Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 86

Tun da safe na miƙe na taimaka wa Ummu Salma suka shirya cikin kayansu na makaranta, sannan suka karya agurguje suka nufi ɗakin shi ya ba su kuɗin tara da na abin hawa.
Daga nan inda nake ina jiyo sautin shi yana yi musu faɗa. "Ni fa wallahi ban da kuɗin da zan ba ku yau. Don ko wurin aiki ba zan je balle na ba ku kuɗin tara, karɓi ɗari ku yi maneji da ita idan za a kai ku hakan.."
Suka fito fuskokinsu a haɗe suka yi mini tsaye, cikin ƙunar rai na miƙe na ɗauko musu kuɗin tara sannan na ƙara musu kuɗin da zai kai su ya dawo da su. Don daman can kuɗin zuwa kawai yake ba su idan an tashi su dawo ƙasa. Sannan na ja kunnuwansu sosai a kan kada su je ko'ina idan sun dawo ba ba nan, matuƙar ba lokacin islamiya ya yi ba su tafi. Saboda asibitin da zan je ganin likita, kuma ban san lokacin da zan dawo ba.
Na raka su har ƙofar gida suka tafi suna ɗaga mini hannu sannan na dawo na nufi ɗakina rai a ɓace. Saboda matuƙar haushin da na shiga dangane da riƙon sakainar kashin da yake yi muna ni da yarana. Wanda hakan ya ƙara saka mini haƙuri da juriya a kan zaman da Umma take so na yi ko don yarana. Domin Mukhtar ko dabba aka bar masa tsaro sai ta mutu bai san ta mutu ba, saboda rashin kula da ko-in-kula irin na shi ta kowane ɓangare. Haƙƙin kan shi ma bai sauke ba balle haƙƙin waɗanda ke tare da shi.

A gurguje na shirya ba tare da na sake bi ta kan shi ba na fice abina. Kai-tsaye gidan Firdausi na nufa, domin ta raka ni asibitin saboda babu waya a hannuna balle na kira ta.
Da murna ta tarye ni muka yi ɗakinta cike da jin daɗin ganin juna, zama na yi a kan gadonta ina faɗin "Wash!" Saboda tafiyar da na yi gabaɗaya jikina ciwo yake yi, domin har lokacin ba na jin ƙarfin jikina.
Bayan mun gaisa na sanar da ita abin da ya kawo ni wurinta, shiru ta yi na É—an lokaci sannan ta ce "Bari na faÉ—a wa Baban su Mujahida tun kafin ya fita".
Da sauri ta fice na bi bayanta da kallo cike da burgewa, saboda suna zaman lafiya sosai ita da maigidanta da yaransu cikin farinciki. Tagumi na yi ina zancen zuci,
'Ke kam kin yi sa'ar aure, ba irina ba da na rako matan auren duniya'.
Har raina idan na ga mace da mijinta suna ƙaunar junansu, burge ni suke yi matuƙa gaya. Saboda ni ban ƙaradda komai a cikin aure ba face wahala da tsunduma kai a cikin masifa. Bayan zubewar ƙimar da mijin ya yi mini a idon mutane, tare da janyo mini zagin da ban ji ban gani ba...

"Yawwa! Ya ce mu je amma fa wallahi ya yi faÉ—a..."
"FaÉ—an me?" Ita ce tambayar da na jefo mata saboda faÉ—uwar da gabana ya yi babu shiri.
"Ya ce ina mijinki da ba zai kai ki asibitin ba sai ni zan kai ki?"
Ajiyar zuciya na sauke tare da yin tagumi nan take na ji wani ɗaci ya ziyarci maƙoshina. Cikin sanyin muryar da ke gaf da kuka na ce "Idan kin ga zan takura kawai na tafi ni kaɗai..."
"Ba fa hana ni ya yi ba, kawai dai haushi abin ya ba shi a ce ni zan raka ki asibiti bayan mijinki ne ya dace ya É—auki alhakin hakan. Bari na shirya mu je kada mu yi latti da yawa mu tarad da jira"

Bayan ta shirya muka fito gidan, abin hawa muka samu muka hau. Muna tafe ina yi mata bitar yadda muka yi da shi a kan zuwa Asibitin. Girgiza kai kawai ta yi cike da takaici ta ce "Ni na rasa wane irin mutum ne Mukhtar! Shi kullum idan bai janyo abin magana ba ba ya jin daɗi. Tsakani da Allah kwata-kwata ba ya kyautawa, domin ita lafiya gaba take da komai". Shiru kawai na yi ban ce komai ba, saboda tsabar ɓacin ran da na shiga.

