Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 30 of 86
_Tun da safe na yi sallama da waɗanda ya zama dole, sannan Baba Ali ya sa aka kai ni tasha tare da kayan alherin da na samu niƙi-niƙi. Saboda mutanen Sokoto da Kebbi akwai ƙara kuma akwai girmama baƙunta._
_Sai dai abin da su Umma ta tarbe ni da shi ya kaÉ—ar mini da 'yan hanjina, duk da ban bari na fito da firgicin a fili suka gani ba. Amma na shiga rashin natsuwar da ta janyo mini kiran Mukhtar babu shiri, saboda Inna Kulu ta sanar da ni,_
"Mun yi ta zuwa a gyara miki ɗakinki ba a iske Mukhtar gida. Kuma an sanar da Mahaifiyar shi ta karɓi makulli a hannun shi idan muka zo mu karɓa, nan ma duk muka je haka muke dawowa babu makullin. A ƙarshe ma cewa ta yi da mu ya yi tafiya, kuma bai bar musu makullin ba. Amma ya ba da haƙuri a kan ki koma gidansa shi ma zai dawo garin a ranar da kika dawo."
_Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce ta bari na kira shi na ji yaushe zai dawo. Ni ma hakurin ya ba ni a lokacin da na kira shin, tare da saka mini ranar da zan koma domin shi ma a ranar zai dawo._
_Kasancewar rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, hakan ya sa na tattara kayana na koma gidansu Mukhtar. Tare da rakiyar su Inna Kulu da Hafsa, sai wata ƙawar Umma da wasu mata biyu daga cikin dangin su Ummata da ke Dunguza._
_Sai dai har tara na dare ta wuce goma ta doso Mukhtar bai dawo ba, dole suka tafi ba tare da sun kai ni É—akina ba. Ni ma a nan É—akin Mahaifiyar shi bacci ya kwashe ni, kasancewar Ummu Salma tana hannun matar Baban shi._
_Cikin bacci na ji muryar shi na yi firgigit na tashi, ya iso inda nake cike da mayalwacin farinciki a kan fuskar shi. Ni ma sosai na ji daɗin ganin shi har raina, ya saɓa Ummu Salma a kafaɗar shi muka yi ɓangarena. Makulli ya ba ni sannan ya miƙo mini ita ya ce; bari ya je ya kwaso mini kayana da muka baro ɗakin Mahaifiyar shi. Ban kawo komai a raina ba, kawai na buɗe na shiga da guntuwar sallamata, sai dai babu shiri na zaro ido tare da kwarma ihu iya ƙarfina ina faɗin,_
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!"
Shin me ke faruwa ne😨 na yi nan ni maðŸƒðŸ»â€â™€ï¸
Idan ban ga ruwan comments ba zan je hutun sati ɗaya😒
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA SHA TARA.*
"Subhanallah! Me ya faru a lokacin? Me kika gani bayan kin shiga É—akin?" Tamboyoyin da Amina ta jefo mini kenan a ruÉ—e, tare da firgici kwance a kan fuskarta. Murmushi na yi saboda ganin yadda hankalinta ya tashi, cikin sauri ta ce da ni,
"Don Allah ki sanar da ni me ya faru a lokacin? Na mats...
"Me dai yake shirin faruwa a yanzu!"
Maganar da muka ji kenan daga ni har Amina a bakin ƙofar ofis ɗina, cike da mamaki muka bi mata biyun da ke shigowa da kallon mamaki, waɗanda ke ƙoƙarin isowa inda muke cikin gadara. Kallon sama da ƙasa ɗaya ta fara yi mana sannan ta tsayar da kallonta a kaina, nuna ni ta yi da key ɗin da ke hannunta ta ce,
"Da alamu ke ce Munafukar da nake nema!"
