Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 67 of 86

"Ke aka zo nema!"

Ummar da yake kallo ya sa muka gano da ita yake, miƙewa ta yi tare da mayar da hijabinta ta fice. Inna Kulu ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,
"Tun da tana jin maganarki Zaituna! Don Allah ki fahimtar da ita. Ta bari a yi komai a hankali ko don yaran nan."
Kawu Sale ya shigo É—akin yana faÉ—in,
"Na san mijinki bai da mutunci, amma muddin aka biye ta Habi; ba za a haifi É—a mai ido ba. Idan ma rabuwar ce a yi ta mutunci ba irin wadda girma zai zube ba."

Murmushi na yi sannan na ce, "Ka yi haƙuri Kawu! In sha Allah komai zai tafi yadda ya dac..."

"Wallahi! Ko kai ne autan maza Zaituna ta gama zama gidanka! Ba kuka da ruwan hawaye ba, ko na jini za ka yi ka daÉ—e ba ka yi ba. Munafukin banza mutumin kawai!"

Zantukan Umma kenan cikin É—aga murya, da sauri muka fito É—akin saboda ba na so tana tayar da jijiyoyinta a kan Mukhtar.
Kawu Sale ya shige ɗakinsa ni da Inna Kulu muka nufi ƙofar gidan.
'Kayan haushi!'
Zancen da yi kenan a zuciyata tare da guntun tsaki. Saboda ganin Mukhtar durƙushe ƙasa gaban Umma yana kuka har da majina.
Hannuwansa ya haɗa yana faman magiya tare da roƙon ta a kan ta janye furucin da ta yi, wanda ta shata mini layin komawa gidansa har abada.
Baban Taufiƙ da ke tsaye rungume da hannuwansa a ƙirji, shiru kawai ya yi kansa a duƙe ban ji ya ce komai ba. Har sai da ya ɗago kai ya gan ni sannan ya ce da ni,
"Don Allah ki bai wa Umma haƙuri. In sha Allah ba za a sake samun matsala ba."

Kallon banza na yi masa sannan na ce da Umma,
"Koma gida abin ki ki bar ni da su."

A fusace ta ce, "Ba zan bar ki da su ba! Wuce mu je ciki! Kuma daga yau kada na sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan nan, matuƙar ba takardar sakinta za ka kawo mini ba!"
Tana ƙare faɗar hakan Inna Kulu ta ja ta suka yi ciki tana faɗin,

"Ke ma ki shigo ciki!"

Ko kallon su ban sake yi ba, muka shige muka bar su a ƙofar gidan tamkar ruwa ya ci su. A cikin gidan ma Inna Kulu ta daɗe tana tausar Umma sannan ta daina faɗan da take yi. Ta janyo Umma Salma da Iman da ke ta kuka ta fara rarrashin su. Haidar kam tagumi kawai ya yi hannu bibbiyu, ba tare da ya yi kuka ko ya tashi daga inda na bar shi ba.

Ni dai Umma ki yi haƙuri 😒

Manage plss!

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*TALATIN DA TARA.*

Daren ranar haka muka kwana cikin tunanin makomar aurena da Mukhtar. Tun da safe Umma ta ce za ta je gidan ta É—auko mana kayanmu. Na ce ta bari na nemo Sajida ta É—auko mana duk abin da muke so.
Ba don ta so ba, na kira Sajida tare da yi mata bayanin abin da nake so ta yi mini.

"Aunty ke kina ina?"

Tambayar da ta yi mini kenan cikin sanyin murya. Ina 'yar dariya na yi mata bayanin duk abin da ya faru. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Lalle wannan lamari ya wuce tunanina. Ni kam wallahi ba da ni ba gaÉ—a a hurumi, don ba zan iya dambe da aljanu ba."

"Kwantar da hankalinki, babu abin da zai faru sai alheri."

"Haka ne Aunty! Amma maganin a yi kada a fara, tun yanzu ake shawara ba sai abu ya lalace ba a dawo faÉ—in da an sani."

"Yanzu dai ki je gidan, zan bai wa Najib makullan gidan da na É—akina ya kai miki."

"To Aunty bari na je!"

