa. Haidar ne kawai yake shan duka a wurina, don ko Iman miskilancinta kawai yake sa na dake ta idan na saka ta aiki tana jan jiki.
Jikina na ɓanɓare ta ina faɗin, "Faɗa mini me ya faru?" Cikin shesshekar kuka ta ce, "Abbanmu ya dake ni"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.