Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 70 of 86

"Allah Sarki! Ki ce ita ma tana ciwo irin nawa? Kai! Allah ya yaye wa mutane wannan lalura."
Cikin sanyin murya ta yi magana, na amsa da "Amin" cikin sanyin jiki da na muryar duka. Saboda jikina ya ba ni ba ta san komai da ke faruwa ba, tun daga tsige kitson Barira har wannan badaƙalar auren da Amininta ya rikito. Haka kawai na ji tausayinta ya kama ni, saboda sanin duk ranar da ta ji wannan labarin; zuciyarta ma za ta iya bugawa ta mutu faraɗ ɗaya, balle tashin hankali ko damuwar da za ta shiga sai ta fi gaban kwatance.

Ganin damuwa a kan fuskata ya sa ta yi gaba tana faɗin, "Ke ai yanzu na samu lafiya sosai saɓanin baya da nake ɓacewa ba a san inda nake ba tsawon kwanaki. Ni ma ba na sanin ina nake sai dai na tsinci kaina a tsakiyar daji babu komai da kowa sai kukan tsuntsaye. Amma tun da muka bar gidan da muka fara zama farkon aurenmu, shi kenan matsalar ta kau sai dai lokaci bayan lokaci hargitsattssun kayan suna motsawa."

"To Allah Ubangiji ya yaye muku gabaɗaya, ya kawo sauƙi da salama a cikin lamarin da rayuwarku gabaɗaya."

"Amin Ya Allah! Ke ma ya sa ki dawo mana, don ba za mu yarda ki suɓuce ba!"

Ta ƙare maganar da yar dariya bayan ta juyo muna kallon juna, saɓanin tafiyar da take yi tana gaba ina bayanta har ƙofar gida. Taka mata na yi har muka je bakin titi, sai ga su Umma cikin adaidaitasahu har sun yi gaba na ga mai adaidaitar ya ja ya tsaya. Su Umma suka fito Inna Kulu tana cewa da ni,

"Ta zo ya kai ta mu sai mu ƙarasa kawai!"

Tare muka nufi wurin tana faÉ—in, "Sai wani murna kike yi kin zo gida kina 'yanmatanci. Ni na manta ma ban ga su Ummu Salma a gidan ba, ina suka je?"

"Suna gidan ƙanwata ɗiyar Kawuna."

"Allah Sarki ki gaishe mini da su, yawwa ma har na tuna.."

Ta fito da wata leda a jakarta ta miƙa mini tana faɗin, "Ki ba su don Allah! Kwanan nan gabaɗaya a hargitse nake ji na wallahi."
Karɓa na yi su Umma suka taya ni godiya ta shige tana cewa Umma, "Zan miki tafiyarki ke kaɗai Umma. Amma don Allah a sassauta kada abin ya yi tsauri ta dawo mana haka nan, don har mun fara kewar ta."

Murmushi Umma ta yi tana faÉ—in,
"Allah ya zaɓa abin da ya fi alheri."
Daga haka suka tafi muna É—aga mata hannu har suka yi mana nisa, sannan muka juya tare da su muna hira.

"Gaskiyar magana mijin yarinyar can bai yi mata adalci ba! Don alamunta ya nuna ba ta san komai ba. Saboda yadda ta nuna alhininta a fili a lokacin da ta zo, dangane da yadda ta ga Sajida ta ruɗe sosai tana zunduma ihu. Haƙuri ta dinga ba ta bayan ta gama tambayar mu me aka yi mata. Har muka bar ƙofar gidan tana ta jera mata sannu da Allah ya ba ta lafiya."

Zancen Inna Kulu kenan a lokacin da muke ƙoƙarin shigewa gida,
"Ai duk mutumin da kika gani tare da Mukhtar, ba mutumin arziƙi ba ne. Shi ya sa idonsa ba su yi mini girma ba, balle na fasa sauke musu duk abin da ya fito bakina. Ai dai duniya ce, su yi duk abin da suke so Allah yana jiran su a madakata, domin su karɓi sakamakon abin da duk suka shuka."

