Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 36 of 86

Haka na yi ta tuno hirar bazawarar da mai kitsona, wadda har suka ci suka cinye ban ce da su ƙanzil ba. Saboda ba na so na katse musu zancen, sannan kuma ba zan iya shiga sabgar da ba a kasa ta da ni ba.
'Yanzu idan ta ji wannan batun ya za ta yi?'
Tambayar da na jefi kaina da ita kenan, wadda ban samu amsarta a zuciyata ba na fara jiyo sallamar da su Ummu Salma suke ta rafkawa.
Tare muka amsa musu ni da Maman Taufiƙ, sai da aka ba su umurni sannan suka shigo. Gayar da ita suka fara yi ni ma suka gaishe ni, na miƙa musu makulli suka fice suna faɗin sai na zo.
Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da ita, "Wallahi kin sa jikina ya yi sanyi Maman Taufiƙ. Saboda har raina, ba na jin daɗin zafin kishin nan naki, da ina da iko da na rage miki shi ko da kaɗan ne. Domin ina jin tsoron abin da zai faru a lokacin da ƙaddarar aure ta haɗa Baban Taufiƙ da wata."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Don girman Allah ki daina ambatar wannan magana, kada tsautsayi ya sa 'yan amin su amsa ki janyo mini masifa. To idan ma wannan ne in Sha Allah babu shi babu aure nan gaba, saboda ni kaɗai na ishe shi rayuwar duniya, kuma ni kaɗai yake da buri zama da ni. Baya hangen kowace mace balle ya yi mata kallon daraja, saboda Allah ya karɓi addu'ar da nake yi masa koyaushe. A kan duk matan duniya, fuskarsu ta koma ta akuyoyi a idonsa, balle ya ga kyawunsu ya ƙyasa ya ɗauko mini jangwam!"
"Hmmm! Kin fi ƙarfina Maman Taufiƙ! Ni zan tafi don babu amfanin duk wata maganar da zan ƙara yi a kan hakan. Saboda kin fi ƙarfina, amma duk da haka, na yi alƙawarin zan dinga yi miki addu'a a kan wannan kishin balbal, domin ina da burin Allah ya rage miki shi ki samu sukunin zuciya ko don ki ji daɗin fuskantar rayuwa."
Zancen da na yi mata kenan a lokacin da na miƙe, fuskarta a haɗe ta rako ni tana faɗin, "Ban ji daɗin wannan zuwan ba, domin kin fama mini mikin da na daɗe ina jinyar zuciyata kafin ya warke."
"Kwantar da hankalinki, in Sha Allah sai kin daÉ—e ba ki gan ni cikin gidan nan ba. Sai dai kuma hakan ba shi zai hana ni yi miki fatan shiriya daga wannan azababben kishin naki ba."
Ina gama faÉ—in hakan na fice gidan, ta raka ni da faÉ—in, "Kishi halas ne! Ke da ba kya yi kuma ai kin hutar da kanki daga ladar da ake samu."

Dariya na ƙumshe gudun ta ga damata, sai da na shiga gida sannan na tuntsure da dariyar tamkar wata zautacciya, 'Waton shi ma zazzafan kishin miji ibada ne da ake samun lada a ciki idan an yi?' Tambayar da na yi wa kaina kenan ina dariya.
"Wallahi sai dai kada na samu wannan lada, da dai a ce na yi kishin Mukhtar irin haka. CabÉ—ijam! Da sake!"
Maganar da na yi kenan a fili lokacin da nake shiga falon, kiran sallar magrib da na ji an fara yi ya sa na ce da yaran,
"Oya a tashi a yi sallah."
Sannan na shige É—akina na faÉ—a toilet. Har na gama sallah tunanin hira ta da Maman TaufiÆ™ nake yi, ban tashi daga kan sallayar ba sai da aka yi Isha. Na daÉ—e ina yi wa Maman TaufiÆ™ addu'a tamkar damuwarta ce kaÉ—ai abin da yake damu na.
wayata na ɗauka na fito falo inda su Ummu Salma, tare muka ci abinci da su ina duba saƙonnin da ya tarar mini. Waɗanda suke buƙatar amsa ta dole, saƙon MD na fara buɗewa raina a haɗe tamkar yana gabana.
'Na gamsu da hangen nesanki. Kuma in sha Allah na janye ƙarar daga yau. Na gode sosai!'

Mere na yi kaÉ—an sannan na tura masa 'Ana tare!'
Daga haka ban sake bi ta kan shi ba duk da yana online a lokacin. Bugun da ƙirjina yake yi, ya sa na bar WhatsApp na koma facebook. Saboda a duk lokacin da na hango sanarwar da ake yi mini a kan yana online, sai na ji gabana ya ƙire ya faɗi dam-dam!

