Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 33 of 86

"Oh! Kenan dai ni kaÉ—ai suke ganin ina sha shi ya sa ya koya?"

"Kai ne dai kusa da shi, don haka ka taimaki yaran nan ka daina sha a gidan nan ko da ba za ka fasa sha duka ba. Sannan ka yi ƙoƙarin nisanta tabar a inda ka san za su gan ta su ɗauka. Saboda tarbiyya daga gida take farawa, kuma Iyaye su ne makaranta ta farko da suke bai wa 'ya'yansu karatun da zai fi shiga kansu."
"Za a yi yadda kika ce!"
Yana ƙare faɗar hakan ya miƙe ya fice da sauri saboda kiran da ake yi masa a waya, tun a lokacin da muka fara magana yana ƙin ɗauka. Ya bar ni zaune ina bin ƙofar da kallo, tare da sauraron maganar da ya yi a wayar kafin ya fita gidan.

"Ga ni nan zuwa yanzu ki jira ni."

Tagumi na yi ina goge hawayen da ban san lokacin da suka gangaro kan fuskata ba.
'Habi ba ta san matsalar zama da irin wannan mijin naki ba, saboda labari ya zo mini har gida a kan riƙaƙƙen ɗan iska ne kuma ɗan shaye-shaye. Duk zaman da za ki yi da shi ba za ki taɓa samun farinciki ba sai kayan takaici da za ki yi ta kwasa kina jibga wa kanki. Amma tun da ta kafe a kan ba ta yarda a sake ki ba, to ki je ki ci gaba da zaman na zare hannuna a cikin sakin da nake nemar miki wurin shi. Don haka zancen zuwa kotun ma na ajiye ki je ki ci gaba da zaman haƙurin har Allah ya kawo miki ƙarshen shi.'

Maganar Baba Ali ce ta faɗo mini a rai, ranar da muka yi wani zama a lokacin da rikicinmu da Mukhtar ya yi tsananin da Baba Ali ya ce; na baro gidan Mukhtar na dawo Kebbi shi zai karɓar mini takardata a hannun shi, ko ta arziƙi ko ta tsiya idan ya ƙi bi ta lalama. Saboda ƙazafin da ya jefe ni da shi tun kafin na san MD kuma tun kafin na fara aiki a ma'aikatarsu.
Daren ranar ma na yi shi ne da ƙunci tare da kai wa Allah kukana a kan ya kawo mini sauyi da mafita ta alheri.
Da safiyar ranar Talatar, mai adaidaitan har gida ya É—auke mu kamar yadda muka yi ajanda.
Fuskata a sake na shiga ma'aikatar saboda tuno abin da MD ya yi wa Sara, ban damu da kallon da mutane suke yi mini ba saboda na yi amanna da cewa, fiye da rabinsu ba za su yarda da ƙazafin da Sara ta jefo mini ba. Duba da yadda ban da sakewa da kowa daga matan har mazan, idan aka cire Amina da gaisuwar mutuncin da nake yi da kowa.

Aikina na yi cikin natsuwa har ana gaf da tashi, sannan Amina ta shigo fuskarta É—auke da murmushi ta zauna. Kallo na bi ta da shi ina 'yar dariya saboda tuno damben da muka sha ni da Fatima matar MD.
"Hajiyata! Me ya sa a cikin labaran da za ki ba ni ba ki sanar da ni kin iya faÉ—a da dambe ba?"
Baki na rufe ina ƙumshe dariya saboda ba ƙaramar dariya maganar ta ba ni ba. "Ai faɗa zuwa yake yi, kamar yadda dambe yake afkuwa bagatatan ba tare da an shirya masa ba. Wataƙila hakan ce ta hana ni sako su a labarin, sai da suka zo da kansu kika gani domin ki tabbatar da komai zuwa yake yi a lokacin da aka rubuta. Yanzu dai na ga fuskar ki da yalwa, me ke faruwa ne? Ba ni na sha tun kafin ta sarare a iska."
"Hmmmmm!" Ajiyar zuciyar da ta sauke kenan sannan ta ce, "Yau dai Mama ta amsa gaisuwata. Saboda 'yarta ta zo jiya kuma a gabanta na koma gidan, ko É—akina ban shiga ba sai da na je wurin Mama domin ta san dawowata. Saboda wani lokaci faÉ—a masa take yi ta ce ban dawo gidan ba sai gaf da magriba. Dalilin hakan na tsiro zuwa wurinta idan na dawo domin ta san lokacin da na dawo ta daina haÉ—a ni da shi."

