Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 86

Zama na yi a kan kujerar offis ɗina, ina dudduba aikin da na yi ina gyara inda ya dace. Kira ya shigo wayata na yi hanzarin fito da wayar a jaka babu shiri ƙirjina ya buga. Cikin sauri na ɗauka,
"Ki kawo takardun idan kin kammala aikinsu".

Zancen MD kenan bai ƙara da komai ba ya katse, cikin sauri na tattara takardun na yi offis ɗin shi. Da siririyar sallama na tura ƙofar na shiga, kaina a ƙasa na ajiye masa takardun zan juya.
"Shi dai wannan turaren ba za a daina saka shi ba kenan?"
Maganar da ya jefo mini kenan cikin ƙasan maƙoshi, shiru kawai na yi masa ina wasa da yatsun hannuna. "A matsayinki na matar aure, bai dace kina bari wani yana shaƙar ƙamshinki ba, wanda na san kin sani ko wadda babu aure kanta ba a halasta mata shafa turare dan za ta fita ba..."
"Sai bayan na saka na tuna, amma in Sha Allah zan kiyaye daga wannan".
Na ƙare zancen cikin sanyin murya da ƙara mata zaƙi. Bai ce da ni komai ba har na kai ƙofa zan fita na tuno saƙon shi na jiya da ban ga me ya rubuta ba. Juyowa na yi riƙe da handle ɗin ƙofar cikin ɗakiya na ce,
"Jiya ban ga saƙon ka ba wayar ta fashe. Ina ƙara godiya Allah ya ƙara buɗi".
"Amin" Ita kaÉ—ai ya faÉ—a ya ci gaba da aikin da yake yi, na fito zuciyata fes saboda kulawar ta shi gare ni. Hakan ya tabbatar mini da fatsata ta fara kamo mini kifi.

Ranar ban yi aiki da yawa ba, ina tsaka da chatting Amina ta shigo, muka gaisa fuskarta babu yabo babu fallasa domin na kasa tantance yanayinta.
Zama ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta ce "Jiya da tunaninki na kwana, ta yadda na matsu safiya ta waye na zo domin na ji tarihinki..."
"Ina Mama fatan tana lafiya?"
Tambayar da na yi mata kenan domin na ji yadda suka ƙare da rikicin kwanan. "Ina kwana ce kawai ta haɗa mu yau. Ita ma ba ta amsa ni ba, na ƙara yi mata duk da na san ta ji ni a farko. A masifance ta katsa mini tsawa tana faɗin na bar mata ɗakinta ba ta son gani na. Da na ƙi tashi ta yi kaina da duka na fice, a bisa tsautsayi ta rufo ƙofar ɗakinta cikin fushi ta dantse mini yatsun hannu na. Na jima ina jinyarsu kafin su rage mini zugi na samu ƙarfin fitowa".

""Hmmmmm! Batun kwanan fa a can ya kwana ko a wurinki?"
Shiru ta yi tana goge hawaye tsawon mintuna sannan ta ce, "A can ya kwana".
"Ki yi haƙuri komai yana da farko kuma yana da ƙarshe. In Sha Allah komai zai zamo tarihi watarana".

Daga ni har ita muka yi shiru, na shiga dogon tunanin cutarwar da mata suke fuskanta a gidajen aurensu. Tare da tambayar kaina 'Yaushe ne mata za su daina fuskantar ƙalubalen aure?'
'Babu rana' amsar da wata zuciyar ta ba ni kenan cike da tabbacin matuƙar ba a ɗinke ɓarakar ba, to ba za a taɓa daidaituwa tsakanin ma'aurata ba.
'Ta wace hanya?'
Tambayar da na sake yi wa kaina a zuciyata kenan, kafin Amina ta katse mini zancen zucin da nake yi, "Ina so ki sanar da ni abubuwan da kika fara faɗa mini jiya, wanda asali dalilin hakan ya sa na fito aiki yau. Domin ba na so na ƙi zuwa na yi missing wannan babban Flight'".
'Yar dariya na yi saboda ƙarshen zancenta, shiru na yi ina nazarin ta inda zan fara ba ta labarin kaina.

