Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 55 of 86

"Wash! Allah! Wayyo-wayyo!"

Barira tana riƙe da hannunsa suka yi ɗakinsa tana jera masa sannu. Haka kawai na nemi annurin zuciyata na rasa, sanadin abin da na gani da idona; ya tabbatar mini da sun kwana suna shan ganimar aure. Tuƙuƙin baƙinciki ya taso mini nan take ya rufe mini zuciya.
Volume na ƙara wa tv'n da nake kallo, dumar waƙar SAI DA KE ta karaɗe falon gabaɗaya.

Abin da ya so ba ni dariya, lokacin da suka je bakin ƙofar ɗakinsa ya dakatar da ita a nan. Ban ji me ya faɗa mata ba, na hango ta tsaye rungume da hannu a ƙirji. Na ƙara ɗora idanuwana a kansu ba don na so ba, ya shige ɗakin shi kaɗai yana jinjina mata hannu sama alamun ta yi haƙuri, kawai ya kulle ƙofarsa dafe da ƙugunsa. Ya bar ta a nan bayan ya gama yi mata dariyar yaƙen kamar an yi masa dole.
Wani juyi ta yi tamkar ta kifa tana fisgar jiki ta faɗa ɗakinta ta rufe ƙofa da ƙarfi. Ajiyar zuciya na sauke tare da kashe tv'n na miƙe kamar wadda aka tsikara, na fito tsakar gidanmu domin na shaƙi iska mai sanyi.
Safa da marya na shiga yi a tsakar gidan saboda na rasa me ke mini daÉ—i a lokacin. Sallamar wasu mata biyu ya sa na shiga natsuwata tare da amsa musu sallama. Wani kallo suka bi ni da shi a lalace suka gaishe ni kamar ba su so suka shige ciki.
Sosai na ji zafin abin da suka yi mini, amma dole na danne don ba zan bari na fara takun-saƙa da ita tun yanzu ba, balle masu zuwa wurinta su tafi. Zama na yi a kan kujerar robar da ke wurin ina nazarin abin a raina.
Har su Ummu Salma suka dawo ban tashi daga zaman da nake yi ba, umurnin cire kayan makaranta na yi musu suka yi ciki da gudu. Mintuna a tsakani na miƙe na bi bayansu zuciyata a cunkushe raina babu daɗi.

"Ke Ruky ina ganin jalala! Ke ko dare É—aya tak! Amma Romiyo ya susuce tamkar ba namijin kirki ba?"
"Ga shi kuma ke a nan ɓangaren ba ki da mutunci! To ki dai yi a hankali, kuma ki tuna kina da kishiya ba ke kaɗai ba ce a gidan."
"Babu ruwana da kowa wallahi kaina na sani, idan ban ga haske ba kuma na tayar da tubana don ba na iya juriya gaskiya."
"Ba ki da mutunci Barira!"

"E ɗin, a bar ni a hakan! Wa ya ƙi daɗi?" Dariya suka fashe da ita dukansu har da shewa, na tura ƙofar ɗakina na shige ina juya maganganunsu a zuciyata.

'Waton ita ma jar wuya ce!'

Zancen da na yi kenan a raina, saboda hirar su ta bayyana wace ce ita, bayan abin da na gani zahirin da idona. Babu shiri murmushi mai sauti ya suɓuce mini saboda farincikin kafcen zai fi daɗi a hakan.
Wayata na cire daga caji na tura wa MD saƙon godiya, saboda rashin kyautawata ban yi godiya tun da zafi ba. Abin yana ta cizon raina, sai da na tura masa saƙon sannan na ji tamkar an sauke mini ƙaton dutsi a saman kaina.

