Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 60 of 86

"Me kika yi masa?"

Ƙirjina yana bugawa na yi maganar saboda sabon ɓacin ran da ya ziyarci zuciyata.
"Girki na zo zan É—ora amarya ta ce ba zan É—ora shi ba, ni kuma ganin kin ce na yi kafin ki dawo ya sa na ci gaba da yi. Ban san ya aka yi ba ina tsaka da kwasar abincin na ji muryar Abbanmu yana ta zagi na. Shi ne ya same ni a kitchen É—in yana ta dukana, kuma ya É—auke abincin duka ya ce ba za mu ci ba tun da amarya ta yi girki shi kowa zai ci."

"To fa! Abin har ya kai can?"
"Har ya wuce ma! Kuma wallahi matuƙar kika sa ta raina Barcy sai na ci uwarta a cikin gidan nan."
Zancen Mukhtar kenan a sama yana ba ni amsar tambayar da na yi wa kaina cike da mamaki. Na saki hannun Ummu Salma na tarye shi gaba da gaba na ce,
"Sai dai ka ci ubansu waton kai kenan! Don wallahi daga kai har wannan ƙanjamammar amaryar holoƙon da kake tinƙaho da ita; kun yi kaɗan ku ci zarafin yarana ba bisa haƙƙinsu ba. Abinci da ta dafa kuma ni na ba ta umurnin dafawa, saboda ba zan sake zama wata ballagaza tana hora mu da yunwa ba."
"Ke kika ba ta umurni Barcy kuma ta hana ta, saboda tun kafin su dawo gidan ta yi girki. Kuma shi za a ci dole don tuni na kyautar da wanda ta dafa."
Baki a sake nake bin fuskarsa da kallo saboda mamakin zancensa na 'ke kika saka ta Barcy ta hana'.
"Waton ita Barcyn ce za ta dinga ba mu umurnin abin da za mu yi a gidan da wanda za mu bari?"
"E! Saboda ni ce amarya kuma har yanzu ina cikin kwanakin girkina. Ki bari idan girkin ya dawo hannunki ki yi duk abin da kike so babu ruwana. Amma yanzu kam babu wanda zai É—ora girki a cikin gidan nan bayan wanda na dafa."
Martanin Barira kenan tana girgizar jiki tare da riƙe ƙugu. Ta so ba ni dariya amma na fuske na ce,
"Sannu shafaffiya da mai jikar sarauniyar Ingila 'yar gidan Sarki Macciɗo. To na rantse da Allah zan yi bikin watan cin ubanki a cikin gidan nan. Ko ki fita sabga ta da yarana; ko na nuna miki na fi ki sanin makamar iskanci da rashin mutunci. Abincinki kuma wallahi daga ni har yaran ba za mu sake jiransa ba, ke da cin abinci ya kawo gidan ki buɗe ciki ki yi ta zubawa, nawa kaso da na yarana duka mun bar miki. idan kin ƙoshi ki miƙa saura gidanku don na san suna da buƙata."

Baki a sake take kallona tare da cizon yatsa tana faÉ—in,
"Kai kai kai!"
Kansa na juya ina faÉ—in,
"Kai kuma mijin ta ce! Namijin ho-ti-ho! Ɗankwali ya ja hula! To ka sanar da ita babu kwanakin girkin kowa a kaina. Idan ma akwai duka na bar mata don haka ku sake wa 'ya'yana mara su ji daɗin fitsari. Kuma daga yau abincinmu daban za mu dinga girkawa, idan ka ji tsoron Allah ka ba mu namu haƙƙin. Domin ka rage wa kanka guzurin mugun bugun da Mala'iku za su yi maka a ranar lahira. Idan kuma ka bijire kamar yadda ka yi a baya, ina maka albishir za ka girbi duk abin da ka shuka khairan ko sharran. Na zare hannuna a cikin sha'anin girkin matarka, ni ma daga yau babu ruwanta da duk abin da za mu ci ko mu sha, a cikin gidan nan ni da yarana. Saboda ba za mu zauna tana gasa mana aya a hannu ba saboda abinci."
" Ina ƙare faɗar hakan na yi gaba zan shige ɗakina, sannan na yi saurin juyowa ina faɗin,
"Gass nawa ne, ni na saya da kuɗina, repelling ma ni nake yi ba wani yake yi mini ba. Daga yau kada a sake taɓa mini kaya ko da ɗora ruwan zafi ne!"

"Wallahi ni kuma ba zan yi girki da itace ba!"

