Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 61 of 86

"Wai ke wace irin mace ce da ba ki ƙulla alheri sai sharri!?"

"Koya na yi a wurinka!"

Na faÉ—a kaina tsaye ina ci gaba da shafa mai, ba tare da na kai idanuwana inda yake ba.
"Ni duk abuna, ban taɓa hana sunnar ma'aiki ba! Ke kuma ƙiri-ƙiri kina ƙoƙarin hana abin da Allah ya halasta. Don kin ga yarinya tana jin maganarki shi ne kika hure mata kunne a kan abin da take so. To ta Allah ba taki ba wallahi! Don aure ne ko kin ƙi idan Allah ya nufa za ki ji kunya."
"Shi kuma wannan soki-burutsun daga ina ya fito? Da kake tayar da jijiyoyin wuya kamar wani zautacce!"

"Da komai ma za ki iya siffanta ni da shi don ba yau kika fara ba, amma auren Sajida da Malam Aminu kamar an yi an gama ne! Ki so ko kada ki so duk É—aya don babu haÉ—in dangin iya ke da ita balle na Baba. Saboda tun kafin ya je wurinta sai da ya fara yi mini zancen, kuma Ni na ba shi lambarta da hannuna saboda na gamsu da haÉ—insu. Don haka kin yi kaÉ—an ki hana sunnar ma'aiki a kan wani guntun dalilinki na banza."
"Wannan kuma ku ta shafa babu ni a ciki. Amma duk wanda ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba."

Zancen da na gama faÉ—a kenan ina saka kayana, saboda mamakin yadda aka yi maganar ta fito. Da kuma wanda ya faÉ—a masa ni ce na hana Sajida kula Baban TaufiÆ™.

"Don girman Allah ki ce da ita idan aka kai Sajida kada ta bar ta da rai ta kashe ta tun a daren farko!"
Maganar da ya faÉ—a kenan a fusace yana nuna ni da hannu tamkar ya tsokale mini ido.
"Ohon muku! Ko a jikina, don babu ni a cikin kashin balle na kwasa." Na yi maganar tare da ɗora haƙarƙarina a kan gado. Saboda jikina ko'ina ciwo yake yi mini duk da wankan da na yi.

"Na dai faÉ—a miki daga yau ki zare hannunki a cikin auren nan!"
"Ummhh! Kanka ake ji!"
Data ta na kunna ina duba saƙonni har ya gama bambamin da yake yi ya fice. Zuciyata cike da tunanin abin da ya janyo maganar har aka saka ni ciki. Don na san Sajida ba za ta faɗi yadda muka yi da ita ba.
Kasa haƙura na yi har sai da na kira ta a waya, raina babu daɗi na ce da ita,
"Ya kuka yi da Baban TaufiÆ™?"
'Wallahi Aunty na faÉ—a masa gaskiya. Kuma ya aminta da zancen har mun yi sallama da shi a kan ya janye. Me ya faru halan?'

"Mukhtar ne ya zo yana wasu surutan da ban san ina ya jiyo su ba, wai na hure miki kunne komai na ƙi idan Allah ya nufa zan ji kunya."

'Gaske na ji suna waya da Mama tana ta faɗa. Ashe zancen ne yake faɗa mata. To wallahi wannan munafukar matar tasa ce ta faɗa masa yadda muka yi ni da ke. Saboda lokacin da muke yin maganar tana falon har ta yi waƙa.'

"Eeeee! Tabbas ita ce! Domin kuwa biri ya yi kama da mutum!"

'Ki bar ta kawai Aunty! Zan zo har gidan na ci uban shegiya. Ba ta san daman can haushin ta nake ji ba.'

"Ki ƙyale ta kawai da ni take zancen! Da sannu sai na koya mata hankali a cikin gidan nan."

'Ke da wa kike waya? Idan mai hure miki kunnen ce ki faÉ—a mata na ce; ta Allah ba tata ba wallahi...Ni dai Mama don Allah ki san me kike faÉ—a haka kawa....'