_"Kamar yadda kika sani sunana Zaituna Aliyu, amma Aliyu Yayan mahaifina ne ba shi ne asalin wanda ya haife ni ba. Sunan mahaifina Alhaji Sani. Na samo asalin sunan tun a ranar da Baba Ali ya saka ni makaranta tare da 'ya'yan shi. "_
_"Haifaffiyar Jahar Kebbi kuma 'yar asalin garin Fulani, waton ƙauyen Ɗakin Gari. Na taso a garin Kebbi tare da mahaifina kafin Allah ya yi masa rasuwa. Na ci gaba da zama a garin Kebbi hannun Baba Ali cikin unguwar Aleru Quarters har na kammala karatuna a matakin digiri. Inda na yi Federal staff school nursery, primary and secondary. Sannan na ci gaba da karatun jami'a a Federal University Birnin Kebbi "_
_"Mahaifiyata 'yar asalin jahar Sokoto ce. A ƙaramar hukumar wamakko lokal government. Jefi-jefi ina kai mata ziyara a duk lokacin da na samu sarari, sai dai ba na daɗewa idan ba babban hutu aka samu a makaranta ba."_
_"A irin wannan ziyarar da nake kai wa Ummata a garin Sokoto na haɗu da Mukhtar har Allah ya ƙaddara aure tsakanina da shi. Sai dai kafin auren ya tabbata sai da aka yi ɗan ƙaramin gumurzu."_

Ni ma dai a matse nake da na ji tarihin aurenki da Mukhtar da wannan gumurzun😅

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

_*Ban yarda ba, ban amince a juya mini littafi, ko a yi amfani da shi ta kowace fuska ba tare da izinina ba. Saɓanin haka zan ɗauki matakin gaggawa wanda babu sani balle sabo😼*_

*LAMBA SHA ÆŠAYA.*

_A ranar da na fara haɗuwa da shi, ina kan hanyar zuwa Bafarawa estate na fito Line G. Inda na kai wa wata ƙawar mahaifiyata ziyara a bisa umurnin ta. Domin ɓeran masallaci ce ni babu inda nake zuwa kullum ina gida, wannan fitar ma ta matsa ne sai na je na gayar da danginta da ke Dunguza, saboda babu tazara tsakanin su da Line G . Kullum suna ƙorafin ba ta bari na yi zumunci, idan na zo har na koma ba su sani ba. Su yi ta mita bayan sun juye laifin da nufin ita ce ba ta so na yi zumunci da su._
_Kasancewar ba wata tazara ce mai yawa ba, na zaɓi komawa ƙasa domin na miƙa ƙafafuwana. Na fito Line G. Kenan daidai polo na ji magana a bayana, cikin sauri na waiga na yi tolazi da fuskar shi ɗauke da murmushi. Amma tun daga kallo ɗayan da na yi masa ban sake bi ta kan shi ba, tafiya nake yi yana bi na a baya yana faɗin,"_
"Don Allah ki tsaya ki saurare ni, unguwarku kawai nake so ki sanar da ni sai lambar wayarki".
_Na ci gaba da tafiyata ban tsaya ba balle na tanka shi kamar yadda yake so. Tun yana yi mini magiya ina jin haushin takurar da ya yi mini har ta kai ya fara ba ni tausayi. Saboda muryar kukan da na ji ya koma yi cikin marairaitar da ya yi nasarar saka ni tsayawa na ce da shi,_
_"Ka yi haƙuri ba na magana a kan hanya..."_

"Lambar wayarki kawai nake so ki ba ni. Sannan ki sanar da ni a ina zan same ki?"

_Tafiya na ci gaba da yi ya biyo ni yana ci gaba da roƙon lambata amma ban sake bi ta kan shi ba, har na isa gidansu Ummata da ke Bafarawa estate._
_Kwana biyu tsakani ina tsaka da aiki aka aiko wani yaro ana kira na, ina gunguni haÉ—i da tsaki na fito. Saboda takurar da Umma ta yi mini a kan dole sai na je na ga wanda ke nema na. Da mamaki na bi shi da kallo saboda tunanin wa ya sanar da shi unguwar balle gidan da nake. Murmushi ya bi ni da shi hannun shi a aljihu ya ce,_
"Kin yi mamakin gani na ko? To Hausawa sun ce mai son ɗan tsuntsu shi yake bin shi da jifa, shi ya sa na biyo sawunki sau da ƙafa har na ga gidan. Saboda na gani kuma na yaba da kalar tarbiyyarki. Hakan da kika ya ƙara miki matsayi a zuciyata da ƙima a cikin idanuwana. Don haka ga Muhammadu Mukhtar da fatar ya yi miki a matsayin mijin auren ki!".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.