Daga haka na kashe wayar ina kallon Haidar da ke faÉ—in, "Ni dai Mama da ma mun bar zuwa makarantar yau! Ni wallahi na ma gaji da zuwan ta"

"Ai kuwa ba ni auren da kai tun da ba ka son zuwa makaranta." Inna Kulu ta faÉ—a a lokacin da take shigowa É—akin Ummar. Kwanon É—imamen tuwon jiya ta ajiye mini nawa daban na su Ummu Salma daban.

"To ai kullum sai na je! Ki tambayi Mama. Yanzu kuma na gaji gaskiya! Koyaushe makaranta-makaranta dai. Jiya na je, gobe na je, jibi ma na je, don Allah Mama yau ki ce ban zuwa."

Godiya na yi wa Inna Kulu ina dariyar Haidar, saboda yadda yake lissafin! jiya ya je gobe ya je, yana lanƙwasa yatsun shi kamar mai lissafin wasu manyan kuɗi.

"To ai ba a gajiya da karatu!" Cewar Inna Kulu tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. Ya ba ta amsa da cewa,

"Ni dai na gaji gaskiya!"

Wayata na cire daga caji na kira Najib, na ce ya zo ya karɓi key ya kai wa Sajida can gidan. Sannan na ajiye wayar na ja tuwona ina ci tare da Haidar. Su Ummu Salma suna cin nasu muna bitar azkar ɗin safiya da ake yi a tashar Tauraruwa. Umma ta shigo ɗauke da taliyar da ta dafa muna a tire.
Sannu da ƙoƙari na yi mata sannan na ce, "Dama ba ki wahalar da kanki dafuwar ba. Saboda tuwon nan ma zai ishe mu ni da su."
"Wahala rashi! Ni kuma ban gan ta a nan ba! Ku dai ci ku ƙoshi kawai!"
Sai da ta zauna tana rage volume É—in tv'n sannan ta ce, "Yaran nan kamar ba za su je makaranta yau ba. Har yaushe aka É—auko kayan? Yaushe suka shirya suka tafi?"

"Sai a tara gobe, duk da ba haka aka so ba."

Zancen da na yi kenan wanda ya sa Haidar ihun jin daɗi, har da 'yar rawarsa yana yi wa su Ummu Salma gwalo. Saboda yadda ya ga sun haɗe fuska alamun ba haka suka so ba. Najib ya kira ni ga shi ya zo, na miƙa wa Haidar makullan ya kai masa. Bayan tafiyar shi na ƙara kiran Sajida ta ce da ni ta kusa kai gidan. Saboda ita tana Gwiwa Low-cost, mu kuma muna Runjin Sambo.
Bayan mun gama cin abincin na yi wa Iman da Haidar wanka, ni ma na yi wankan sannan Umma Salma ta shiga. Ina tsaka da shafa mai Sajida ta kira ni, tana sanar da ni Mukhtar ya hana ta ɗauko kayan. Raina a ɓace na ce da ita ta jira ni zan zo da kaina tun da abin nashi babu arziƙi.
Umma ta ce "Lafiya?" Na sanar da ita abin da Sajida ta faÉ—a mini. Fuskarta a haÉ—e ta ce da ni na yi zamana ita za ta je da kanta.
"Jiyan ma mantawa na yi da É—aukar komai shi ya sa muka fito ba ki É—auko kayanku ba."
Tana ƙare maganar ta ja hijabinta ta fice, Allah ya tsare na ce da ita sannan na sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin Mukhtar da tsanarsa a cikin raina.

Ban san ya aka yi ba misalin ƙarfe goma sai ga Umma da Sajida ɗauke da kayanmu niƙi-niƙi. Da fara'a na tarbe su na karɓi kayan ina yi musu sannu muka shige ɗakin Umma.
Sajida ta zauna tana faÉ—in, "Wash! Allah!" Yar dariya na yi mata ina buÉ—e jakunkunan kayanmu na ce,
"Sannu da ƙoƙari, ai kun sha aiki."
"In da ma a ce aikin ne da sauƙi. Don ba ki ga irin tataɓurzar da aka sha tsakanin Umma da Baba Mukhtar ba. Shegiyar matarsa sai leƙe take yi kai ya sha bandeji tana gulma. Ai ni yau na san na kaɗe har hanjina, saboda Baba Mukhtar har dukana ya so yi mijin maƙociyarki ne ya hana shi."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.