Bacci ya ci idona, ban san lokacin da Mukhtar ya dawo gidan ba, sai da safiya ta waye muna shirin fita. Sannan na hango shi ya nufo ɗakin su Ummu Salma ya buɗe da makulli ya shiga, jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya shigo da bokitin fenti biyu a hannunsa ya shige ɗakin. Mintuna kaɗan wani ya ƙara shigowa da wasu bokitan ya shige.
Raina ya fara turirin baƙinciki, saboda haushin shigowar mutunen ba tare da Mukhtar ya sanar da ni ba, domin a tunanina ko ba gidan aure ba ne, yana da kyau a sanar wa masu gida wasu gardawa za su shigo, domin su kimtsa. A matsayin su na mata ko ba su da aure, tun da ba maza ne danginsu ba balle a ce duk ɗaya ne.
Zuciyata ta zo wuya, na dinga ji kamar na shiga na shaƙe wuyan Mukhtar a gaban mutanen, kuma na gasa masa baƙaƙen maganganun da ke cizon raina. Da ƙyar na iya furta 'Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!' A zuciyata, domin na samu sauƙin da nake ji, dangane da ingizanin da take yi, a kan na yi abin da zai rage mini takaicin da aka ƙumsa mini.
A gurguje muka shirya muka fice gidan, daga ni har yaran babu wanda ya bi ta kan shi, ko mai adaidaitan a kan hanya ya haÉ—u da mu ya É—auke mu, saboda gudun na yi jinkirin jiran shi cikin gidan, na aikata aika-aikar da zan raba halina a gaban gardawan.

Raina a jagule na kammala aikin da na taras ofishina, ko da Amina ta zo ta daɗe ban ce da ita uffan ba bayan gaisuwar da muka yi. Har sai da ta kasa haƙuri ta ce da ni,
"Yau dai kamar an sake taɓa mana ke?"
Shiru na yi mata tsawon lokaci, sannan na sauke ajiyar zuciya tare da fesar da iska a bakina na ce, "Ina muka tsaya a labarin?"
"Inda kika shiga É—aki"
Amsar da ta ba ni kenan a taƙaice cikin sanyin murya. Na cire gilashin da ke sanye a idona, sannan na gyara zama na ce da ita,

_"Baƙin tozalin da na yi ya sa na yi salatin da na yi babu shiri. Saboda falona babu komai a ciki face ledar tsakar ɗaki da agogon da ke manne jikin bango, da sassarfa na yi ƙuryar ɗakin, a nan ma sai da jiri ya so kayar da ni. Bango na yi hanzarin kaiwa na jingina bayana ina sauke numfashi da sauri da sauri. Nauyin da ƙafafuwana suka yi mini, ya janyo na kasa ɗaukar kaina a hankali na sulale na yi ƙasa. Zaman dirsham na yi rungume da Ummu Salma da ke baccinta sharkaf ba tare da ta san wainar da ubanta ke toya mini ba._
_Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin Mukhtar ya shigo da guntuwar sallamar shi, ban iya ɗaga kai na kalle shi ba balle na samu kuzarin amsa masa sallamar da ya yi. Zama ya yi kusa da ni ya miƙe ƙafa tare da janyo mu jikin shi, na yi hanzarin sakar masa Ummu Salma sannan na miƙe tamkar wadda aka tsikari. Jikina yana rawa tamkar mazari muryata tana harɗewa na ce da shi,_
"Ina ka kai mini kayana!? Ka yi gaggawar dabon fito mini da su yanzun nan, kamar yadda suka yi ɓatan dabo a cikin gidanka. Domin na tabbatar da ka san yadda aka yi suka salwanta, shi ya sa kake gwara kan mutane ka dinga zagaye-zagayen ƙarya!"
_Na ƙare maganar muryata a sama numfashina yana hawa da sauka saboda tsananin ɓacin ran da na shiga. Kansa ya duƙar ƙasa ba tare da ya ce da ni komai ba, mintuna a tsakani na fara jin sharɓen kukan shi. Mamaki fal raina na bi saman kan shi da kallo, domin idan ba kunnuwana ne suke ƙoƙarin yaudarata ba, to tabbas na ji sautin kukan shi. Lallaɓawa ya yi a hankali ya ajiye Ummu Salma, idona a kan shi har ya durƙusa a gabana gwiwa biyu, tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana sharɓar kukan da ya saka jikina yin sanyi. Kafin ya samu kuzarin yin magana cikin muryar kuka ya ce,_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.