Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 49 of 86

"Magana za mu yi ranka ya daÉ—e!"

Ya tsaya ba tare da ya waigo ba, na je ta gabansa kamar ban taɓa jin haushin sa duniya ba.
"Gobe za a yi wa amarya jere. Me za a tanadar musu a matsayin abincin da za su ci, da wanda za su riƙa idan sun je gida su raba?."
Kallon mamaki ya fara bin fuskata da shi kafin ya ce, "Me ya haÉ—a ki da tambayar abin da ya shafi aure na?"

"Saboda ina cikin gidanka ina amsa sunan matarka a zahiri."

Na ba shi amsa cikin gadara don na fahimci take-takensa ba zai bari mu ƙare maganar cikin daɗin rai ba.
"To wannan ba abin da ya shafe ki ba ne! Ki fitar da kanki cikin abin da babu ruwanki."
Yana ƙare maganar ya wuce fuu zai shige falo, na bi shi ina faɗin, "Da ruwana fa! Don ba na so a ce ban tarbe su da komai ba, a matsayina na uwargidan amarya mai ƙashin arziƙi."

Ƙanzil bai ce da ni ba ya shige ɗakinsa, dariyata na ƙumshe ina faɗin,
"Ka kira mana Barirar mu ji su nawa za su zo? Domin a yi musu komai a wadace babu harkar ƙaranta."
Bai kula ni ba har ya gama abin da yake yi a É—akinsa ya fito ya nufi hanyar fita yana haÉ—e rai,
"Na ce ka kira mana Barirar mu..."

"Yanzu don biyar diddigi har da sunanta sai da kika binciko? Ai da kin yi haƙuri idan ta zo komai za ki gani da idonki."
"Yo ita Barirar da ta gama gantalin talllar awara zan bi diddigi don na binciko wace ce ita?"
Dariya na tuntsure da ita ina riƙe ciki saboda ganin yadda ya yi shock tare da ƙura mini ido baki a sake. Hakan ya ƙara mini kuzarin faɗin,
"Kai ma dai da neman zance kake wallahi. Allah dai ya ƙara danƙon ƙauna mijin Barira mai awara."

"Ko kashi take kasawa a kasuwa ai sana'a ce balle awara. Don haka ni ita na hango ba awarar da take sayarwa ba, ki je ki ci gaba da tsegumin ki tun da ba sata take yi ba Alhmdulillah!"
Na bar wurin ina ta dariyar ƙeta, saboda safci faɗi ne kawai ya sa na laƙaba mata tallar awarar. Ashe da gaske na yi sara a kana gaɓa, tun da ya kasa shanye damuwar ya tona wa kansu asiri a ƙoƙarinsa na wanke ta.

Har ga Allah na ji na ƙara raina auren a raina, na ji haushin kashe kuɗina domin na yi musu barazana. Ashe ma a hakan da nake na fi ta kyaun gani ko da ban yi wanka ba, saboda duk macen da ta san kanta ba za ta iya talla ba.

***
Tun da safe wayar Maman TaufiÆ™ ce ta katse mini baccin da na koma bayan sallar asuba. Tambayar da ta yi mini a kan girkin ya sa na wartsake daga baccin ina faÉ—in,
"Ki bar shi kawai, ashe ma ya ba da komai a gidansu za a dafa a kawo musu."
Daga haka muka gama wayar na sauko daga kan gadon, saboda ganin su Ummu Salma har sun gyara katifar da suka kwana an É—auke ta Haidar.

