Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 27 of 86

Dukanmu muka bi ƙofa da kallo saboda shigowar Inna Kulu da kula. Gaban Amina ta ajiye tana faɗin, "Ku ci awara tun kafin ta yi sanyi."
Bayan fitar Inna Kulu Amina ta miƙe tana faɗin, "Bari na fara yin sallah don ba na son na ci na kasa motsin kirki. Tun da kin tayar mana da hankali a wurin aiki ana ta jimamin ciwonki, MD ma yau bai zauna ba tun da ya zo da safe ya fita har na baro wurin bai dawo ba."
"Uhumm!" Kawai na ce ta fice na ci gaba da jan carbina, har ta dawo na tashi na ba ta sallayar. Kafin ta gama na zuba mana awarar a plate É—aya, tare da ruwa a kofuna.
Bayan ta gama muka fara cin awarar ta sha kayan haÉ—i da daddaÉ—an yaji, domin sana'ar Inna Kulun ce kuma sosai take samun rufin asiri da ita. Shiru ya ratsa tsakani, kafin Amina ta kawar da shirun da cewa,
"Da zumuɗi na tashi yau domin na zo na ji cigaban labarina, abin haushi sai ga shi na tsinci zancen ciwonki a bakin MD. Bayan na yi ta rangadin zuwa offishinki ina ganin shi a kulle, a zuwa na ƙarshe ne da na gan shi zai fita nake tambayar shi ko kin zo; ya ce da ni kin turo masa saƙo ba kya samun damar zuwa ciwonki ya tashi kina gida. Da ƙyar na samu na kammala aikina na nufi gidanki, ganin gidan a rufe ya sa na kira lambarki ba ta shiga. Dole na na sake neman shi na sanar da shi ba kya gidan, ya sanar da ni kin ce kina gidanku wurin Umma Bafarawa Estate. Adaidaita na ƙara samu na yi gida, sai da na kammala ƙananun ayukana sannan na ƙara shiri zan fito."
Ƙasake ta yi tana lagudar awarar da ke hannunta wanda a take na gano akwai abin da ya faru kafin ta fito gidan. Hakan ya sa na samu kuzarin faɗin, "Ai da kin yi haƙuri gobe ma zan shiga aikin. Kin ga sai mu ɗan samu abin da zai sauwaƙa kafin a tashi."
"Hmm! Ai ba zan iya haƙurin ba wallahi, in da na samu wayarki da ba zan shiga damuwar da na shiga ba. Saboda ina tunanin a wane hali kike ciki duba da yanayin da kika baro wurin aikin jiya, kamar akwai wani abu maras daɗi da ya faru da ke. Hakan ya ƙara tayar mini da hankali ga shi matsalar da na samu ban san gidan da zan faɗa a kawo ni ba. Kuma ina da tabbacin MD ma bai san gidan ba shi ya sa ban neme shi ba."
"Ya aka yi kika gano gidan yanzu?"
"Tambaya muka fara yi ni da mai adaidaitan da muka zo unguwar, har na yi katarin ganin Haidar tare da wasu yara a daidai wani shago. Da hanzari na kira shi yana gani na ya nufo ni yana gaishe ni, a nan yake yi mana kwatance na ce ya shigo ya kawo mu kawai."

Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Allah Sarki Amina, na gode sosai da ƙoƙarinki. Allah ya bar zumunci."
"Amin" ta ce sannan ta yi hanzarin fiddo wayarta a jaka saboda kiran da ake yi mata. "Ga ni nan zuwa yanzu." Abin da ta faɗa kenan fuskarta a haɗe bayan ta gama sauraron abin da aka ce cikin wayar. Mere na ga ta yi tare da hurar hanci tana lasar maiƙon da ke hannunta. Ban ce da ita komai don na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.
"Na rasa me na tare wa Mama da ko kaɗan ba ta ƙaunar farincikina. Yanzu fa ba ta ji kunyar kai ƙara ta wurin shi ba. Kuma shi ya bar ni fitar nan amma ƙiri-ƙiri ta so hana ni fitowa, saboda girkin da zan gama wahala a hana ni kwana da miji."
Ta ƙare maganar fuskarta a cure, hakan ya tona mini asirin takaicin da take ƙumsa dangane da baƙar dokar Mama. Wadda mijinta ya mayar tamkar faɗar Allah da ta faɗa sai ya aiwatar ko ba ya so, duk da san kuskure ne yake aikata wa matar shi, bayan alaƙar zumuncin da ke tsakaninsu mai ƙarfi. Domin Mama uwar miji ce gare ta kuma Gwaggonta, saboda Yaya take ga Mahaifin Aminar uwa ɗaya uba ɗaya.