"Ma sha Allah! In Sha Allah da sannu za ki ga komai ya zama tarihi. Saboda ko Bature ya ce; No condition is permanent. Babu abin da yake tabbace idan ba ƙudura da irada ta Ubangiji ba. Wanda yake kum-fa-kun ne da ya ce a yi komai zai tabbata babu jinkiri."
"Na yarda da zancenki, kuma in Sha Allah zan ci gaba da haƙuri. Fatana kawai ta gane da wuri saboda ta daina ɗaukar zunubin da take loda wa kanta." Zancen da ta yi kenan bayan ta sauke ajiyar zuciya. Sannan ta ce,
"Yanzu nake ji, wai jiya Basiru ya ɗebo wa MD 'yansanda a kan ya mari matar shi. Shi kuma MD an ce ya maka Sara kotu, a kan ƙazafin da ta yi muku."

"Subhanallah! Abin duka bai yi daÉ—i ba. Gaskiya da bai biye shirmen su ba. Saboda suna yi ne duka don haushin korar da ya yi wa Basirun. Da ya bar su don ko ba komai shi sama yake da su, kuma ya fi su mutunci a idon mutane, bai dace ya biye su girmansa ya zube a banza ba saboda hakan."
"Ni ko sai na ga ya kyauta, saboda sun yi ne kawai don su ci zarafin shi. Amma nuna musu da ya yi ya fi su hauka, hakan zai rage wa iskancinsu kaifi. Don na tabbatar da ba su da kuɗin ɗaukar lauyan da zai ƙaryata abin da Sara ta faɗa a idon mutane."
Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce, "Ba za ki gane ba Amina. Wani abin fa kana da ikon ɗaukar mataki kake haƙura, saboda illar da abin zai haifar maka ya fi amfanin shi ya yawa. Domin fallasuwar wannan abin zai taɓa ƙimar MD sosai wallahi, kuma ba zai gano hakan ba har sai an gama shari'ar tsegumi zai fara tashi a tsakanin mutanensa da bai yi tsammani ba. Amma idan ya haƙura ya ƙyale shi kenan komai zai wuce waɗanda suka sani ma za su manta. Saɓanin fallasar da za ta janyo labarin ya fantsama ta yadda goge tarihin zai yi wahala a zukatan mutane."

"Lalle kin fi ni gaskiya Maman Haidar. Don haka ya dace ki yi wannan gudunmawar domin ki datakar da shi ko za a dace ya haƙura ya janye."
Shiru na yi ina nazarin maganar, saboda duk abin da zai haÉ—a ni magana da shi personally ba na so, amma idan aiki ya haÉ—a ko É—ar ba zan ji ba saboda babu yadda zan yi.
"Ba na son duk wani abu da zai haÉ—a ni da shi Amina."
"To ki tura masa saƙo!"
Shiru na yi na ɗan lokaci, sannan na janyo wayata ba don ina so ba na tura masa saƙo kamar haka;

'Ka yi haƙuri ka janye ƙarar da na ji ka saka. Saboda babu alfanu idan sirrin ya fallasu a idon waɗanda ba su san da shi ba. Maimakon kankare laifin, sai ka ƙara ɓanɓaro mana yamaɗiɗin mutane, garin neman gira za a rasa ido. Ba na jin kaina, amma ina jin takaicin ƙimarka ta taɓu ta sanadina.'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.