Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 29 of 86

Dariya muka saka a tare sannan na jingina bayana jikin kujera ina É—an juyawa a hankali. Murmushi É—auke a kan fuskata na ce da ita, "A ina muka tsaya da labarin? Don na san kin fi ni sanin inda za mu tashi."
Zama ta gyara sannan ta ce, "Abu mai sauƙi cire wando ta kai, mun tsaya ne a daidai inda cikinki ya kai wata tara haihuwa yau ko gobe. A lokacin da Abban su Ummu ya yi miki laifin da ya so katse igiyoyin aurenku."
"Madallah da ke, don ni haddar kaina ta daÉ—e da gogewa."
Shiru na yi ina nazarin abubuwan da suka faru a lokacin, sannan na yi murmushin da iyakacin shi leɓe tare da sauke ajiyar zuciya na ɗora daga inda na tsaya.

_EDD na yana cika na ce da shi ya bari na koma wurin Ummata, saboda koyaushe zan iya haihuwa amma ya nuna ba zan je ba har sai na haifu. Domin ita kanta Ummar ta so a mayar da ni wurinta na haifu gabanta, amma babu kunya ya nuna ya fi so sai na haifu gidansa. Ba ta ja da tsauri ba ta bar maganar saboda ya fito ƙarara ya nuna ba ya so._
_Duk da girmama al'ada irin ta Sakkwatawa haka ta haƙura, domin abu ne wanda kowa ya sani haihuwar farko a gida yarinya take yi. Wani lokaci ma da wuri ake komawa a yi ta dakon zuwan haihuwar._

_Ranar da zan haifu, tun cikin dare na fara naƙuda, amma ban da bacci babu abin da yake yi. Sai idan na ji azaba ta yi mini yawa na ƙwala masa kira ya tashi yana jera mini sannu. Da ƙyar na ga asuba, zuwa lokacin na galabaita sosai ta yadda ko magana ba na iya yi. Ko da 'yan gidansu suka zo ban san lokacin da suka kai ni asibiti ba, saboda jinin da ya fara zubar mini ya sa na cire rai da duniya balle ganin abin da zan haifa._
_A gurguje aka karɓe ni cikin sauri aka yi labor room da ni, a saman gadon ɗaukar marasa lafiya jini yana ta bin jikina. Cikin ikon Allah har an fara zancen yi minti aiki sai ga yarinya ta kunno kai. Nan take na haifo 'yata ba tare da cikina ya sha askar likitoci ba._
_Bayan na samu kaina na ga an kimtsa ni tare da abin da na haifa. Ummata na fara gani sannan Inna Kulu da sauran 'yan gidansu Mukhtar, har da ƙawata Hafsa waton ɗiyar maƙocin Kawu Sale da muke kai ɗaya a nan Bafarawa Estate. Murmushi na bi kowa da shi cike da jin daɗin ganin kyautar da Allah ya ba ni. Mamaki fal raina tare da bin Mukhtar da kallo saboda ganin wasar bakin da yake yi, wanda alamu ya nuna fili ya yi farincikin da samun Bbyn. A raina na ce 'Ashe dai ana so ake kai wa kasuwa.'_
_Kwanana ɗaya Asibitin ana ƙara mini jini, saboda jinina ya yi zubar da dole sai an ƙara mini da wani. Da dare aka sallame ni muka yi tsinke sai gidan Kawu Sale, a nan ma mutane suka fara tururuwar zuwa gani na tsakanin 'yan'uwa da abokan arziƙi._
_Kwana huÉ—u da haihuwa 'yan gidansu Mukhtar suka kawo mana kayan fitar suna, kayan da suka janyo mana ce-ce-ku-cen mutane. Domin kala uku ce da kayan jarirai biyar sai wasu tarkacen da rashin su ya fi kawo su rana. saboda ba a kawo sauran kayan da Sakkwatawa suka mayar tamkar ibada ba. Domin babu kayan yajin da suka daÉ—e da camfi kansu, a kan duk maijegon da ba a ba ta su ba, ko lahira sai an biya ta su a gaban Allah. Surutun mutane ya sa Umma ta je kasuwa da kanta ta siyo tare da wasu kayan da ya dace a ce Mukhtar ne ya kawo su._
_Ana gobe suna mutanen Kebbi suka zo, farinciki fal raina saboda ganin babbar ƙawata Asma'u. Wadda muka yi karatu tare tun daga matakin primary har zuwa Sakandire, ko a Jami'a mun yi makaranta ɗaya sai dai kowa da ɓangaren da ya karanta. Akwai shaƙuwa sosai a tsakanina da ita, irin wadda kowa ya san ta zai san ni, haka ma wanda duk ya san ni ya san ta a baki ko a zahiri, saboda ƙarfin abotarmu._
_Ranar suna aka raɗa wa yarinya Ummu Salma, an sha hidima sosai komai a wadace ma Sha Allah, saboda ƙoƙarin Ummata da Baba Sale har ma da Baba Ali. Domin sun yi namijin ƙoƙari wurin fitar da ni kunyar 'yan biki, saboda ɓangaren abinci da abin sha Alhmdulillah har rara aka yi da dare. Domin girka abincin ake yi wani kan wani, sai da sawun mutane ya ɗauke aka dawo jinyar jiki._
_Da safe aka fara rabon tsokar abin sunan kusufa-kusufa lungu da saƙo. Saboda babu laifi Mukhtar ya yi abin kai gida, domin dabba biyu ya yanka amma sai da Umma ta dawo siyen ƙaramar tunkiya saboda mutanen kunyar da ba su samu ba._
_Yan Kebbi kuma suna gama sallar zuhur suka fara sallama da mutanen gida. Don daman can sun haɗa kayan tafiya tun da sake aka dakatar da su domin a ba su nasu kaso. Sai da suka soye namansu sannan suka yi haramar tafiya, har raina ban so tafiyar Asma'u ba. Na so a ce ta zauna amma ta nuna mini wannan tafiyar da da ƙyar aka bar ta, saboda Babansu mutum ne mai tsattsauran ra'ayi da masifar faɗa tamkar ya ci babu. Amma ni duk da faɗan shi Allah ya haɗa jinina da shi sosai yake mutunta abotarmu._

