Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 35 of 86
"Kwana biyu kin ɓuya!"
Maganar da ta yi mini kenan a lokacin da na gutsura doghnut ina taunawa. "Shirye-shiryen zuwan amarya muke yi. Shi ya sa kika ji ni shiru, ga kuma aiki da yake hana ni zama kullum ina zarya kan titi."
Kallo mamaki take yi mini sannan ta ce, "Wace Amarya kuma?"
"Amaryar Mukhtar!"
Amsar da na ba ta kai tsaye kenan, murmushi a kan fuskata. Baki a sake take kallo na bayan tagumin da ta rafka, dariya na shiga yi mata alamun ko a jikina illa tsabar farincikin da nake ciki. Wanda ya kasa ɓoyuwa har sai da ya bayyana kan fuskata.
"Yanzu ke don Allah a kan auren Mukhtar kike wannan murnar?"
"Sosai ma! To miye cikin ido ban da ruwa? Ai inda akuyar gaba ta sha ruwa, ko ta baya idan ta zo a nan za ta sha."
"Hmmmmm! Kina wasa da lamarin maza Maman Haidar. Ke a tunaninki abin da ya yi miki shi zai yi wa wata idan ta shigo?"
"Sosai ma kuwa! Don ƙwaryar sama ce take dukan ta ƙasa. Kuma ni wannan auren ma da ina da dama har sadaki ni zan biya masa. Domin kawai ya gano na fi shi farinciki da ƙulluwar auren."
"Lalle da sauranki har yanzu Maman Haidar. Ai wallahi ni da na ga ranar da Amini zai yi aure, gwara na ga ranar mutuwata."
Dariya ta suɓuce mini babu shiri, da abun ya yi mini daɗi ma har da bajewa na yi a kan kujerarta riƙe da ciki. Saboda zancenta ba ƙaramar dariya ya ba ni ba, domin zurfin da ta yi a kan sha'anin maza, ya nuna har yanzu ba ta san zafin duniya ba.
Natsuwar dole na gayyato, saboda yanayinta da na ga ya juya zuwa kalar tausayi.
"Ko ni na samu mijin ƙwarai wanda ya san zafina, wajibi ne kuma dole na yi kishin abuna. Amma kuma ba zan zafafa kishina irin haka ba, saboda ba gare ni aka fara ba kuma ba za a ƙare kaina ba. Sannan shi ɗa namiji, a duk lokacin da kika zafafa kishinki a kansa, matuƙar ba ki yi dace da mai dogon nazari da hangen nesa ba. To zai yi miki kallon wata shashasha wadda ba ta san abin da take yi ba, ƙarshe ma ya ce ba kya son zaman lafiya, ko kin cika fitina da janyo abin da zai kawo muku faɗa. Saboda a lokacin idonsa a rufe yake da son auren, duk abin da za ki yi masa ba zai burge shi ba, matuƙar ba goya masa baya za ki yi a kan auren ba."
"Ai kuwa wallahi sai dai kada ya gani, domin ba zan taɓa goya masa baya ya yi mini kishiya ba. Cabɗijam! Allah kada ya nuna mini wannan ranar, don na san tun kafin lokacin auren ya yi zan mutu saboda mugun kishin Amini da nake yi. Shi ma ya sani ba zai taɓa zo mini da irin wannan zancen ba."
Shiru na yi ina kallon ta, domin idan akwai naƙasunta da na sani duniya bai wuce kishi ba. Kuma ina yi mata uzuri saboda shaƙuwar da ke tsakaninta da Aminin mijinta. Wanda saboda tsabar so da shaƙuwar da ke tsakaninsu yake kiran ta Aminiya ita ma ta kira shi Amini.
"Ni dai kam! Ko a kwalar rigata Maman Taufiƙ. Idan zai yi huɗu a rana ɗaya wallahi babu abin da zai ɗaga ni sama balle ya buga ni a ƙasa. Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Kuma wanda duk ya ce zai iya haɗiye gatari ya dace a riƙe masa ɓota."
"Wallahi Zaituna kina ba ni mamaki, shin wai ba auren soyayya kuka yi da Abban su Haidar ba?"
"Soyayyar gaske ma, irin ta bugawa ga jarida a yi talla. Amma yanzu, ƙiren sonsa ba na ji a cikin zuciyata, kamar yadda ko wulagawar shi na hango daga nesa, sai na ji haushin sa ya yi mini rumfa."
"Anya ba namijin dare ne yake aurenki ba?" Tambayar da ta jefo mini kenan na ba ta amsa.
"Idan ma shi ne ya burge ni, domin ya nuna zallar kishin da yake yi mini wanda ba ya son kowa ya raɓe ni. Domin ina da tabbacin zai ba ni kulawar da za ta gamsar da ni, kuma zai hana ni kukan kaɗaaicin da nake yi yanzu."
