Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 45 of 86
"Babu komai akwai Allah!"
Maganar da na yi kenan a zuci ba tare da na san ta fito fili ba. Gaba su Ummu Salma suka saka ni da tambayoyi.
"Me ya faru Mama?"
"Me Sajidar ta faÉ—a ne?"
"Babu komai ku jira na je gidan Maman TaufiÆ™ na dawo yanzun nan!"
Daga haka na koma É—aki na janyo hijabina, waya a kunnena na fice muna magana da Firdausi.
"E da gaske ne mana! Satin nan ma za a kawo amaryar."
Amsar tambayar da ta yi mini kenan daga bakina, kafin ta gama jimami ta samu sukunin cewa,
"Anya Mukhtar kansa É—aya kuwa?"
Murmushi na yi mai sauti sannan na ce da ita,
"Me kika gani?"
"Yo idan ba don Allah yana son tona masa asiri ba, me zai sa ya rikito aure yanzu? Bayan ke ɗin ma bai iya sauke haƙƙinki ba amma yake neman ɗebo wa kansa masifa."
"Ya ji ya gani ne! Kuma kika sani ko ya samu lafiya ni ce bai bari na gane ba?"
"Shi dai ya sani, namu kallo ne kawai! Amma don Allah kada ki nuna masa komai a kan auren nan. Ki bar shi da kan shi zai yi regretting É—in me ya sa ya aikata."
"Na bar shi ai! Tuni na zamo 'yar kallo."
Daga haka muka yi sallama na shige gidan Maman Taufiƙ zuciyata babu daɗi, don daman can ƙofar gidan na tsaya saboda ba na so na shiga gidan ba mu gama maganar ba.
Zama na yi a kan ɗaya daga cikin kujerun falonta, bayan ta amsa mini sallama ta yi mini jagora har cikin falon, sannan ta fice. Lemun Coca-Cola a ɗan ƙaramin tire ta ajiye gabana, sannan ta zauna tana faɗin,
"Oyoyo Maman Haidar! Yau na so shiga gidanki Amini ya kawo mini aikin kajin da ya hana ni fitar."
"Ni ma yanzu wani uzuri ya shigo da ni, wurin mai hajarki nake so ki kai ni na zaɓo kaya. Sannan ki yi mini jagora wurin mai ɗinkinki ya rantsama mini ɗinki mai kyau, irin na gani na faɗa da tsokanar magana."
Da dariya na ƙare maganar saboda ƙoƙarin kore damuwar da nake ciki a kan fuskata.
"Wai don Allah da gaske auren nan zai yi?"
Tambayar da ta yi mini kenan bayan ta shiga natsuwarta.
"Tun ranar ai na faÉ—a miki, yanzu haka a cikin satin nan za a yi auren idan Allah ya ara mana numfashi."
"Hmmmmm! Ikon Allah!"
Abin da ta faÉ—a kenan sannan ta janyo wayarta ta yi kira, mintuna a tsakani bayan an É—auki wayar ta ce,
"Hajiya Ruƙayya Wada, kaya nake so ki turo mini yanzu na zaɓa. Ki haɗo da sarƙoƙi da takalma half shoe's masu kyau kalar ya yi."
Tana ƙare maganar ta ajiye wayar tare da rungume hannu ta ce,
"Jarumtarki tana burge ni Maman Haidar. Ina ma zan iya kwatanta ko da rabinta idan Amini ya tashi aure? Amma har ga Allah na san ba zan iya ba."
"Za ki iya! Matuƙar kika saka kanki."
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce, "Mu bar maganar! Wane shiri kika yi wa kanki a matsayinki na Uwargida?"
"Shiri kuma?"
"E" Ta ba ni amsa, cikin rashin sanin inda zancenta ya dosa na ce,
"Wane iri fa?"
"Gyaran babbar hedkwatar mana! Don ke ma kin san ba zai yiyu amarya ta zo ta same ki a haka babu wani canji ba. Saboda ita kanta sai ta yi gyara sosai kafin ta shigo, to ke ma me zai hana ki yi gyaran da za ki mayar da tsohuwar shimfiÉ—arki sabuwa dal?"