Ummu ta ƙare maganar tare da cire hijabinta ta ja buta zuwa bayi. Na ja kujera 'yar tsugunno na zauna, sannan na sauke ajiyar zuciya na ce,
"Ni na rasa da me zan fassara wannan lamari. Duk da idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Maman Taufiƙ tana da zafin kishi sosai har na fitar hankali. Shi kuma mijinta yana da idon kallon mata ya ji sun burge shi. Idan ya yi laifi a kan ɓoye matan da ya yi, to laifinsa kaɗan ne nata ya fi yawa. Saboda ya fi kowa sanin zafin kishinta, yana gudun ya faɗa mata hakan ya janyo masa tashin hankali. Amma kuma da ya faɗa mata gaskiya sai ta fi jin sauƙin abin, da a ce ta ji labari kwatsam! Bayan aikin gama ya gama."

"Maza! Maza!"

Zancen Inna Kulu kenan tare da jinjina kai, kafin maganar Kawu Sale ta shigo dodon kunnuwanmu tun kafin mu gan shi.

"Me mazan suka yi?"

Murmushi na yi mai sauti ban ce komai ba, Inna Kulu ce ta yi ƙarfin halin faɗin,
"Tsohuwar bazawararka aka ce yaushe za ta kawo sadaki a É—aura muku aure?"
"Ki rantse da Allah gaske kike yin maganar nan, ni kuma cikin satin nan a É—aura na dinga zuwa gidanta dangana sanda."
"Idan da rabon sandar ta jingine ka gidan da ƙarar kwana ai sai ka je ga fili ga mai doki."

Zancen Inna Kulu kenan da Kawu Sale, tsam na miƙe ina dariya na yi ɗakin Umma. Kwance na yi, bayan na mayar da ruwa da kunun ayar da Maman Taufiƙ ta ƙi sha a furji. Ina ta juya abubuwan da suka faru a kwanyata bi-da-bi, har tunanin Sajida ya faɗo mini a rai zumbur na miƙe na fito waje. Inna Kulu na iske ɗakinta ina faɗin,

"Wai Inna ya aka yi da kuka kai Sajida gidansu?"

Inna Kulu fuskata babu yabo babu fallasa ta ce da ni,
"Lafiya lau na fito gidan, duk da Uwarta ta yi ta jifa ta da maganganu marasa daÉ—i. Bayan na ce ga 'yarta nan mun kawo mata kada ta tsine mata. Tun kafin na gama fitowa na ji tana faÉ—in, yau gidan mijinta za ta kwana ta gama kwana gidan har abada."

"Allah Sarki Sajida!"

Haka kawai na tsinci hawaye suna kwaranya a kan fuskata, saboda duk abin da aka yi mata sanadina ne. Domin a huce haushi na da ake ji a kanta, saboda ta nuna tana ƙaunata a fili fiye da kawunta.

"Akwai Allah! Kuma in Sha Allah sai abin ya zame mata alheri."

Zancen Umma kenan, wadda ke riƙe da labulen ƙofar ɗakin Inna Kulu. Kafin ta ɗora da faɗin, "Ke kuma Kulu idan ba ki daina zancen Bazawarar Sale ba, sai 'yan Amin su amsa ya tare can tun da ba za ki bar shi ya huta da magana ɗaya ba."

"Ai da yana iyawa da ya yi tun lokacin da take rawar ƙafa kansa. Idan kuma kun isa a yi auren cikin satin nan kamar yadda ya ce."
"To ba mu so, kuma Allah ya raba mu. Ke ma da kike zancen saboda kishi Allah ya ba ki ikon dainawa. Mace saboda jin daÉ—in aure da tsufanki ma sai kin yi kishin Salenmu! Amma duk kika motsa sai kin cika baki kamar gaske."

"Kyale ta Habi! So take yi na ɓanɓaro sabuwar budurwa ɗanya shataf!"

Zancen Kawu Sale ya sa na yi murmushi ban shirya ba, haka suka dinga wasar su kamar yadda suka saba na baro É—akin. Zuciyata cike da tunanin. 'Kenan dai mace komai tsufanta idan ta ji daÉ—in aure tana kishin mijinta. Balle masu rangwamen shekaru waÉ—anda suke tsaka da cin ganiyar lokacinsu.'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.