Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 78 of 86

Umma ta fice na ja ƙafafuwana na shige ɗakinta na kwanta ina cizon takardar a bakina. Saboda tunanin maganar da Mukhtar ya sha faɗa a kan ba zai taɓa sakina ba, a haka zan ƙare cikin gidansa a wulaƙance, gudun ya sake ni wani mai kuɗi ya aure ni.

"Hmmmmm! Akwai Allah!"

Kuma ba ya barci balle gyangyaɗi😢

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*ARBA'IN DA HUÆŠU.*

_'Komai za ki yi yanzu; aikin gama ya gama sai haƙuri. Kuma zama da ni yanzu kika fara, don wallahi babu wata kotu ko alƙalin da zai sakin ki ba tare da amincewa ta ba. Yadda muka fara rayuwa tare haka za mu ƙare ta, saboda babu ɗan iskan ƙaton da zan bari ya aure ki bayan ya gama bibiyar ki da aurena, ba tare da ya yi duba da illar ɗaukar wa kansa kaya a dalilin auren da ke saman kanki ba.'_

Zancen Mukhtar kenan da ya faÉ—o mini a zuciya, tamkar a lokacin yake furta mini shi a cikin dodon kunnuwana. "Hmmmmm!"
Sautin ajiyar zuciyar da na sauke da ƙarfi kenan, saboda na yi amanna da cewa Mukhtar ba zai sake ni ta daɗin rai ba, ko kuma cikin ruwan sanyi irin haka ba. Wannan shiri ne daga hannun su Yaya Maimuna.
'Shin ta ya ya zan faÉ—a wa Umma har yanzu ina É—auke da auren Mukhtar a saman kaina?'

'Ki ƙyale ta kawai a kwashe miki kayanki. Don ko kin bar su ba za ki koma zama gidansa ba!'
Zancen da wata zuciyar ta yi mini kenan cikin ƙwarin gwiwar da take ƙara mini, a kan rabuwa da gidan Mukhtar ta wannan hanyar. Kiran sallar Zuhur ya sa na miƙe jiki babu kuzari na yi arwala. Ina tsaka da sallah yara suka shigo da gudu Haidar yana faɗin,

"Yeeee! Ni na riga ku shigowa."

Shigowar su É—akin daidai da shigowar Inna Kulu da kulolin abincinmu a hannunta. Ajiye mana namu ta yi a gabana tana faÉ—in,
"Ga abincinku nan, kuma don Allah ki daure ki ci kafin ta dawo mu je mu kwaso kayan."

Rungume ni yaran suka yi dukansu suna faÉ—in,
"Mama mun dawo!"
Murmushin yaƙe na yi wa Inna Kulu ina ƙoƙarin zare jakar makarantar da ke bayan Haidar. Sannan na ce da ita,
"Mun gode sosai Inna!"
Haidar ya fara ƙoƙarin buɗe kular abincin Umma Salma ta dungure masa kai tana faɗin,
"Kai dai ka sha haushi! Tun da ba za ka bari sai an ba ka ba!"
"Ƙyale shi je ku cire kayanku! Kai ma tashi sai ka cire uniform ɗinka sannan ka zo ka ci abincin!"
Yana turo baki ya miƙe yana hararar Umma Salma da ta janyo na hana shi cin abincin ba tare da ya cire kayansa ba.
Tare da su muka ci abincin babu laifi na ci da ɗan dama kafin na zare hannuna. Saboda jin da nake yi kamar zan yi amai muddin na ci gaba da cusa shi kamar yadda nake ta ƙoƙari.
Ko da Umma ta dawo gidan, gabaÉ—aya alamun jigata ya bayyana kan fuskarta. Amma a hakan ta ce da ni na tashi mu je a É—ebo kayan saboda na fi ta sanin kayana, gudun a haÉ—o da na Barira kuma hakan ya zamo wani sabon tashin hankali.
Inna Kulu ce ta ce da ita ta ci abincin tukunna idan ta yi sallah sai mu je. Ta ce ta yi wa mai motar kwatancen gidan wataƙila ma sai ya riga mu zuwa.
Dole ba don ta so ba ta zauna zaman cin abincin a gurguje ta yi sallah, saboda kiran da mai motar yake ta yi mata a waya yana faÉ—in ita yake jira. Zuciyata babu wata walwala muka fito gidan, bayan na bai wa su Ummu Salma umurnin su yi sallah da wanka kafin mu dawo.