'Na ga saƙo na gode sosai! Ubangiji ya ƙara buɗi da rufin asiri'

Mintuna a tsakani ya dawo mini da 'Amin' kawai ba tare da ya ƙara komai a kai ba. Haushi na ji na goge saƙon duka, sannan na mayar da wayar a caji.
Ban san ya aka ƙarge ba tsakanin amarya da angonta ba, balle marasa kunyar ƙawayenta. A cikin bacci na jiyo sautin muryar Barira tare da bugun ƙofar ɗaki, na so kada na bi ta kai don ban san kalar rainin wayon da suka shirya ba.
Amma haƙƙin zamantakewa ya sa na miƙe na buɗe ɗakina na fito, hango ta na yi a bakin ɗakin Mukhtar tana ta dukan ƙofar tare da kiran sunansa.
Da sauri na juya da nufin komawa na ji muryarta É—auke da damuwa tana cewa,
"Aunty don Allah ki ce ya zo ya buɗe ƙofa, tun yamma da ya shige bai sake fitowa ba. Ga shi ba ya jin daɗin jikinsa kuma ya dace mu san a wane hali yake ciki."
Murmushi kawai na yi, sannan na ƙaraso bakin ɗakin na fara kiran sunansa. Kamar jira yake yi ya buɗe ƙofar a fusace yana faɗin,
"Kun fa dami mutane cikin dare, ko ku ba ku san dare mahutar bawa ba ne?"
Dariyata na ƙumshe sannan na ce da shi, "Amarya ce ke neman sanin halin da kake ciki. Shi ya sa na ga ya dace na taya ta neman ka saboda haƙƙin zamantakewa."

"To lafiyata ƙalau ku je ku kwanta! Don ba na jin ƙarfin jikina ne shi ya sa ban fito ba. Tun da kun gan ni ku je ku kwanta kawai sai da safe!."

Na juya ina 'yar dariya na ce da su, "Mu tashi lafiya."
"Me za ki yi a nan ke kuma? Wuce É—akinki ki kwanta ko'ina jikina ciwo yake yi wallahi."
Maganarsa kenan da na jiyo kafin na isa ɗakina, 'Garam!' Na ji ya rufe ɗakinsa da ƙarfi. Sai da na shiga zan rufe ƙofata na hango Barira a bakin ɗakin tamkar an dasa ta.
Dariya ta suɓuce mini na yi hanzarin rufe ɗakin, raina fes na koma kan gadona na kwanta ina jin kaina cikin nishaɗi.
Bacci mai daɗi na yi tare da mafarkin MD a cikin wani kyakkyawan yanayi. Rungume nake a jikinsa, hannunsa cikin nawa yana yi mini raɗa a kunne ina ta faman murmushi. Fuskarsa ɗauke da annuri yana fesa mini siririyar dariyar da ta ƙara wa fuskarsa annuri.

'Ina sonki da yawa matata!'

Rufe fuskata na yi tare da lakuce masa karen hanci, kiss ya yi mini a goshi cikin shauƙin ƙauna yana aika mini kallon da da ya haifar mini da kasala. Ya rungume ni gabaɗaya a jikinsa, sannan ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya mai sauti 'Hummmmmm!' Luf na yi cikin jikinsa numfashina yana fita a hankali cikin wani yanayi mai daɗi.

Kiran sallar asuba ya katse mini daddaÉ—an mafarkin da na yi, wanda na so na É—ore da shi a hakan ba tare da na farka ba. Jikina ko kaÉ—an babu kuzari, a haka na yi sallah na tayar da yaran sannan na fito É—aki da nufin zuwa kitchen.
Turus na yi saboda hango Barira a yashe ƙofar ɗakin Mukhtar, rigar barcin da ke jikinta gabaɗaya ta kware cinyoyinta a buɗe.

"Ita kuma wannan me ya same ta?"

To fa😱 amaryar Romiyo ya take ne?😂

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*Ina ƙara tunatarwa!Ban yarda ba! Ban amince ba! Kada a ɗora mini littafi YouTube ba tare da izina na ba! Masu nema daga farko ku yi haƙuri har a kammala🙏*

*TALATIN DA UKU.*

Tambayar da na yi wa kaina kenan a zuciya, sannan na yi tattaki a hankali har na isa inda take. Sunanta na fara kira domin alamu ya nuna mini ƙarara bacci take yi sharkaf!
Ba ta motsa ba har sai da na duƙa na bugi hannunta tare faɗin, "Barira!"
Ta miƙe firgigit tana waige-waige tare da faɗin, "Don Allah Romiyo ka buɗe mini ƙofar"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.