Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 37 of 86
"Ki yi haƙuri ki yafe mini, saboda na san na yi miki laifin da na cancanci duk wani hukunci daga gare ki. Amma don alfarmar Ubangiji da darajar Manzonmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ki yafe mini. Ta wannan hanya ce kaɗai idan kin yafe mini zan iya ba ki labarin dalilin da ya sa na sayar da kayan nan, wanda ko ke kika ji za ki iya ba ni da kanki ki ce na sayar domin daga ni har ke cigaban namu ne. Don haka don Allah ki yafe mini ba don halina ba, saboda matsin da na shiga wurin nemo mafita ya sa na sayar da kayan nan. Kuma na tabbatar da idan kika ji za ki amince da kanki ki ce na je na sayar domin mu rufa wa kanmu asiri."
_Jikina ya yi sanyi ƙalau! Saboda maganganun shi sun shiga jikina, kuma ratsa zuciyata sosai. Saboda idan akwai abin da ba na iya kaucewa a duniya, shi ne a haɗa ni da Allah a kan abu. Komai hawan da na yi sai na sauko saboda ba na kauce tayin alfarmar da duk aka haɗa ni da roƙon Allah. Sai dai kuma zama da shi ya fice mini a rai, duk da na ƙudurta yafe masa laifin kamar yadda ya roƙa. Tsayuwata na gyara, sannan na sauke hannuna ƙasa daga rungumar da na yi musu a ƙirji, tare da kawar da kaina gefe bayan na riƙe ƙugu na ce da shi,_
"Zan yafe maka kamar yadda ka roƙa, amma sai ka yi mini alƙawarin za ka yi abin da zan nema daga gare ka. Saboda zuciyata ba za ta taɓa yarda da kai a matsayin miji ba, ka sauwaƙe mini kawai cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya sani ba. Ni kuma na yi maka alƙawarin zan yafe maka duk kayan da ka salwanta mini. Don haka ka ba ni takardata yanzun nan gobe idan Allah ya kai mu lafiya na koma inda na fito. Kuma komai za a yi ba zan fasa wannan ƙwan ba balle wani ya ji warinsa, amma fa idan ka sallame ni cikin mutunci ba tare da wani ya ji ko ya sani ba. Domin Wallahi ba zan iya zama da miji irinka ba."
"Don Allah! Don girman Allah ki yafe mini Zaituna! Wallahi ba zan iya sakinki ba ko da za a ɗora mini wuƙa a wuya."
_Ya ƙare maganar tare da riƙo hannuna yana cisgar kuka tamkar zai shiɗe. Ƙwace hannuna na yi sannan na tura shi ya faɗi ta baya, saboda tsabar takaicin da ya ba ni. Amma hakan bai hana shi furta mini cewa,_
"Gara kawai ki yi mini duk abin da kike so a matsayin huce haushin laifin da na yi miki, idan ma dukana za ki yi na shirya karɓar hukuncin kowane irin duka daga gare ki, amma ba zan taɓa yafe wa kaina ba muddin na yi abin da kike so. Na fi so na mutu, ko kuma duniya ta Allah-wadai da ni, a kan abin da na yi miki da a ce na sake ki."
Uhumm! Maza mutanenmu😊
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ASHIRIN DA UKU.*
_Kallon takaici nake aika masa ta gefen idona, hawaye yana zarya a kan dandamalin fuskata. Duk da maganganun shi sun saka zuciyata rauni, sannan kukan da yake sha tamkar wani ƙaramin yaro, ya saka ni jin lalle akwai babban dalilin da ya sa shi sayar mini da kaya dole. Tsayuwata na gyara tare da zuƙe majinar kuka na ce,_
"Me ka yi da kuÉ—in kayan? Sannan wace lalura ce ta janyo ka salwantar mini da kaya ba tare da sani na ko na Iyayena ba?"