Tun da muka doshi ƙofar gidan na ji ƙirjina yana dakan luguden uku-uku, saboda har raina ba na farinciki da kwashe kayan da muke ƙoƙarin yi. In da ta ni za a bi sai an jira idan ya sake ni sannan a kwashe kayan, duk da ba na zaton zan sake zama gidan amma kuma ba na so mu yi wahala a banza.
Kasancewar ina da makullin gidan a jikin na ɗakina, da na ƙofar falo tare da wadrobe ɗin da nake ajiyar wasu kayana a kitchen. Hakan ya sa ba mu sha wuyar shiga gidan ba duk da yake ƙargame, alamun masu gidan ba su ciki.
Da mamaki muka isa tsakiyar gidan, saboda ganin komai kaca-kaca tamkar an yi yaƙi. Ko'ina kwanoni da kofuna warwatse bayan tukunyoyin da aka jera kowace an yi girki da ita an ƙi wankewa.
Ganin murhu da itace ajiye tsakar a gidan, hakan ya sa na gano da shi Barira take girki. Falon muka kutsa kai babu shiri na zaro ido waje, saboda ganin an dawo da kujeruna inda aka ajiye na Barira. Sannan babu nata ko É—aya a falon sai nawa da aka maye gurbin nata da su.
Kasancewar mai motar tare yake da waÉ—anda za su taimaka masa, na ba su umurnin su fitar da kujerun waje su saka mota. Sannan na buÉ—e É—akina Inna Kulu tana faÉ—in,
"Ita wannan amarya halan ɗiyar wane hamshaƙi ce a garin nan?"

"Me kika gani?"

Tambayar da na yi mata kenan ina tura ƙofar ɗakina da na buɗe ina 'yar dariya.

"Na ga gidan kamar ba ta san miye shara ba balle wanke-wanke!"

Ɗakin muka shiga ina faɗin, "Matar so ai ba za a auro ta don wahala ba. Da dai a ce shi ɗin ba son jiki ne da shi ba, da sai ya dingà gyara mata komai su huta da ƙazanta."

"Ikon Allàh!"

Inna Kulu ta faɗa tana ƙoƙarin cire labulen ɗakin, na yi 'yar dariya sannan na ce,
"To wallahi in dai Mukhtar ne har tsutsotsi sai kayanta sun yi ba tare da ya ɗaga su daga inda suke ba, balle ya kawar da su a ji daɗi. Saboda duk lokacin da na je Kebbi, na sha dawowa garin nan na tarar da kwanonina ko wata kulata da tsutsotsi suna gwazarniya. Saboda ba ya iya ɗauke kwano a inda ya ci abinci, haka ma ba ya iya wankewa sai dai ya nemo wani ya ƙara ɓatawa. Gidan nan kuma tamkar an yi yaƙi a cikinsa don komai sai na gani, tsakanin kwalayen tabar da yake Sha, gwangwanin maltina da ledodin ruwan pure water. Wasu ma an sha rabi an ajiye, wasu kuma ajiya ta sa sun fashe da kansu, sai tarin takardu da mujallun da yake bita tamkar wani furofesa."

"Cabɗijam!" Inna Kulu ta faɗa tana riƙe da gemunta, fuskarta cike da mamakin maganganun da na faɗa. Umma tana fito da kayan wadrobe ɗita ta ce,
"Ai duk wanda ya zauna da Mukhtar dole ne a yi masa sannu, kamar yadda ake yi wa mara lafiya idan an je ganin sa. Don zama da shi babban ciwo ne mai zaman kansa, wanda babu maganinsa matuƙar ba rabuwa aka yi da shi ba!"
Ina dariya na ce, "Wallahi ko kashi ya yi ba ya flooshing Umma, haka zai cika masai abinsa ya wanke jikinsa ya fito. Tun ina zuba ruwa cikin mutunci ba na damuwa har na fara jin haushinsa ina masa ƙorafi. Amma wallahi bai daina ba, don sai ya gama wankansa ya fita idan na shiga toilet ɗin na taras da kashin zanƙare cikin kwalbar masan. Dole ba don na so ba nake zuba ruwa na wanke toilet ɗin ina gunguni. Allah bai raba ni da matsalarsa ba har sai da muka dawo gidan nan."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.