Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 52 of 86
****
A ƙofar gidanmu maƙociyar tawa ta sauke Firdausi da Amina tare da Maman Taufiƙ da Sajida. Saboda su Ummu Salma tun kafin mu baro wurin na kira Najib ya ɗauko su.
Godiya muka yi mata sosai, sannan ta shige gidanta da motarta bayan an ba ta ledar walimar. A nan Sajida ta bai wa kowa ledarsa Maman TaufiÆ™ ta yi mana sallama ta shige.
Firdausi da Amina saboda mazajensu za su zo É—aukar su, tare muka yi gidan suna ta tsokana ta.
A nan ma bayan mun yi sallah wata sabuwar hira aka dasa. Sajida ta tuntsure da wata mahaukaciyar dariya tana cewa,
"Wai Aunty kin ji ƙaimon da hannunta yake yi, tamkar busassar takarda?"
Kai jama'a😂
Ni dai babu luwanaðŸƒðŸ»â€â™€ï¸ðŸƒðŸ»â€â™€ï¸
D.AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*TALATIN DA ÆŠAYA.*
"Innalillahi Sajida! Lamarinki da girma fa! Shi kenan kin saka wa yarinya ido komai nata kin kushe."
Zancen da na yi kenan ina ƙoƙarin danne dariyata, saboda iskancin Sajida a kan amaryar Mukhtar ya shalle tunanina.
"Tsakani da Allah ni ma dai na raina ganin ta! Sai ka ce wanda ya hango ta idonsa rufe?" Amina ta ƙare maganar tare da tagumi, bayan jimamin da ya bayyana kan fuskarta a zahiri.
"Hmmmmm! Ni gaskiyar ma ta yi mini yawa walla..."
Kiran da ya shigo wayar Firdausi ya datse sauran maganar da ke ƙoƙarin fitowa daga bakinta.
"Yawwa! Bari na fito!"
Abin da ta faɗa kenan ta miƙe tare da saɓa jakarta a kafaɗa ta ce da mu, "To ni zan wuce, sai gobe kuma idan mun dawo tarbar amarya." Sallama su Amina suka yi mata ta fice, na raka ta har bakin ƙofa. Zuciyata a cunkushe na ce da ita,
"Wai kin san Mukhtar bai ba ni komai na faÉ—ar kishiya ba?"
"Cabɗijam! Hmm! Ki zura masa ido kawai, don babu inda cin amana take zuwa wallahi! Ko an yi gaba sai haƙƙi ya dawo da mutum baya. Idan ban da ya rasa mafaɗi; wannan ƙazamar yarinya me zai yi da ita?"
Shiru kawai na yi saboda hawaye masu zafin da suke malala a kan fuskata. "Ki daina damar da kanki a kan Mukhtar! Na sha faɗa miki tun ba yau ba, saboda kuka bai da amfani a wurin da ba za a share maka hawaye ba. Da yardar Allah sai haƙƙinki ya fita a kan wannan auren takaicin da ya ɗebo wa kansa. Dauriyar da kike yi ki ƙara ƙaimi, domin salon takun kisa da mummuƙe ne daga kan shi har amaryar da danginsa duka. Marsiyatan banza azzalumai, marasa tsoron Allah..."
Odar da maigidanta yake yi ya sa ta fice da sauri fuskarta a haɗe cikin ƙololuwar ɓacin rai. Domin tana matuƙar jin haushin halayen Mukhtar da matsin lambar da Umma take yi mini a kansa.
Abin da na sani ne, da ace tana da iko; da tuni ta raba aurena da Mukhtar. Saboda ƙawata ce da ba na ɓoye mata komai nawa, wani lokaci ma idan ta zo gidan tana gani da idonta. A wasu lokutan baya da suka shuɗe ma; ita ce ƙashin bayan ɗauke kwatar lalurorin da Mukhtar ya bar ni da su a cikin gidansa.
Sai da motarsu ta tashi sannan na koma cikin gidan bayan na daidaita natsuwata. Shiga ta ɗakin ke da wuya Amina ta miƙe tana faɗin, "Ni ma zan tafi, ga shi can a ƙofar gida ya zo!"