Tsinke kiran kawai na yi tare da sauke ajiyar zuciya, saboda zancen Yaya Maimuna ba ƙaramin ƙona mini rai ya yi ba. Duk da daman can na san tana adawa da ni tun lokacin da na tuɓure, a kan ba na son zama da Mukhtar sai ya sake ni. Tun daga lokacin ko gaishe ta na yi sai ta nuna mini zallar ƙiyayyar da take yi mini. Bayan zagi da cin zarafin da take yi mini a bayan idona suna dawo mini.

Kwance nake kan gadon ina ta juya abin cikin raina, tare da rikicin da za a yi muddin Maman TaufiÆ™ ta san da labarin. Har su Ummu Salma suka dawo ban tashi daga kwanciyar ba, ba su jima da shigowa ba aka yi kiran sallar magrib.
Saboda punishment É—in da aka ba su makaranta a kan lattin da suka yi. Iman sai ajiyar zuciya take yi saboda tambon bulolin da suka sha sun fito raÉ—au a tsintsiyar hannunta.
Da ƙyar na shawo kanta ta daina kukan, don daman can ita raguwa ce. Ko kaɗan aka taɓa lafiyar jikinta sai ta yi raki balle an saka bulala an dake ta.

Sai da muka yi sallah dukanmu, sannan muka zauna zaman cin abinci ni da su a cikin ɗakin. Bayan sallar Isha muka koma falo muna kallo, Barira ma tana ta wayoyinta da mutane tana shewa. Bayan zagin da take kamfatowa iri-iri tana sauke wa ƙawayenta.

"Ke shegiya! Gobe ki zo akwai sabuwar chepter...Sosai ma ke dai ki zo kawai akwai labarai...Yawwa 'yar gari ki zo da kayan duka mu É—an kora an kwana biyu ba a haÉ—u ba."

Maganganunta sun saka jikina sanyi, saboda tunanin yarana da za su dawo ba na gidan. Kai-tsaye wata sabuwar idea ta zo mini, na yanke hukuncin tura su wurin Ummata goben. Gudun na taras da tashin hankalin da ya fi na yau, kuma ba zan juri rainin hankalin kowa ba a kan yarana.
Matsayar da na kai kenan wadda kuma na kwana da ita a cikin raina. Da kayansu na fita na miƙa wa Najib tare da yi masa kwatancen gidan Kawu Sale, sannan muka rabu da zummar idan aka tashi ya kai su gidan. Zuciyata wasai saboda ganin na kashe gobarar da take ƙoƙarin tashi ta ƙone zuciyata da ta yarana.

Hmmmmm! Akwai badaƙala fa!🥲

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*TALATIN DA SHIDA.*

Zuciyata ɗauke da tunanin wace irin waina ce Barira take ƙoƙarin toyawa ita da ƙawayenta. Har na kammala aikina na miƙe na fito offis ɗin, saboda Amina ba ta zo ofishina kamar yadda ta saba ba.
Ɓangaren su na nufa cike da burin na gan ta domin na sanar da ita rikicin da ke ƙoƙarin ruftawa da ni. Wanda nake ji a raina muddin Baban Taufiƙ ya nace da son auren Sajida; tamkar ya saka takobi mai kaifi ya datse alaƙar da ke tsakanina da matarsa.
Saboda duk abin da zan faɗa mata ba zai goge kallon da za ta yi mini ba. Samun ta na yi cikin 'yan ofishin su suna ta hira, gani na ya sa ta miƙe tana faɗin,

"Yanzu nake son na je hirar Sara ya riƙe ni."

Gaisawa muka fara yi da mutanen sannan na fito Amina ta biyo ni, wuri muka samu muka zauna Amina ta fara faÉ—in,
"Duk abin da mutum yake yi a ɓoye, watarana sai Allah ya tona masa asiri. Ka yi alheri ma ya ka ƙare balle ka ce ɗan akuya za ka mayar da kanka?"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.