_Miƙewa ya yi daga durƙushen da ya yi, ya iso inda nake ya riƙo hannuna. Ya zaunar da ni bakin gefen ƙwalluwar katifar da ta yi saura a cikin ɗakin, shi ma ya zauna tare da rungume ni jikin shi yana share mini hawayen da suka kasa tsayawa a kwarmin idona. Sannan ya goge na shi da gefen hannunsa, tare da kama hannuwana duka biyu ya riƙe gam-gam! Kamar wanda yake gudun na tsere masa._
"Na san ban kyauta ba saboda ban yi shawara da ke ba kafin na zartar da hukunci. Amma ki sani wallahi Allah ya sani ban da wata mafita ne shi ya sa na yi hakan."
_Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya sake cewa,_ "Kamar yadda kika sani, wurin da nake aiki ba wani albashin kirki ake ba ni ba. Saboda matsayin ajiya nake yi a wurin har zuwa lokacin da zan ƙara karatu, domin a ba ni gurbi mai kyau da karatun da zan ƙaro idan na gama. Shugaban wurin namu ya uzzura mini a kan ko na ƙaro karatuna, ko kuma su canza ni da wani mai manyan takardu.
Dalilin da ya sa na shiga neman kuɗin registration kenan ido rufe, lungu da saƙo kusufa-kusufa a cikin faɗin garin nan ban samu ko dubu biyar ba. Har na gaji da gantalin neman bashi ga shi taimako ya yi ƙaranci ga mutane yanzu. Ga kuma karatun yana buƙatar kuɗi masu ɗan kaurin da zai wadata, kuma ana saura ƙiris a rufe sayar da foam ɗin a lokacin. Wannan dalilin ya sa na shiga damuwa tare da neman ta wace hanya zan samu kuɗin nan, saboda tsoron na rasa aikin kuma na zo mu rasa ya za mu yi ni da ke a cikin gidan nan. Tunanin sayar da firij da telarki ya zo mini, shi ne ya sa har na kira ki a lokacin na yi miki zancen. Duk da kin nuna kada na taɓa dole ta sa na sayar da su, sai dai abin haushin kuɗin ba su kai ko rabin na registration ɗin ba. Tunanin na haɗa da kayan gadonki ya faɗo mini, da nufin duk lokacin da na samu sarari na saya miki wasu idan buƙata ta biya.
Dalilin da ya sa na saka su kasuwa kenan domin mu samu abin da za mu rufa wa kanmu asiri. Shi ne na sayar da kayan na yi kuÉ—in registration, amma ki kwantar da hankalinki in sha Allah cikin kwanan nan zan saya miki wasu. Saboda ba zaune nake ba akwai buge-bugen da nake yi, idan Allah ya saka mana hannu komai zai wadata gare mu da yardar Allah."
_Shiru ya ratsa tsakani bayan dire maganganun shi, na shiga nazarin dalilin da ya janyo kayana suka salwanta. Sai dai ni a nawa hangen da ya yi shawara da ni, da ban ji rabin zafin da na ji yanzu ba. Saboda ni kaina ina buƙatar cigabansa, kuma ina fatar ya samu rufin asirin da zai riƙa ni ni da jinjirar 'yata Ummu Salma. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce da shi,_
"Tabbas! Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Amma da ka yi shawara da ni tun farko ba za a rasa yadda za a yi ba, domin ina da tabbacin zan samo nama kuɗin registration ɗin ba tare da an taɓa kayana ba. Saboda ni yanzu ban san da wane baki zan yi wa su Umma bayanin yadda kayan suka yi b..."
"Ni ma ba na son ki yi musu bayani, don Allah ki bar zancen nan a tsakanina da ke ba tare da kowa ya sani ba. In da hali ma ki nuna kawai ni da ke ba mu san yadda suka yi ba, idan ta kama ma za mu ce ɓarayi ne suka sace a lokacin da ba na garin. Don Allah ki yi mini alƙawarin ba za ki tona cikin wannan magana ga kowa ba, har da Umma don Allah kada ki bari ta san gaskiyar maganar nan!."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.