Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 63 of 86
"Daman kin dawo Aunty?"
"E!"
"Yaushe kika shigo ban sani ba?"
"Tun lokacin da kuka fara ihu ke da ƙawarki."
Na ba ta amsa ina ci gaba da cin abincina alamun ko a jikina. Barira ta fara rawar murya tana faÉ—in,
"Aljanun..ta ne..suka ta..shi..shi ne fa..na yi mata addu'a..da ƙyar suka kwanta."
"Allah Sarki! Gara da suka kwanta da wuri, don har na kira Mukhtar na faɗa masa; ya yi gaggawar zuwa Barcynsa da ƙawarta suna ɗaki suna ta sambatu. Domin ya ji daɗin cin uban aljanun da kyau har sai sun daina ihun daɗi"
"Wallahi Aunty da gaske nake yi ko gidansu an san suna tashi lokaci bayan lokaci." Abin da Barira ta faɗa kenan tare da isowa inda nake jikinta yana ɓari.
"Daman ai ban ce kina ƙarya ba."
"Zo Aunty Suby ki yi mata bayani ko za ta gane" Ta ƙare maganar tana zarar ido alamun rashin gaskiya ɓaro-ɓaro a kan fuskarta.
Murmushi na yi mai sauti, sannan na ajiye plate ɗin na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya a kan teburin na ce,
"Kun fi ni tashanci, ni kuma na fi ku wayo saboda dukanku na girme ku. Don haka na ji duk abin da kuke faɗa a cikin sambatunku. Kuma na san me kuka aikata, saboda haka zaɓi ɗaya na ba ki. Ko ki daina wannan shashancin daga yau. Ko na faɗa wa Mukhtar gaskiya ya ɗauki mummunan mataki a kanku daga ke har ita."
"Wallahi Aunty na daina, daman can magani ne muka sha muka yi bacci. Ba mu san duk abin da ya faru ba har sai da muka farka."
"Wane irin magani ne haka?"
"Ke kam Barira kin sha haushi! Ita kishiyar kike yi wa wannan rawar muryar? To ki zauna tana yi miki titsiye tun da uwarki ce! Mitsssss! Aikin banza kawai, ni kin ga tafiya kya ji da kayan takaicin ki ke kaÉ—ai."
Zancen ƙawar Barira kenan wadda na ji ta kira da sunan Suby. Na yi hanzarin miƙewa na biyo ta, gani na ya sa ta ja ta tsaya tana hurar hanci ta ce,
"Wallahi daidai nake da ke, don ba tsoron ki nake ji ba"
Gidan na rufe da kwaÉ—o ta ciki, sannan na koma É—akina na É—auko waya na kira Mukhtar. Kira É—aya biyu ya É—aga yana faÉ—in,
'Lafiya?'
"Ba lafiya ba! Ka zo gida yanzun nan ga wata ƙatuwa nan ta zo har gida tana lalata da Barira."
'Ban gane ba!'
"Ka zo gidan za ka gane"
Ina ƙare faɗar hakan na nuna ta da hannu na ce, sai kin san ƙaryar bariki kike yi yau. Don sai kin raina kanki tun da ke kwartanci ba komai ba ne a wurinki.
"Idan ya zo ki ce ya kashe ni!"
"Ba zai kashe ki ba, amma za ki raina kanki."
"Don Allah Aunty kada ki biye ta, wallahi ba na so Romiyo ya ji maganar nan. In Sha Allah daga yau ko gidan nan ba za ta sake zuwa ba."
"Ke kam kina da abin takaici Barira! Har yaushe za ki dinga kwantar da kai ga kishiya irin haka tamkar za ki yi mata sujada. Abin da take tunanin an yi kuma shi aka aikata, idan akwai wani abu da za ta yi kafin soloɓiyon mijin ya zo ta fara yi kafin shi. Ni wallahi da na auri irin wannan ragon mazan ƙara na lalace a kan titi."
Dariya ta so ba ni, amma kuma na mazge na ce,
"Oh ita Barirar ce ta faɗa miki soloɓiyo ne?"
"Ko ma dai mene ne hakan yake."