"Hu'ummm! Kin yi nisa Zaituna, amma ni kam har abada ba na fatar Amini ya yi mini kishiya ko da a mafarki. Ke akwai wata da ta so zautar da ni a kan nacin da ta yi masa ya aure ta, don bala'i macen da yaranta har sun je jami'a. Wai a haka ta nace masa dole sai ya aure ta tun da mijinta ya mutu ya bar mata gado. Ai na rantse da Allah ranar da na gano, daga ni har shi ba mu yi bacci ba, asubar farin na bar garin nan na yi Kano. Domin gabaɗaya idona rufewa suka yi ba na hangen komai a lokacin face mutuwata. Abin baƙinciki kuma babu wanda ya goya mini baya a gidanmu, sai laifina da aka dinga gani ana ƙoƙarin nuna ya fi ni gaskiya. Sun kasa gano zafin da nake ji idan na tuno girman matar da manyan 'ya'yanta. Don akwai wata 'yarta da ta ci ta ƙoshi, wadda ko yanzu aka ce ta haifi yara uku ba zan musa ba. Amma wai a hakan take son Amini ya aure ta don baƙar zalama irin ta wasu ƙattin mata."
ðŸ¤sannu Maman Taufiƙ😂
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ASHIRIN DA BIYU.*
Dariya na sha sosai har ta nemi ƙulle mini ciki, saboda maganganun Maman Taufiƙ sun saka ni dariya ba tare da na shirya ba. Fuskarta na kalla bayan na gama dariyar, hadarin da fuskar ta ɗoro tare da ƙwafar da na ga ta yi, alamunta ya nuna mini har lokacin kishin matar bai daina cizon ranta ba.
"To ke Maman Taufiƙ, ai ita ce ke son shi idan na fahimci labarin da kyau. Da kin bari an yi auren, wataƙila da yanzu har mu maƙotanki mun je hajji. Saboda bauta ce kawai za ta zo yi miki tun da kin fi ta power a wurin Baban Taufiƙ."
"Hmmmmm! Ba za ki gane ba!"
Zancen da ta yi kenan tana haÉ—e fuska tamkar ta yi kuka, kafin ta cire tagumin da ta rafka hannu bibbiyu ta sake cewa,
"Kin san me? Ko da za ta kwanta ƙasa na dinga taka ta da ƙafafuwana saboda biyayya, ba zan taɓa cire takaicin ta a raina ba. Wai ko ki san yadda nake kishin Amini kuwa? Ke ni fa da dai a ce ya haɗa ni sharing ɗinsa da wata, gara kawai ni na haƙura na bar wa kowace ce shi. Na fi son haka da a ce na zauna baƙinciki ya kashe ni."
"Ba fa za ki mutu ba! Matuƙar ba ke ce kika ƙwallafa wa kanki hakan ba. Saboda duk abin da kika gani daman can muƙaddari ne daga Allah, don haka ki daina zafafa kishinki gudun ki saka kanki matsala a banza."
Na yi maganar cike da burin saka mata ƙwarin gwiwa a zuciya, sai dai ko kaɗan zancen bai yi tasiri ba. Domin idonta a rufe ta ce da ni,
"Ni fa komai za ki faÉ—a in dai a kan zancen kishiya ne, to ba zan fahimta ba balle na gane. Don haka mu bar zancen kawai raina suya yake yi sosai wallahi."
Shiru ya ratsa tsakani sannan na sauke ajiyar zuciya, bayan na dawo daga zuzzurfan tunanin da na lula, a kan tashin hankalin da za ta shiga a lokacin da ta ji Baban TaufiÆ™ yana neman aure, domin da idanuwana na gan shi da wata bazawara a bayan layinmu suna taÉ—i.
Saboda kusa da gidan su bazawarar nake zuwa kitso, da tunani fal raina na shiga gidan a lokacin, bayan zancen zucin da nake yi. Ina ta jefa wa kaina tambayoyin da ba amsa, a kan miye haÉ—in shi da ita? Duk da yanayinsu ya bayyana mini zahirin abin da ya haÉ—a sun. Amma ban gasgata ba sai lokacin da bazawarar ta shigo gidan ana tsaka da yi mini kitso, mai kitson tana 'yar dariya ta ce da ita,
'Har ya tafi?' Ita ko bakinta har kunne ta zauna tana faÉ—in,
'Ya tafi! Ai mutumin ya san kansa, sosai yake da qualitys É—in da nake so, kuma nake fatar samun su a wurin namijin da nake muradin ya zama mijina. Yanzu haka duk da ba mu jima tare ba, amma ya nuna mini shi ba ya son a ja lokaci. Idan na shirya wata biyu masu zuwa a yi komai a gama.'
'Caɓji! Lalle wannan da zafinsa ya zo.'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.