Ƙamshin wainar ƙwan da na ji yana tashi ya tabbatar mini da Ummu Salma tana kitchen. Faɗawa na yi idona a kan plate ɗin da nake da tabbacin kalacina ne ta zuba.
Gaishe ni ta fara yi sannan ta ce, "Yanzu nake zancen na tayar da ke kada Indomien ta yi sanyi."
Ƙwan da take soyawa na karɓa ina faɗin, "Je ku shirya kada ku yi latti lokaci ya tafi."
Na gama soya wainar ƙwan da ta rage na saka wa kaina, sannan na buɗe kulolin su Haidar na jefa musu tasu wainar. Ita ma na saka mata a wani plate ɗin silbar da take cin abinci da shi idan ta yi ra'ayi.
Sanin ba ta son zuwa da abinci Makaranta, ya sa na ɗauki plate ɗina da nata na fito ina ƙwala wa su Iman kira su zo su ɗauki kulolinsu.

Na taras ta saka unuiform na ajiye mata plate É—in a kan mirror ina faÉ—in,
"Ki yi sauri fa! Don yau kun makara."
Tura Indomien take yi cikin sauri sai ga su Haidar da gudu suna faÉ—in ta fito Najib ya zo. A gurguje ta lamushe ta fice da plate É—in tana faÉ—in,

"Mun tafi Mama!"

A dawo lafiya na yi musu har sun fice na ji dawowar Haidar da gudu yana faÉ—in,
"Ba a ba mu kuÉ—in tara ba!"
Jakata na janyo na zazzage kayan cikinta, na lalubo nera ɗari na miƙa masa ya fice da gudu. Addu'o'ar tsari na dinga yi musu ina jefawa a bakin ƙofar kamar suna wurin, sannan na je na yi brush na fito na karya.

Ina gamawa na share gidan fes sannan na wanke kayan da aka ɓata, na ɓoye wasu kayana. Wanka na faɗa na shirya cikin shigar da ni kaina na san na yi kyau. Sallamar su Sajida da na jiyo na fito daga ɗakin ina zuba ƙamshi da murmushi a kan fuskata. Sajida da Mamarta na hango, sai wasu yayun Mukhtar na 'yan'uwa tare da yaransu.
Gaisawa muka fara yi da su babu yabo babu fallasa sannan na zauna. Sajida ta fara koÉ—a ni bakinta a sake take ta yabon kwalliyata, ina hankalce da Mamarta tana aika mata harara ta gefen ido.
Ganin ba za ta daina rawar ƙafar da take yi da ni ba ta miƙe tana faɗin,
"Abincin masu jere za mu dafa. A fito mana da tukanen girkin mu je mu yi abin da ya kawo mu."
Na miƙe tare da kiran Sajida da wasu yaran da suka zo da su muka nufi kitchen. A nan muka fito da manyan tukanena da murhu biyu, tare da wasu kayan da za a buƙata duka muka fitar da su a tsakar gidan.
Ina ƙoƙarin shige falo na ji ihun yara suna faɗin ga motar kayan amarya nan ta iso. Dam-dam! Na ji dakan lugude a tsakiyar zuciyata, da murmushin yaƙe na zauna falo ina kiran lambar Firdausi.
Bayan ta É—auka nake sanar da ita Mukhtar zai yi aure yau ake gyaran É—aki,

"Ai na É—auka ba za ki faÉ—a mini ba har sai an kawo amaryar mu zo ganin ta."

"Kwantas Hajiya! Ni ma daga sama na tsinci zancen auren. Don haka gobe ki fito ku danne mini ƙirjina."

Na ƙare maganar a daidai lokacin da ake shigo da kayan gadon amarya ana shigar da su ɗakinta. Miƙewa na yi na koma ɗakina, mayafi na ɗauko mahaɗin kayan na saka, sannan na rufe ɗakin da key na yi wa matan da ke shigowa sannu da zuwa.
Na fice tsakar gidan bayan jikina ya ba ni shaidar kallon da dangin amaryar suke yi mini. Maman TaufiÆ™ na kira a waya na ce ta fito ga aikin an kawo mana har gida.
Hannu na saka ina taya su aikin ba tare da na damu da kallon mamakin da Yayunsa suke yi mini ba. Na dinga jan Sajida da hira muna dariyar da iyakacinta kan fuskata, saboda ina so na nuna wa kowa ba na baƙinciki da auren a zahiri.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.