"Ta ya za ki neme ni bayan ni ban san ki ba!" Maganar da na faɗa mata kenan cike da jin haushin rainin hankalin da take ƙoƙarin yi mini, har cikin ofishina. Bayan dakan luguden da zuciyata ta hau yi saboda tsabar kaɗuwar da na shiga"
Kallon uku kwabo ta yi mini sannan ta miƙa hannu ta baya wadda suka zo tare ta saka mata wani wallet a hannunta, sai da ta buɗe shi sannan ta wurgo mini a fusace saman ya daki ƙirjin ya yi ƙasa. Daga shi har kayan da ke cikin shi suka yi ɗaiɗaya, na yi hanzarin kai kallona a kayan da suka zuba daga wallet ɗin, cike da mamakin yadda aka yi ta yi ta same su. Kafin na duƙa na ɗauko Amina ta riga ni haɗa kansu ta ɗago, cike da zallar mamaki a kan fuskarta ta fara jujjuya kayan cikin wallet ɗin a hannunta tana faɗin,
"Wai ku bayin Allah me ya kawo ku ofinshin nan da rana tsaka haka? Sannan ina kuka haÉ—u da Id card É—in ta, da passport har da ATM?"
"Za ki samu duka amsoshin tambayoyinki dalla-dalla, kuma zan yi miki gwari-gwari yanzu ba sai na ja zaren da tsawo ba. Amma kafin nan ke ki yi mata bayanin inda kika je kwatankwaci kika baro wallet É—inki."
"Kwartanci kuma!?"
Maganar da muka haɗa baki kenan wurin faɗa ni da Amina cikin tashin hankali, babu zato na ji 'Karaf' sauti da dirar marin matar a kan fuskata. Kafin na yi wani yunƙurin ramawa ta ci kwalata a masifance tana faɗin,
"Sai na illata ki, ta yadda gobe ko da kuɗi aka ce ki sake zuwa gidana kwartanci ba za ki iya taka ƙafarki ki je ba."
Duka ta fara kai mini Amina tana riƙe hannunta cikin zafin nama, yayin da ni kuma na shiga ƙwatar kaina ta ƙarfi duk da fargaba ya hana ni kataɓus. Ƙawarta ta fara janye Amina tana faɗin,
"Ke dalla malama matsa daga gefe ba wurinki muka zo ba. Ci ubanta Fatima gobe ko kallon MD aka ce ta yi ba za ta sake ba, balle ta kai ƙafarta gidanku a matsayin ƙatuwar kwartuwar da ba ta ramin kanta sai na wasu."
Sunan MD da na ji ƙawarta ta faɗa na ji ƙirjina ya buga dam-dam! Amma a hakan bai hana ni jarumtar ƙwace riƙon da ta yi mini. Amina ta yi hanzarin shiga tsakaninmu tana tura ta baya, ita kuma sai ƙoƙarin kai mini bugu take yi ta gefen Amina.
Cikin ƙololuwar ɓacin rai na fara nuna ta da hannu ina huci na ce,
"Zan nuna miki na fi ki tashanci matuƙar kika sake taɓa ni da sunan du..."
Kafin na rufe bakina ta shammaci Amina ta kawo mini wani sabon duka, kukan kura na yi tare da ture Amina gefe. Cikin rufewar ido da na zuciya na yi cikinta da duka iya ƙarfina. Kokawa muka fara yi ni da ita Amina tana ƙoƙarin raba mu, ƙawarta kuma tana ƙara zuga ta da ihun faɗin ta ci ubana kada ta ƙyale ni.
Ta dake ni na dake ta muke yi a tsakiyar ofishin ba tare da ta yi nasarar kayar da ni ƙasa ba. Cikin sa'a na saka mata ƙafa ta faɗi na hau kanta ina ta jibga, ƙawarta ma tana kai mini duka tare da ƙoƙarin ture ni daga saman ruwan cikinta.
Ban san ya aka yi ba na tsinkayo muryar MD yana salati, amma hakan bai hana ni ci gaba da jibgar ta ba inda ta yi mini daÉ—i. Domin ko a shekaru zan iya girmar ta kaÉ—an ko mu zo tsara, duk da ta fi ni zama duma-duma amma hakan bai sa ta yi nasara kaina ba.
Amina ta janye ni daga samanta ina huci tare da ƙoƙarin ƙwacewa na koma, da nufin sake kai mata wani dukan domin na cire rainin da ke tsakaninmu. Saboda raina ya yi ƙololuwar ɓaci a kan abin da ta yi mini, haka idona ya rufe ba na ganin komai face na yagalgala ta iya son raina.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.