"Zan yi! Yanzu haka ma ina kan yi."
Amsar da na ba ta kenan, don ba na so ta fara nuna mini ban iya komai ba a kan tattalin miji kamar yadda ta saba.
"Kin yi farar dabara, bari na ƙaro miki wasu zafafan da aka kawo mini daga Maiduguri jiya. Don mazan nan idan babu sabon service kullum idanuwansu suna kan leƙe-leƙen wasu matan. Amma idan kina gyara jikinki komai cif-cif, da wuya su yi miki kallon raini balle su nemi ɗauko miki wata masifar a waje."
Ta miƙe ta kawo mini kayan mata kala-kala, tun daga kan shu'umar humra har wani ɗan matsin da ta tabbatar mini yana mayar da tsohuwa yarinya. Sannan turaren tsugunno da na jiki, bayan tsimin da ƙamshinsa kaɗai zai sa mutum ya ji sha'awar shan sa.
Leda na zuba su duka, na ce da ita sai na je gida zan sha, ta matsa mini na sha tsimin a nan saboda ya yi saurin kama jikina. Domin akwai buƙatar na sha shi kamar sau uku kafin bikin, domin ya haɗe mini jiki ta yadda idan na karɓi girki zai rasa bambance wace ce amarya a tsakaninmu.
Kasa musa mata na yi, saboda ba na so ta gano ba na so, kaɗan na kurɓa na rufe gorar swan ɗin da ta cika mini ita taf! Hira muka ci gaba da yi a kan amfanin kayan mayen, tare da yi mini bayanin yadda suke yi mata aiki sosai har aka kawo kayan.
Kala biyu na zaɓa masu kyau shadda da lesi, sannan na zaɓar wa su Ummu Salma atamfa ɗaya da shadda gizna, wadda ba ta kai kuɗin tawa ba yadi bakwai su uku. Saboda na san estimate ɗin abin da suke ci don na fara koyon ɗinki tun kafin na yi aure. Yanzu ma ina da experience sosai a kan abin da ya shafi ɗinkin duk da ba na yin sa.
Gyale, takalmi da jaka na samu mahaɗin shaddar da lesin. Sannan na zaɓar mana sarƙoƙi nawa set biyu su Ummu Salma ɗaiɗaya. Na ɗaukar wa Haidar 'yan kanti ɗaya shi ma ya yi kala biyu kamar yadda su Ummu Salma za su yi. Maman Taufiƙ ta kira mai kayan aka haɗa lissafin kuɗin dubu saba'in da uku cif. Shiru na yi ina nazarin kuɗin a raina, saboda ba na so na yi abin da zai ƙure mini maneji.
Kamar Maman TaufiÆ™ ta fahimce ni ta ce, "Kayanta akwai tsada, amma kuma quality ne za ki ji daÉ—insu sosai."
"A ido ma kayan kowa ya gani zai san sun ci kuÉ—insu. Amma akwai uzurorin da ke gabana, zan rage kala É—aiÉ—aya mu ji nawa kudiyn za su kama."
"Kada ki rage ki bar su kawai, ba ta da matsala duk lokacin da kika samu dama da ƙire-ƙire ma za ki biya ta ba sai duka ba."
"Gaskiya na ji daɗi Maman Taufiƙ! Saboda a yanzu samun masu haƙurin bashi 'yan kaɗan ne a wannan lokacin da muke ciki."
Ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce, "Ai Maman Marwan ba ta da matsala ko kaɗan, kuma ta iya hulɗa da mutane sosai. Duk masu sayen kayanta sun san da hakan, shi ya sa ba na iya sayen kaya a wurin kowa sai wurinta. Ga quality, ga sauƙin kai, kuma babu matsi balle a dame ka da aiken kawo kuɗi wata ya ƙare. Tana ɗaga ƙafa musamman idan ta san kana cikin masu biya babu taurin bashi."
"Ai kuwa in Sha Allah za ta same ni mai cika alƙawari, don ni ma ba na son bashi sai ta kama dole. Ki ce ta turo account yanzu na tura mata 20k ɗin da nake da ita ƙasa, idan aka yi biya zan ƙara mata wani abu in Sha Allah!"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.