_Sai da suka isa gida sannan hankalina ya kwanta, domin lokaci bayan lokaci ina kiran su na ji sun isa ko suna kan hanya._

_Na ci gaba da zaman jego a gidan Kawu Sale har yi arba'in, sannan na tafi Kebbi cike da jin daɗin ganin Baba Ali da sauran 'yan'uwa da abokan arziƙin da aka yi zaman mutunci. Satina biyu a can na dawo saboda matsin lambar Umma da Kawu Sale suke yi mini, a kan na dawo haka nan na koma gidan mijina. Sai dai su abin ba su sani ba, koyaushe muna waya da shi, amma bai damu da sai na dawon ba. Bayan wata tambayar da ya yi mini wadda ta sa na kasa tantance ina zancen shi ya dosa. Domin a lokacin da muka gama waya da Umma a kan dawowar sai ga kiran shi, na dauka cike da tunanin shi ma zancen da zai yi mini kenan. Sai ga shi na ji sabanin abin da zuciyata ta zata._
"Telar nan taki da firij. Kina so a sayar miki da su kafin ki dawo?"
"Kada a sayar domin idan na dawo zan fara koyon ɗinki, kuma zan dinga yin zoɓo da ƙanƙarar zaƙi na san yaran unguwar za su saya."
"To" _Kawai ya ce sannan ya katse kiran, bayan mintina kaÉ—an ya sake kira yana yi mini gargaÉ—i a fakaice._
"Yawwa! Ki bar zancen nan a tsakaninmu ba sai kin faÉ—a wa kowa ba."
_Murmushi kawai na yi masa sannan na ce,_ "Wannan maganar ai ba ta kai na yi yamaÉ—iÉ—i da ita ba."
_Daga haka muka yi sallama tare da sanar da shi gobe zan koma Sokoto, sai dai ban ji ya yi murna ba balle ya yi zumuÉ—in dawowar ta yadda zan gane._

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.