Ko da muka je Asibitin mun taradda jira muka bi sahun masu bin layi. Muna ta hirar matsalolin ma'aurata ni da Firdausi har layin ya kawo kaina, na shiga ofishin likitan cikin sanyin jiki na zauna kujerar da ke gaban shi. Bayani na fara yi masa bayanin abin da nake ji, shiru ya yi mini na ɗan lokaci yana rubuce-rubuce sannan ya ɗago kai yana ƙare mini kallo ya ce
"Kina da aure?"
Na ce masa "I"
Ya sake yin rubutu jikin wata takarda sannan ya miƙo mini ya ce
"Je ki a yi miki awon, idan aka gama ki kawo mini result".
Na miƙe cikin hanzari na fice, wanda nake ji a jikina kallona yake yi ta bayana. Takardar na miƙa wa Firdausi muka nufi ɓangaren da za a yi mini awon. A nan ma jira muka yi har layi ya kawo kanmu, tare da ita muka shiga. Aka ɗibi jinina da fitsari sannan muka dawo muna jiran sakamako. Mintuna a tsakani aka kira ni na karɓi takardar gwajin muka koma wurin Likitan. Na miƙa masa takardar ya duba tsawon minti biyu sannan ya kalle ni ya ce,
"Kina da ulcer, kuma sannan kina fama da matsananciyar sha'awa a jikinki. Ki yi ƙoƙarin shawo kan matsalar tun kafin ta yi ƙarfi".
Kunya ta rufe ni na haɗe fuska ban ce komai ba. Takardar ya miƙo mini ta magungunan da zan saya sannan ya raka ni da addu'ar samun lafiya, na fito offishin cikin sauri saboda kunyar da ta yi mini lulluɓi.

Ban sanar da Firdausi zancen ba, amma na yi mata bayanin ulcer da aka ce ina ɗauke da ita. Chemist ɗin da ke bakin Asibitin Firdausi ta sa muka je, magungunan aka duba mana sannan aka saka leda bayan an yi total. Kuɗin da ke hannuna ba su isa ba sai da ta cika mini, sannan na karɓi maganin muka tafi.

Abin hawa muka fara nema a bakin titi, kamar an ce na kalli gefena. Sai ga MD da gudu zai wuce ta gabanmu karaf idanuwana suka sauka cikin na shi. Gabana ya ƙire ya faɗi saboda tozalin da na yi da shi ya tuna mini ɓarnar da Mukhtar ya yi masa. Nan take na shiga sunkuyar da kai har ya dawo ya tsaya gabanmu, cikin fara'a yake tambayar inda za mu je. Firdausi ce kawai ta amsa masa da cewa, "Gida za mu je..?"
Gaishe shi na shiga yi cike da jin nauyin shi a idona, buÉ—e motar ya yi ya fito idanuwan shi a kaina yana faÉ—in
"Ya jikin naki?"
Kaina a duƙe na ce "Da sauƙi".
"Allah ya ƙara lafiya"
"Amin" Firdausi ta amsa, ni dai kaina a duƙe zuciyata cike da son ba shi haƙuri dangane da abin da ya faru. Motar shi ya koma ya fito da wata leda a hannun shi ya miƙo mini yana faɗin
"Ga wayarki nan da na manta ban ba ki ba ranar. Tsoron wata rigimar ya hana na bai wa kowa ya kai miki gida. Sannan ki yi haƙuri dangane da abin da na janyo miki ranar, ban san hakan zai faru ba da ban je ba..."
"Babu komai ni ce ya dace na ba ka haƙuri..." Maganar da na yi kenan cikin sanyin jiki, kafin ya katse ni da faɗin,
"No! Kada ki damu. Allah ya ƙara lafiya".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.