Bubbugar ƙofar da ake yi ya sa na je na buɗe kwaɗon na ja gefe, saboda ganin Yaya Maimuna fuskarta a haɗe. Tana ƙoƙarin yin magana Barira ta iso wurinta da gudu tana kuka tare da kai mata ƙara ta.
"Kin ga Aunty nan ta saka Aunty Suby gaba tana ƙoƙarin manna mata sharri. Don Allah ki ce ta bar ta ta tafi tun da ba gaskiya ba ne abin da take zargi."
"Yi shiru! FaÉ—a mini me ya faru?"
Zancen Yaya Maimuna kenan tana ƙoƙarin rarrashin Barira, ta hanyar bubbuga bayanta tana share mata hawaye.
Suby ta fara magana tana cewa,
"Wai daga ta dawo ta gan ni cikin gidan, shi kenan take neman haÉ—a ni da sharri. To wallahi ni daidai nake da zamaninta don na ci dubu sai ce..."
Marin da na kai mata a haukace ya sa ta haɗiye sauran maganar da ke bakinta. Ban jira komai ba, na yi cikinta da duka cikin sa'a na jefar da ita ƙasa na haye. Yaya Maimuna da Barira suna ƙoƙarin ture ni kanta na yi wata zabura na watsar da su ƙasa warwas suka faɗi.
Sannan na ci gaba da kai wa Suby naushi a baki su ma suka rufe ni da duka. Hargowar Mukhtar ta sa dukanmu muka shiga hankalin kanmu. Gefen bakin Suby ya kumbure tamkar zunɓutun kaza, amma a hakan ta dinga aika mini zagi ta uwa ta uba.
Mukhtar ya dakatar da ita, sannan ya tambayi dalilin faɗan. Na yi masa bayanin komai Barira ta fashe da kuka tana faɗin ƙarya nake yi mata. Suby ma ta tuɓure a kan sharri ne na yi musu ba gaskiya ba ne.
Yaya Maimuna ta dinga jifa ta da miyagun maganganun da suke nuni; da fatar abin da nake yi wa Barira ƙazafi da shi ya hau kaina ko 'ya'yana.
Raina a ɓace na ce, "Bakinki ya sari ƙaton dutse, don har abada ni ko yarana ba za mu yi irin wannan halin tumakai ba."
Mukhtar ya taso mini da masifa kamar ya dake ni, wai na yi wa Barira da Subyn ƙazafi kuma idan na sake duk abin da na janyo wa kaina babu ruwan shi. Haushi ya sa na dinga mayar masa da raddi bakina yana kumfa tamkar na kai masa duka.
Sanin halina ya sa bai taɓa ni ba, ya dawo kan Suby yana ba ta haƙuri tare da lallaɓa ta har ta fice gidan. Yaya Maimuna kuma ta dawo da faɗan sabo don daman can shi ya kawo ta.
"Daman wurinki na zo! Zugar da kike yi wa Sajida ta yi aiki. Amma ki sani wallahi muddin kika ga ba a yi auren nan ba; to sai idan ba na numfashi a cikin duniya. Amma wajibi ne sai Sajida ta auri Aminu ko kina so ko ba kya so."
"Wane Aminun!!?"
Zancen Maman TaufiÆ™ kenan cikin muryar tashin hankali, a lokacin da take shigowa gidan idonta a kan Yaya Maimuna.
"Aminu na ji kina faÉ—a!"
"Ko ma dai wane ne ba ku isa ku hana abin da Allah ya ƙaddara ba"
Tambaya Maman TaufiÆ™ kenan da amsar Yaya Maimuna a lokaci É—aya. Jikina yana rawa na ja Maman TaufiÆ™ muka shige ciki ina faÉ—in,
"Ba da ke suke ba ni aka zo yi wa takakkiya. Ni kuma a yanzu daidai nake da kowa tun da abin nasu babu mutunci balle kawaici."
"Wai har na ji sanyi wallahi. Ba ki ji yadda ƙirjina ya buga ba a lokacin da na ji ta kira sunan Amini.."
Zama muka yi a kan kujera tana faÉ—in, "Ita Sajida aure za ta yi ne?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.