Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 77 of 86

Mintuna a tsakani muna maƙale ni da Umma, 'yan sandan suka dawo suna murmushi suka ce da matar ta fice ta bar mu. Ta fice tana aika mana harara tare da yin ƙwafa, Umma ta ja ni ta zaunar da ni a kan kujera ita ma ta zauna. A bisa umurnin da babban jami'in ya ba mu daga ni har ita.
Sannan ya yi gyaran murya ya ce, "To maganar gaskiya, mun fahimci wannan lamari ƙarya ce kawai babu gaskiya a ciki. Don haka mun kori wannan case ɗin ku je ku sasanta kanku a gida. Amma kafin ku je, ya dace mu yi muku iyaka da juna, a matsayinmu na jami'ai. Daga yau kada wanda ya sake tayar da wannan magana, saboda mun kashe ta daga yanzu kuma mun binne ta a nan. Tun da daman can kun kai matsalar kotun ƙoli kuma ba a gama zartar da hukunci ba. To mu babu abin da za mu yi muku a nan, ku tashi ku je kuma ku tabbatar da an kashe wannan rigima daga nan."

Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata, cike da tunanin abin da ya sauya musu ra'ayi lokaci ɗaya kuma nan take. Wani ƙanen Mukhtar cikin zafin rai ya ce,
"Ranka ya daɗe haƙƙin ɗan'uwanmu muke so a ƙwato mana fa! Saboda ta ji masa a mazakutarsa yanzu haka yana ƙarƙashin kulawar likitoci."

"Mu dai mun kori case ɗin daga hannunmu, amma idan kun ga za ku iya kai wa wani wuri ƙofa a buɗe take."
Zancen babban jami'in kenan, sannan ya miƙe ya fice. Yaya Maimuna cikin ƙololuwar ɓacin rai ta ce,
" Rashin adalci dai ake ƙoƙarin yi mana, to wallahi Mukhtar ya gama zama da ke daga yau ɗin nan. Hamza miƙo mini takardar sakinta da ya ba mu sallahun a ba ta." Ta miƙa hannunta ga wani ƙanen Mukhtar, wanda tun da aka zo wurin bai ce komai. Takarda ya ciro daga aljihunsa ya miƙa mata, ta fisga cikin fushi ta wurgo mini tana faɗin,
"Ga shi nan! Daga yau Allah ya raba mu da masifa da bala'i!"

Cikin sauri Kawu Sale ya duƙa ya ɗauki takardar ya saka aljihu ba tare da ya duba ba. Umma ta miƙe tana faɗin,
"Masifa da bala'i kam yanzu kuka fara cin karo da ita! Kuma ku jira ku gani idan haƙƙi zai bar ku ku shaƙi iska mai kyau!"
Tana ƙare faɗar hakan ta ja hannuna muka fice, 'yar sandar muka ci karo da ita za ta shiga ɗakin. Umma ta nuna mata wuyanta da hannu alamun sai ta yanka ta, murmushi kawai 'yar sandar ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Kawu Sale ya biyo mu muka fito harabar wurin. MD na hango da babban jami'in suna ta hira har da dariya, sosai mamaki ya kama ni. Saboda walwalar da na hango kwance a kan fuskokinsu, kuma alamunsu ya nuna akwai kyakkyawar sanayya a tsakaninsu.
Ban bi ta kan shi ba daga ni har Umma, Kawu Sale ne kawai ya nufi inda suke, ina ji kafin mu yi nisa da su yana faÉ—a wa babban jami'in takardar sakin da aka ba ni.
Ban san ya suka yi ba, muka nufi hanyar gida a ƙasa ni da Umma jugum-jugum babu mai magana. Har mun yi nisa MD ya biyo mu tare da Kawu Sale a cikin motarsa.
Tsayawa ya yi daf da mu ya yi parking ya fito. Har ƙasa ya duƙa ya gayar da Umma kansa a duƙe. Umma ta amsa tana haɗe fuska ni ma na gayar da shi fuskata babu yabo babu fallasa, saboda har lokacin akwai busasshen hawaye a kan fuskar tawa.