Abin da Barira ta yi hanzarin faɗi kenan tana murguɗa baki. Saboda Ummu Salma ta faɗa mini ita ce ta nuna mata yadda ake amfani da shi. Lokacin da take girkin tana 'yan waƙe-waƙen farinciki, lokacin da wata ta kira ta a waya baki a sake take faɗin,
'Ke yarinya na wuce nan! Sabod Allah ya kawo ni gidan arziƙi, inda ba zan sha wahalar hura wutar ice ba. Gass cooker Hajiya shi nake girki da shi yanzu haka har na kusa gamawa... Ja can yarinya! Allah dai ya ba ku irin tawa kawai, don ni na tako arziƙi na wuce da sanin ku ƙananun ƙwari.'

Tuno labarin na yi murmushi mai sauti sannan na ce da ita, "Wannan kuma mijinki za ki faÉ—awa ba ni ba!"

"To ni ko idan dai da ice zan dinga girki, sai dai kada kowa ya ci abinci a gidan nan, daga ni har shi wallahi."

"Kanku ake ji!"

Kafaɗa na ɗaga, sannan na juya na shige ɗaki yarana suka biyo bayana, Haidar na kalla raina a ɓace saboda yadda ya zama kalar tausayi. kuma na sani ba komai ba ne face yunwa don ko kaɗan bai da haƙurin ci.
Jakata na ajiye da sauri na nufi kitchen É—in, dole na yi tsaye ina wassafa abin da zan yi a lokacin. Saboda komai na kayan abinci an kwashe babu komai na sarrafawa, kuma na san ina da sauran Indomie da kayan tea waÉ—anda ni na saya da kuÉ—ina, ba waÉ—anda Mukhtar ya kawo ba a daren da aka kawo Barira.
Amma duka an haɗa an kwashe domin a nuna mini iyakata. Na fito kitchen ɗin cikin ƙoluwar ɓacin rai na ƙwala wa Haidar kira, umurni na ba shi ya je gidan Maman Taufiƙ ya ce, na ce ta zuba musu abinci su ci shi da Iman.
Sannan na koma ɗaki na ɗauki kuɗi na fice tamkar wata zararriya, saboda tsananin ɓacin ran da nake ciki. Adaidaitasahu na hau kai-tsaye ta ajiye ni shagon da nake siyayya, na ɗauki duk abin da muke da buƙata tsakanin abin kari da na girki har da rabin buhun shinkafa.
ATM ɗina na bayar ya zuƙe kuɗin da ke ciki tas, sannan sauran da ya biyo ni na ce da shi mu tara ƙarshen wata. Don a lokacin kwanaki ne kawai suka rage a yi albashi.
Cikin Napep aka loda mini kayan na nufi gida. Inda na taras da Mukhtar yana ta bala'i har da kumfan baki, a kan na je roƙon abinci a wani gida bayan ga wanda Barira ta dafa.
Ƙanzil ban ce da shi ba, illa yaran da na tambaya sun ci abincin suka ce da ni sun ci har sun ƙoshi. Sanyin daɗi na ji ya tsirga mini sosai a raina, saboda ganin kular da ta zubo musu abincin na tabbatar da zai wadace su.
Tuwon garin masara na fara yi sannan na kaÉ—a miyar kuka, saboda ban da kuÉ—in nemo cefanen wata miyar bayan kukar da nake da ita.
Duk da babu ƙiren nama ko kifi ta yi daɗi sosai, don ta sha daddawa da waken da na kwankwatsa cikin kayan yaji, wanda nake amfani da shi a wasu lokutan, a watsa a matsayin naman miya.
Ban samu damar yin sallar Zuhur ba sai da aka yi kiran Asr, saboda ina gudun na bar girkin Mukhtar ko Barcynsa su yi mini ganganci.
Abincin na kwashe duka a kula na kawo ɗakina har miyar, na ce da yaran su ƙara abincin kafin su tafi makaranta. Ummu Salma da Iman suka ce da ni sun ƙoshi, suka fara shirin makaranta Haidar kawai ya ce bai ƙoshi ba, na zuba masa sannan na yi arwala na yi sallah.
Ruwa na fara watsawa sannan na fito cikin sauri, saboda surutun da Ummu Salma take yi wa Haidar a kan ya ja sun yi latti. Don huɗu da rabi har ta gota saɓanin dokar makarantar da ake zuwa ƙarshe uku da rabi.
Gani na ya sa suka fice shi ma ya bi su da gudu yana faÉ—in su tsaya masa. Ina tsaka da shafa mai a jikina Mukhtar ya faÉ—o É—akin kamar an jefo shi yana faÉ—in,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.