Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 82 of 86
"In Sha Allah zan kiyaye!"
Iya abin da na faɗa kenan, sannan na mayar da kaina ina ci gaba da latsar wayata. Takun wucewarsa na ji bayan ƙafafuwansa da na gani a duƙen da nake suna wucewa ta gabana.
Haka kawai na tsinci kaina da wata sabuwar damuwa, saboda yanayin muryarsa da na ji yayin maganar; ya fito mini da damuwar da yake ciki a kan laifin fashin zuwa na aiki. Inna ta fito tana sanar da ni ta kammala, godiya na yi mata sannan na shiga da guntuwar sallama a bakina.
Zaman da na yi a kan kujerata ya tuna mini da file's É—in da na tura a wadrobe na ajiye, waÉ—anda ban kammala aikinsu ba a ranar da Najib ya kira ni yana sanar da ni bai ga su Ummu Salma ba.
Abin mamaki ko da na buÉ—a wurin babu komai, sai jakata da na zo da ita a ranar na gani. Hakan ya sa na tuno lokacin da na fice ofishin da gudu cikin ruÉ—u waya a kunnena. Murmushi kawai na yi sannan a fili na furta,
"Allah ya raba mu da tashin hankali!"
Amina ce ta faɗo mini a rai, saboda tuno tun ranar ban koma jin ɗuriyarta ba ko a waya. Cikin sauri na fiddo wayata na nemo lambarta na danna mata kira. Sai dai har ta yi ringing ta ƙare ba a ɗauka ba, sai da na sake kira sannan aka ɗauka. Maimakon na ji muryar Amina sai na ji muryar wata babbar mace tana cewa,
"Waye?"
Bakina yana rawa na ce, "Amina nake nema, ni abokiyar aikinta ce kwana biyu ban ji motsinta ba, shi ya sa na kira na ji ko lafiya?"
"Lafiyarta ƙalau! Wayar tana hannuna ne! Kuma ta daina fita yawon gantalin da take zuwa da sunan aiki. Ki faɗa wa shugabanku ya cire sunanta cikin ma'aikatanku don ba za ta sake zuwa yawon tanɓelen ba!."
Tana ƙare faɗar hakan ta katse kiran, ko da na sake bin wayar da kira, da nufin na ba ta haƙuri na ji wayar a kashe.
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce,
"Ita kuma Amina tata ƙaddarar kenan baƙincikin Suruka! Shin yaushe mata za su huta da matsalolin gidajen aurensu ne? Daga wannan sai wannan!"
Hmmmmm! Mataye Allah ya ƙara mana haƙuri😢
D.AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA SHIDA.*
'Babu rana!' Ita ce amsar da zuciyata ta ba ni kai-tsaye ba tare da jinkiri ba. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na gyara zamana, tare da lulawa duniyar nazarin abubuwan da suka shuɗe a cikin rayuwata. Da waɗanda nake fuskanta a yanzu, bayan tunanin gobena da inda za ta nufa idan aurena da Mukhtar ya ƙare.
Ranar dai kamar MD ya yi fushi da ni, domin kuwa babu aikin da ya ba ni yadda na je haka na fito a lokacin da aka tashi. Zuciyata babu daÉ—i na fito ofishin ina tunanin na je na same shi ko kuma na share. Saboda ina so na ji laifin da na yi masa, bayan na fashin zuwa aikin da ya sanar da ni.
'Tafiyar ki kawai' shi ne umurnin da wata zuciyar ta ba ni, cike da jin kaina wata saboda ba na son Shan ƙamshin da yake yi mini. Bayan haɗe fuskar da yake yi idan ya gan ni tamkar wata dodanniya.
Adaidaitasahu na samu na nufi gida ban jira Najib ba, saboda zuciyata a cunkushe take da tunanin MD. A kan kalar halin da yake nuna mini, idan yana mini magana tamkar an yi masa dole ba ya so. Motar da na gani a ƙofar gidan Kawu Sale, ta sa na yi hanzarin isa bakin ƙofar ɗakinsa da ke wajen gidan. Saboda ganin baƙin takalmi da kuma muryar Baba Ali da na jiyo suna hira da Kawu Salen.