"Mama ku zo na sauke ku gida!" Umma ta ce,
"Tafiyarka kawai mun kusa ƙarasawa kada mu wahalar da kai."

"Don Allah Habi ki shigo mu tafi! Saboda akwai maganar da za mu yi da shi idan mun je gida!"

Hannun Umma na ja muka shiga motar muka zauna, "Ai Habi wannan yaro; babu abin da za mu ce da shi sai godiya! Saboda shi ne ya kashe wannan gobara da ta turnuƙe. Ba don shi ba da yanzu ba mu san inda matsalar za ta tsaya ba, don haka mu gode wa Allah mu gode masa. Saboda waɗannan mutane da gaske suke yi sai sun nuna wa yarinyar nan iyakarta. Amma da yake ta Allah ba tasu ba, ga shi komai ya dakata ba tare da sun ci galaba a kanmu ba!"

Daga ni har Umma tsit muka yi ba tare da mun ce komai ba, Kawu Sale kawai yake ta zuba shi kaɗai har muka kai ƙofar gidansa.
Bayan mun fiffito ne Kawu ya fara yi wa MD godiya Umma ma ta yi masa godiyar ta shige gida. Kawu ya ƙaraso inda nake yana faɗin,

"Ki gode wa Allah ki gode masa. Don shi ne ya yayyafa wa wutar ruwan sanyi ta kwanta, kuma babban jami'in ya tabbatar mini da duk inda suka kai ƙara a cikin garin nan; sai sun sa a kore su."
Hawaye mai sanyi na ji ya zubo mini a kan fuska, da sauri na goge sannan na kalli MD na ce,

"Na gode maka sosai! Ubangiji ya jiƙan magabata!"

Ina gama faÉ—ar hakan na yi cikin gida na bar shi a nan tare da Kawu Sale. Muryar Umma na tsinkayo a lokacin da na kutsa kaina gidan tana cewa,
"Ni fa Kulu wallahi ba na son mutumin can yana manne wa Zaituna. Haka fa shekaranjiya ko da muka fita mun gan shi a ƙofar gidan nan. Haushi ya sa ban bi ta kansa ba a lokacin da yake roƙon mu zo ya kai mu inda za mu je."

Kaina a tsaye na isa inda suke tsaitsaye suna maganar na ce,
"Shi ya cece ni a lokacin da mota ta tashi kaɗe ni bayan na fito ma'aikatarmu a ruɗe. Hakan ya sa ya kawo ni gida, kuma shi ne dalilin da ya sa kika gan shi kenan bayan mun fita, saboda wayata da ke hannunsa yana son ba ni. Don jiya bayan mun dawo daga kotu, Inna Kulu ta ba ni wayar da ya kawo a ajiye mini. Yanzu ma ni ce na tura masa saƙo a lokacin da 'yan sandan suka zo tafiya da ni. Kuma kin ji abin da Kawu ya ce ba don shi ba da ba mu san inda matsalar za ta tsaya ba!"

Shiru kawai Umma ta yi ba ta ce komai ba, illa butar da ta É—auka ta shige bayi. Inna Kulu ce kawai ta fara jinjina abin tana faÉ—in Allah ya saka masa da alheri. Kawu Sale ya shigo gidan yana yabon kirkin MD tare da nuna jin daÉ—insa a fili, dangane da halin girman da ya nuna mana.
Takardar sakin ya ciro daga aljihunsa ya miƙo mini yana faɗin,
"Allah ya raba ki da alaƙaƙai. Ubangiji ya kawo miki kyakkyawan sauyi a nan gaba."

Hannu biyu na saka na karɓi takardar zuciyata fes! Sai dai ganin rubutun ya sa annurin fuskata ɗaukewa. Domin a kallon farko na gane ba rubutun Mukhtar ba ne a jikin takardar, kenan dai har yanzu tana ƙasa tana dabo tsugunne ba ta ƙare ba.
"Yawwa! Bari na je yanzu na nemo mana motar da za ta kwaso miki kayanki." Zancen Umma kenan da ya sa na É—auke kallona daga saman rubutun sakin da su Yaya Maimuna suka yi mini. Domin ganin rubutun ya sa na yi tantamar bai san wainar da suke toyawa ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.