Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 57 of 86
Ɗakinta ta nufa karaf ta dantse ƙofar, ya fara aiko mini da harara yana nuna ni da hannu yana cewa,
"Ko shaiÉ—an sai ya shafa miki lafiya a wurin ibilisanci. Don haka ki je kawai akwai Allah!"
Dariya na fashe da ita sannan na yi masa gwalo, ƙwafa kawai ya yi sannan ya tsaya bakin ƙofarta yana faɗin,
"Ki yarda da ni Barcy! Wallahi ba haka muka yi da ita ba."
****
Tun da na shige ɗaki ban sake fitowa ba, sai da su Ummu Salma suka dawo na ce su je su yi wanke-wanke. Bayan na yi wanka na haye gado ina ta faman chatting da na gaji na koma kallo har bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da ni.
Ƙarfe uku lis na fito ɗakin, saboda hayaniyar faɗan da yaran suke yi. Kokawa sosai suke suna dambacewa tsakanin Haidar da Iman, Ummu Salma tana raba su Haidar bai bari. Ganin Barira a kan kujerarta zaune tana latsar waya ko a jikinta; hakan ya sa na ji raina ya ɓace.
Fakar Haidar na yi cikin fushi na fara yi masa faÉ—a sannan na dawo kan Iman. Ummu Salma ce ta fara yi mini bayanin abin da ya haÉ—a su faÉ—an.
"Wai don ba a ba mu abinci muka ci ba, shi ne ya ce dole sai ya je ya É—auko. Kuma amarya ba ta ce mu É—auko ba, ta ce mu jira har Abbanmu ya dawo shi ya ce zai ba mu."
"Ban gane ba! An gama abincin shi ne ba za a ba ku ba sai ya dawo ya ba ku?"
Ummu Salma ta É—aga kai alamun tabbatarwa,
"To ai shi ne zan je na ɗauko mana mu ci Iman tana riƙe ni. Ni Ko da na gaji haushi na dinga kai mata duka, daga nan muka fara kokawa."
Kitchen kawai na nufa ba tare da na ce da su komai ba balle Barirar, kulolin da na gani ajiye na fara buÉ—ewa. Shinkafa da miya na gani a cikin kuloli biyu, ban tsaya neman bayani a kansu ba na É—auki wadda ta fi girma na fice.
Ina tsaka da zuba musu abincin na ji muryar ta a saman kaina tana faÉ—in,
"Kan ubancan! Abincin Romiyo kike zuba musu?"
Ban fasa juye musu abincin a tire ba, na bi abincin da miya tare da zuƙa-zuƙan namun da na gani duk na juye musu. Ina ƙoƙarin tura musu gabansu ta fara faɗin,
"Gaskiya Aunty wallahi ba ki kyauta mini ba! Saboda Allah yaushe zan yi wa mijina girki ki zube wa yara su cinye?"
"Abincin daga gidanku kika zo da shi ne? Ina ga ai har yanzu ba a kawo miki kayan garar da ake kai wa kowace amarya ba. Ki jira idan aka kawo ki yi iko da abin ki, amma wannan ba ki da halin hana wa yara abincinsu. Domin ubansu ya sayi shinkafar kuma shi ya yi cefanen da aka yi gurkin."
"Haka ma za ki ce?"
"E, haka na ce!"
Kuka ta fashe da shi wiwi tamkar wadda aka daka, saboda sallamar da Mukhtar ya yi tun kafin ya shigo falon. Wurinsa ta yi da gudu ta faÉ—a jikinsa tana rera sani sabon kukan, a ruÉ—e ya fara tambayar,
"Lafiya? Me aka yi mata?"
Kallo ma bai ishe ni ba, na zauna ina faÉ—in su yi sauri su gama su tafi. Isowa ya yi wurinmu tare da ita a jikinsa yana faÉ—in,
"Wai me yake faruwa ne!?"
Mere na yi musu daga shi har ita, sannan na ci gaba da bai wa su Ummu Salma umurnin su yi sauri su gama su tafi.
"Wai fa abincinka ne ta É—auko ta zube wa yaran, bayan kuma sun ci abincin tun lokacin da na gama girkin."
Kallo na kawai ya dinga yi fuskarsa a haÉ—e sannan ya ce,
"Wai ke don Allah har abada ba za ki bari a zauna lafiya ba? Yanzu wannan abin da kika yi miye ribar shi?"
"Daga kai har ita ban da lokacinku! Don haka idan ta gama shirya maka zance ka haye, to ka zuba mini fetur ka ƙone mu duka mu kama da wuta daga ni har yaran."
Wata zabura ya yi tare ƙoƙarin kai mini duka, ta yi hanzarin riƙe shi tana faɗin,
"Don Allah Romiyo ka ƙyale ta a bar ta da halinta. Idan ma sun ci ai 'ya'yanka ne ba na kowa ba. Mu je na ba ka wanda ta bar mana ai gobe ma rana ce!"
"Da ba ki hana shi ba! Tun da ba ki ji kunyar yin ƙaryar da za ki haɗa ni da shi ba. Na rantse da Allah duk ranar da ka yi gangancin taɓa jikina da sunan duka sai na illata ka. Ke kuma baƙar Munafuka annamimiya sai kin gwammace ba ki san shi ba a faɗin duniya, don sai kin yi kukan da ko uwarki ta mutu iyaka kenan. A dai juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe."
Ba su ce da ni komai ba, ta ja shi suka shige kitchen na ce da su Ummu su tashi su je tun da sun ƙare.
Na zauna ina ta huci tare da girgizar ƙafafuwa, saboda na zo wuya komai zan iya aikatawa a lokacin. Su Ummu Salma suka fice gidan tamkar ƙwai ya fashe musu a ciki, su kuma tsuntsayen soyayya suka fito aka baje tsakiyar kujerunta. Shwagaɓa ta dingà yi masa tana ba shi abinci a baki suna hira ƙasa-ƙasa, idan abin ya yi musu daɗi su fashe da dariya.
Komawa É—aki na yi na É—auko wayata na kwanta, na fara waya tamkar gaske cikin kashe murya ina faÉ—in,
"Haba dai ai kai ma ka san bayan kai babu wani a faÉ—in duniya. Daina zancen wannan lusarin, wanda bai ajiye komai ba face masifa da hargowa tamkar zai cinye mutum da ransa."
Shiru na yi kamar yadda su ma suka yi tsit tamkar ba su cikin falon, dariya na yi mai sauti sannan na ce,
"Cabɗijam! Ai ka yi shiru kawai abin ba a cewa komai. Fankam-fankam ai ba ya kilishi, ita ma kwana biyu za a jone mu bi sahu. Ai na rantse da Allah da ta san kowane ne ba za ta yi gangancin raɓarsa ba. Saboda muddin ya ƙyalla ido ya hango wata ƙawarta sai ta sha mamakin abin da zai aikata mata. Yo nawa aka yi wai an yi wa ɓarawo kashedin sata?"
Wayar na ji an fisge ba tare da na ji lokacin da aka zo a kusa da ni ba. Da sauri na miƙe fuskata a haɗe na ce da shi,
"Ban wayata!"
"Sai kin faÉ—a mini da uban wa kike waya? Kuma wane É—an iska ne ya kira ki?"
Raina fes ba tare da shayin komai ba na ce da shi,
"Da uban da ke so na yana dakon aure na! Sannan da É—an iskan da ka ajiye mini ina lalata da shi a waje."
Kallona ya dinga yi bakinsa yana rawa, na yi 'yar dariya sannan na ce,
To ba ni wayar tun da na amsa tambayar ranka shi daÉ—e! Romiyo mijin Barcy!"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.