Har ƙasa na durƙusa bakina a washe na fara gayar da shi, ya amsa mini cike da kulawa na yi masa sannu da zuwa. sannan na gayar da Yaya Manu babban ɗansa da suka zo tare. Na miƙe ina ƙoƙarin juyawa na shiga cikin gidan, Kawu Sale ya yi saurin faɗin,
"Ke muke jira ki dawo mu je kotun fa! Saboda a yi komai a ƙare kowa hankalinsa ya kwanta a huta da an-yi-an-ce."
Dam-dam! Sautin bugun ƙirjina kenan ina dariyar yaƙe na ce, "Ai da an kira ni tun ɗazu Kawu, saboda yau ban yi aiki da yawa ba!"
"Alhaji Ali muka jira ya zo, saboda shi ma bai daÉ—e da shigowa garin nan ba."
"Allah Sarki!"
Ita ce kalmar da na iya faɗa sannan na yi cikin gidan, Kawu Sale yana faɗin na yi sauri mu fito ni da Umma, kada mu ɓata masa lokaci yau za su komwa Kebbin.
Na jinjina lamarin sosai a zuciyata, saboda tunanin yadda aka yi Baba Alin ya zo garin sanadin matsalar kawai. Domin rabon da ya zo gidan har na manta, duk abin da ake yi ana yi ne a waya. Ko ya kira mu ni da Umma da Kawu Sale, ko kuma mu mu kira shi idan ta kama.
Yarana suka zo da gudu suka faÉ—a jikina suna faÉ—in,
"Mama sannu da zuwa!"
Na rungume su kaÉ—an ina murmushi na yi É—akin Umma, bayan na yi wa Inna Kulu sannu da gida. Ganin Umma fes cikin shirinta na sabuwar atamfa gal, hakan ya sa na ajiye jakunkunan da ke hannuna ina faÉ—in,
"Wanga gayu Umma kamar mai zuwa biki?"
Harara ta wurgo mini tana cin abinci ta ce,
"Ki dai shirya ke kaÉ—ai ake jira!"
Na cire hijabina na fice da sauri, jikina kawai na wanke sannan na yi arwala na yi sallah a gurguje. A tsaitsaye na tsakuri abincin da Ummu Salma ta ajiye mini a lokacin da nake sallah, na sauya kaya da ɗan turare kaɗan na goga na fito. Saboda Umma har ta fice waje tare da yaran duka saboda da su za a je, kamar yadda Alƙalin ya ba da umurnin na zo da su tun farko.
Motar muka shiga dukanmu, Baba Ali gaban motar tare da Yaya Manu da ya tuƙo shi. Umma da Kawu da ni har yaran muka zauna bayan motar, Kawu Sale rungume da Haidar Ni na rungume Iman, Umma Salma zaune tsakaninmu ni da Umma.
Kasancewar babu tazara mai yawa a tsakanin Bafarawa Estate da High Cort ɗin. Mintuna kaɗan suka kai mu bakin gate ɗin kotun, Yaya Manu ya shigar da motar harabar kotun bayan an ba shi damar shiga. Wuri ya samu cikin inuwar Durumin da ta yi luf-luf ya yi parking. Muka fito dukanmu muka nufi cikin kotun, ƙirjina yana bugawa da sauri da sauri.
Ba mu jira iso ga kowa ba, muka nufi ofishin Alƙalin Baba Ali gaba muna bayansa. Cike da mamaki kafin mu shiga Alƙalin ya fito ya tarbe mu, sannan ya bai wa Baba Ali hannu suka gaisa cikin fuskar sanayya. Bayan ya gaisa da Kawu Sale mu ma muka gaishe shi ya amsa cikin kulawa.
Ɗakin sulhun muka nufa kai-tsaye tun kafin mu ƙarasa shiga na hango Mukhtar, tare da Yaya Maimuna da ƙannensa biyu maza har da Barira. Zuciyata cike da mamakin me ya kawo Barira a cikin case ɗinmu.
'Mijinta ta yi wa rakiya!'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.