Ita ma na raka ta tare da yi mata godiyar karamcin da ta yi mini. Na dawo muka dasa wata sabuwar hira da Sajida, inda take nuna zallar takaicinta a kan auren Mukhtar. Na dinga nuna mata komai nufi ne na Allah kuma babu wanda ya isa ya kauce wa ƙaddarar shi.
Bayan kowa ya yi bacci tsakanin Sajida da su Haidar, na yi shiru ina nazarin makomata ta gaba idan rayuwa ta ci gaba da shura mini a haka. Ƙarar shigowar saƙo ya sa na janyo wayata na duba, alert na yi tozali da shi wanda ya sa babu shiri na tashi zaune.
Dubu talatin na gani É—auke da sunan MD na asali ALIYU S. NOMA, a matsayin wanda ya turo mini da kuÉ—in. Shiru na yi ina nazarin waÉ—anni irin kuÉ—i ne ya turo mini, saboda ban san wata ajandar da muka yi da shi ba, wadda kuÉ—in za su zo mini da yawa haka.
Ga shi dare ya yi ƙarfe ɗaya saura balle na nemo shi na ji kuɗin na mene ne. Shigowar wani saƙon ya sa na rarumi wayar da sauri na duba, babu shiri jikina ya yi sanyi ƙalau, saboda wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata.
'Ga tawa gudunmawa nan, Allah ya ba ku zaman lafiya'
Abin da na yi ta maimaitawa a zuciyata kenan, kuma na kasa ɗauke idanuwana a kan saƙon. Juya kwanciyata kawai na yi saboda ban san da wace kalma zan yi masa godiya ba.
Duk da har lokacin ban daina jin haushinsa a raina ba. Haka na yi kwanan daÉ—i da tunanin abin da zan yi da kuÉ—in idan safiya ta waye.
****
Da safe danginsa suka cika gidan ana ta hada-hadar dafa abincin bikin. Duk da na ji zafin rashin saka ni cikin hidimarsa, amma haka na danne zuciyata saboda ba na so a ga kasawa ta.
Sai dai ko kaÉ—an ban saka hannuna a cikin aikin ba. Abinci ma nawa na sa aka girka mini a gidan Maman TaufiÆ™, da kuÉ—in da MD ya ba ni na yi komai a wadace.
Na shiga tarbon mutanena da ke zuwa daga dangin Ummata da waÉ—anda muke gaisuwar mutunci. Duk da ban yi gayya ba an yi mini kara sosai.
Wanka kala biyu na ɗauka na safe daban na marece daban, musamman shiga ta biyu da na saka baƙar shaddata kuma ɗinkin ya zauna jikina daram. Sannan na ƙawata kwalliyar da ɗan kunne da sarƙata mai kama da zinari. Don waɗanda ba su san zinarin a ido ba; kai-tsaye za su gasgata ita ce a kunne da wuyana.
Na saka gyalena ja da takalmina half shoes jajaye da wata ƙaramar jaka mahaɗinsu, bayan agogon fata baƙi da ke tsintsiyar hannuna.
Na fito sharr ina ta haske idon maƙiya tamkar sabon wata ɗan daren goma sha biyu, saboda duk inda na doso sai an lalace wurin kallona da sakakken baki. Haka ma idan na juya baya hararar 'yan hassada ta raka ni tare da cizon yatsan ba haka aka so ba; wai ƙanen miji ya fi miji kyau.
Tsakar gida muka fito ana ta É—aukar hotuna, saboda mai hoton ma Sajida ta nace a kan sai ta nemo shi. Domin kwalliyar da muka yi kada ta tafi a iska ba tare da an bar wa bikin tarihi ba.
Muna tsaka da hotunan ni da su Ummu Salma sun saka ni tsakiya an saka mana rumfar hoton. Sai ga Mukhtar ya shigo yana baza babbar rigar shadda fara da ke sanye jikinsa. Ihu aka saka ana faÉ—in ga ango nan, saboda ya yi kyau gwanin burgewa don daman can bai da makusa a halittarsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.