Amina ta so zama na ɗora mata labarin, amma dole na dinga nuna mata rashin dacewar zaman tun da gobe zan fito aiki. Sannan na ba ta haƙuri sosai tare da nuna mata alfanun juriya a kan cutarwar da Mamar take yi mata da gangan, matuƙar tana son ganin ribar a gaba. Cikin nasara na ci kanta ta miƙe tana saɓa jakarta a kafaɗa tana faɗin,
"To ni zan tafi Allah ya ƙara sauƙi. Amma don Allah ki ƙoƙarta ki fito goben."

Har bakin titi muka raka ta ni da su Ummu Salma, tare da ba ta tabbacin zan fito gobe ta tsumaye ni. Ta tafi muna ɗaga wa juna hannu na juyo ina goge ƙwallar tausayin kanmu ni da ita, duk da na fi ta matsala amma har zuciyata ina jin tausayin ta a raina. Saboda ba ta da ƙarfin zuciyar shanye damuwa, saɓanin ni da na zamo turmin tsakar gida sha luguden mahassada. Domin duk wani sara da sukan da aka yi mini bai hana ni kirkiza ba, balle damuwar hakan ta bayyana a jikina. Dalilin hakan ya sa wasu da yawa suke hawa kan batutuwan Mukhtar su zauna. Saboda na kasa zama abin tausayi a kan fuskokin mutane, ta yadda za a gano matsalar da nake ciki ta hanyar rama ko lalacewar da ido zai tabbatar da lalle ina shan wahala a gidan shi.

Da dare misalin ƙarfe tara da rabi na dare, Umma da Inna Kulu suka kai ni gidan Mukhtar. Da motar wani Baban ƙawata kuma maƙocin Kawu Sale kuma abokin shi. Bayan sun gama jan kunnena sosai a kan na yi haƙuri na zauna lafiya da mijina, sai dai ni ko kaɗan ban ɗauki shawarar zama da shi a yadda suke so ba. Don ya gama sire mini kuma mutuncin shi ya daɗe da zubewa a idona. Saboda ba na jin zai iya dawo da martabar shi gare ni ko da zai mallaka mini ƙasar Nigeriya da abin da ke cikinta.
Ko da muka je mun tarad da shi, suka ƙara haɗa mu duka suka yi mana nasiha tare da saka mu neman yafiyar juna. Bayan sun tafi na saka yarana suka kwanta na tofe su da addu'o'in bacci sannan na rufo musu ɗaki.
Ɗakina na nufa na yi sabon wanka don jin daɗin kaina, sannan na kwanta tare da janyo wayata. Messages na shiga dubawa ta inbox da saƙonnin da ake ta turo mini daga waɗanda nake mutunci da su a wurin aikinmu. inda ake ta yi mini ya jiki tare da fatar samun sauƙi, saboda tun an karɓo mini jakata a hannun su Ummita, ban sake kunna wayar ba sai a lokacin. Shi ya sa ban san da shigowar saƙonnin ba. Amsa na shiga bai wa mutanen har na zo kan saƙon MD, haka ƙawa na tsinci kaina da yin guntun tsaki ba tare da na shirya ba. Saboda har lokacin ban daina jin haushin abin da ya yi mini ba, wanda nake ji a raina tamkar ya datse ganin walwalar fuskata har abada. Domin na ci alwashin ko kallo don ya zama dole na gan shi, amma da ina da iko da hana kaina ganin shi saboda tsabar takaicin shi da nake ji.
Bubbugar da na ji ana yi wa ƙofar ɗakina ya sa na yi kasaƙe ina sauraron muryar Mukhtar da ke ta faɗin, "Ki buɗe magana za mu yi." Tsaki kawai na ja sannan kashe wayar tare da juya kwanciyata, yawan bugun da yake yi wa ƙofar ya sa na miƙe a fusace na buɗe ƙofar tare da tare hanya, ƙugu na riƙe fuskata a cure na ce,
"Malam lafiya?"
"Lafiyar ce ta kawo hakan!"
Amsar da ya ba ni kenan ya ratsa ta gefena ya shigo ɗakin. Zama ya yi a kan gadona yana murmushin shi da ke nuna mini alamun wata sabuwar yaudara ta kawo shi ɗakina. Domin ba na kawo ƙarshen zuwan shi ɗakin cikin lalama ba tare da tashin hankali ya ingizo ƙeyar shi ba.
"Zo ki zauna."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.